BABI NA GOMA SHA DAYA

81 3 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

11
Ba k'aramin tashi hankalin momy ya yi ba jin yadda Nuwaila ta yi sanyi, kuma wai har ta raba d'aki tsakaninta da y'ar uwarta Azzah.

"Ki taimaka ki tambaye ta halin da take ciki, ina jin tsoro, hankalina ba zai kwanta ba".

Momy ke fad'awa mama Dije haka saboda ta kasa tsayar da zuciyarta akan azalzalarta da take yi.

"Na lek'a ma d'azu na same ta tana magana a waya shiyasa ban tambaye ta ba, na yi mamaki tsawon lokaci haka ban lura da basa d'aki d'aya ba, sai yanzu hankalina yake bani, Nuwaila yanzu ita take fito da kayan wankinta kuma koda Ila zai kawo sai dai naga na Azzah kawai".

"Abba komai na gama shiryawa, na shiga na gansu, idan lokaci ya yi kawai zamu kwashe su ne daga nan a kai su Sokoto".

"Idan hakan ya yi babu matsala sai ku shirya ranar da za a yi tafiyar, sai dai ga shawara".

Shiru Hisham ya yi yana sauraren Abba sai da ya gama magana tukunna ya ce, "to shikenan Abba, Allah ya sa mana hannu".

Amin ya amsa sannan suka tashi daga palon.

Shiri yake da sauri-sauri saboda ganin lokaci ya tafi sosai zai iya rasa jirgin ma.
Momy na kwance kamar yadda ta saba idan yana nan tana binsa da kallo.

Rama ta hango ajikinsa duk da dama ba mai k'iba bane shi sosai, amma kuma ba ramamme bane, rufe idonta ta yi tana tunanin matsalolin dake tunkaro su a yanzu, babu mamaki ramar da ya yi tana da nasaba da manyan asarorin da yake tafkawa acikin sati shidan da ya yi a k'asar nan ga shi har zai kuma tafiya ba'a gano daga ina matsalar take ba.

Shafa fuskarta da ya yi ne yasa ta bud'e idonta ta sauke su ras acikin nasa, blowing kisses ya mata a fuska ta kawar da kai daga kallonsa.

Tana mamakin irin wannan soyayya, tana so ta yadda amma kokonta ya shiga zuciyarta.

"Kiyi min addu'a Zainab zan tafi, insha Allah wannan karon sati d'aya zanyi, na daina zuwa ina barinki da kewata".

Da ido ta bashi amsa kamar yadda ta saba, zaunar da ita ya yi kan wheelchair d'inta suka zo palo Azzah ta fito daga d'akinta da sauri tana kallonsu.

"Azzah je ki kira min Nuwaila da Gaddafi kuma ki yi sauri", Dady ya ce.

Dak'yar take tafiya a cikin skirt d'in da ke jikinta saboda ya kama jikinta sosai.

A tare suka dawo, kud'i Dady ya bawa Gaddafi, "ka sa mai a motarka, ka siya abinda kake buk'ata kafin na dawo".

Gaddafi ya kalle shi yana murmushi.

"A'a Dady ka ji da k'annena kawai ni babu abinda nake buk'ata".

Murmushi shima Dady ya yi sannan ya k'aro kud'i akan wanda ya bawa Gaddafi sannan raba kud'in biyu ya bawa Nuwaila rabi ya bawa Azzah rabi.

"Kuyi abinda ya dace, karb'i Nuwaila ki ba mamanku Hadiza ta siya abinda take so zata iya aikin Sama'ila ko Gaddafi idan yana da lokaci".

Mama Dije da fitowar ta kenan daga kitchen ta ji abinda yake fad'a ta koma kitchen da sauri saboda kukan daya zo mata ba zata iya rik'ewa ba, daga baya baya na rayuwar nan bata tab'a yin farin-ciki irin wannan ba.

Dady bai fita ba saida ya jaddadawa Azzah ta cire kayan nan, ko takai a bud'a ko kuma ta yi sadaka da su.

Shirin zuwa kasuwa Azzah ta yi Zarina ce zata raka ta ita ma dai da abinda zata siya.

Tun azahar ta fita har bayan isha'i bata dawo ba, hankalin Mama Dije yai mugun tashi, duk rawar kai irin na Azzah ko magrib bata tab'a kaiwa a waje ba, ta kasa fad'awa momy sai kawai ta fito k'ofar gida ta tsaya.

Bayan kamar mintuna goma ta ga Sama'ila ya bud'e gate ta ja dogon numfashi amma ta kasa sauke shi yadda ta yi niyya ganin motar Gaddafi ce ba Azzah ba.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un

Ta fad'a a fili.

Gaddafi ne ya k'arasa kusa da ita yana tambayar ta lafiya.

"Gaddafi tun azahar Azzah ta fita har yanzu bata dawo ba".

Wayarsa ya zaro daga aljihu ya nemo layinta ya shiga kira, ta yi ringing har ta yanke ba'a d'aga ba, sai da ya mata miss call yafi shida amma ba'a d'aga ba.

"Mama ina tace muku zata je?"
"Kasuwa wai ita da Zarina, to ganin har k'arfe shida da rabi bata dawo ba ya sa na yi tunanin ko ta tsaya a gidansu Zarina d'in ne".

"Ok shikenan ki koma cikin gida yanzu kar ki fad'awa kowa kuma ki kwantar da hankalinki, yanzu zanje gidansu Zarina d'in ingani".

Bai saurari tambayar da take masa ba wai ko yasan gidansu Zarina d'in ya tafi.

"Wallahi yaya Gaddafi bata zo ba, na dai ga miss call d'inta bayan awa d'aya dan lokacin ina bacci ta kira bayan na tashi na kira ta  amma bata d'aga ba shikenan ban kuma kira ba ita ma bata kira ba".

Zufa yake ta ko ina dan yasan ba yawo suke ba in ba yanzu da suke zuwa makaranta ba.

"Cewa ta yi zata zo ki raka ta kasuwa lokacin data kira ki a lokacin ne ta bar gida, amma shikenan bari in koma gida in gani kota dawo".

Sallama ta yi masa da addu'ar Allah yasa lafiya.

Y'an gidansu ma hankalinsu ya tashi sosai.

Kasa hak'uri Gaddafi ya yi har ya isa gida, kiran Nuwaila ya yi ya tambayeta ko Azzah ta dawo tace ita dai tun d'azu tana palo kallo take yi bata ga shigowar Azzah ba.

Rashin sanin meya kamata ya yi gaba yasa shi dawowa gida.

A palo ya samu mama Dije da Nuwaila, mama Dije sai kuka take dan yanzu har tara ta gota amma babu wani labari sai ma ji ta yi daga bakin Nuwaila Gaddafi yace bata gidansu Zarina.

Zama ya yi kusa da Nuwaila yana kallon agogon dake manne jikin bango.

"Gaddafi me zamu yi yanzu? Ba fa zama zamu yi muna tunani ba".

"Na rasa ma wane kalar tunani zan yi, inaga kawai mu fad'awa momy".

Tashi suka yi suka shiga d'akin har mama dije.

Shiru momy ta yi tana sauraren bayanin Gaddafi, ba tada sauran nutsuwa amma ta kasa magana saboda Nuwaila na wurin.

"Momy ki yi magana na san komai ki bamu mafita bamu san halin da take ciki ba dan Allah". Ta kai karshen zancen tana kuka sosai.

Zaro ido momy ta yi tana kallon ta.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now