BABI NA BAKWAI

74 1 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

7

Ya jima a wurin yana tunanin mai ya ke damun ta amma tunani ba shine mafita ba zuwa wani lokaci zai tambaye ta matsalar ya ji ko da taimakon da zai iya bata.

A meeting d'in gaggawa da Dady ya had'a kamfaninsu babu wani abu da su ka gano, sai dai sun yi tunanin ko wani kamfani aka samu da ya fi nasu ko kuma yake musu shigo-shigo ba zurfi.

Ba k'aramin tashi hankalinsu ya yi ba, saboda wannan aikin da shi ne su ka fi maida hankali da kuma rayuwarsu, idan ya samu matsala to tabbas su ma su na cikin mawuyacin hali.

"Mama Dije wai waye yake miki kitso".

"Ni nake yi wa kai na mana tunda ba fita nake ba".

Shiru Azzah ta yi tana tunani ya mutum zai yi wa kansa kitso amma dai bata kuma magana ba.

Tun daga lokacin Hisham ya ware ranakun da yake zuwa duba Azzah, amma ya bata lokaci har sai da ta kammala exam d'in ta.

Mama Dije da momy zaune a d'aki, momy ta kalli Dije da kyau idonta sun cika da hawaye.

"Hadiza na gaji da kwanciya na gaji da rufa asiri, yaran nan k'arfinsu ya kawo ya kamata su san halin da ake ciki".

"A a Zainab na sha fad'a miki lokaci bai yi ba, wata gagarumar matsala ce za ki tono duk lokacin da kika nuna lafiyarki k'alau, Gaddafi ne ya kama aiki shi kad'ai ga Azzah ta zaburo da maganar aure saurayin ya nace mata, ina lura da ita kullum suna mak'ale da waya abinda yake k'ara d'aga min hankali bai fi irin rashin jituwa tsakaninta da Nuwaila ba".

Ta gama maganar tana dafe goshinta alamar matsalolin suna so suyi yawa.

"Meye amfanin Gaddafi shi ba zai iya had'a su ya jaddada musu duk ranar da suka k'ara yin dambe zai dauki mummunan mataki akan su ba".

Murmushi mama Dije ta yi har ta bud'e bakinta za ta yi magana aka k'wank'wasa k'ofar d'akin tashi tayi ta bud'e sannan ta dawo ta zauna.

Gaddafi ne ya shigo had'i da kuma rufe k'ofar. duk zancen da suka yi yaji yana kuma neman a k'ara fito dashi haske, kallon momy ya ke idonsa har sunyi ja sosai tana ganin haka ta gane ya ji, juyar da kanta ta yi gefe tana murmushi a zuciyarta ta ce, " dama k'arya tana k'arewa lokacin wannan k'aryar ya K'are".

Hannunta taji Gaddafi ya rik'o ya mik'ar da ita zaune.

"Momy me yasa zaki mana haka muna so muji muryarki, muna so muga kina tafiya kamar kowa da k'afafuwanki momy, me yasa ki ka zab'i wannan rayuwar?".

Murmushi ta yi tana shafa kansa ta ce, "a cikin Ku na san kaine mafi nutsuwa sannan Nuwaila ce ta ke bin bayanka amma k'anwarku Azzah a firgice take, ka saurareni da kyau Gaddafi kar ka yadda Nuwaila ko Azzah su ji wannan maganar kaima kasan dalili saboda su mata ne".

Gyad'a mata kai yayi alamar ya fahimta hawaye na zuba daga idonsa,"idan na ce kada su Nuwaila su san wannan zancen ba wai ina nufin kada ka kirasu ka fad'a musu kawai ba yana nufin kada ka sake ka fad'awa wani".

"Kalli mama Dije duba mai tsafta Gaddafi".

Kallon mama Dije ya ke yana sauraren sirrin da su ka jima suna b'oyewa, ya kuma girmama k'aunar uwa awurin d'anta har sai da momy ta tsaya da magana sannan ya d'auke ido daga kanta yana kuka har da sheshsheka.

"A tak'aice na baka labari Gaddafi saboda bamu da lokaci ka rik'e sirri sannan ka tabbatarwa kanka cewa kai d'in namiji ne, akwai ranar da mu ke jira, ka kuma goge hawayenka duk wanda ya gani zai nemi sanin dalili, tashi ka tafi kasan dadynku na nan".

Duk lokacin da Hisham ya kira Azzah a waya koda Nuwaila ba ta so to lallai ne sai ta karb'i wayar sun gaisa da shi.

Gaddafi zaune a dinning room yana cin abinci yana danna wayarsa ya jiyo hayaniya a palo sai ya saurara sosai, Azzah ce ta samu damar yiwa Nuwaila yadda ta ga dama.

"Kiyi ta yiwa samarin wulak'anci lokacinki idan suka d'auke k'afa samarin sai a barki a gida ke kad'ai ki ci tsufanki a gida, zuwa lokacin babu mai sonki daga nan idan kin kasa auruwa sai ashiga yawon..."

Kyakkyawan mari Gaddafi ya sauke mata daya gigita tunaninta.

"Saboda kinga ana k'yale ki ko Azzah, Nuwaila sa'ar ki ce?, To bari kiji daga yau idan na k'ara gani ko kuma na samu labari kin yiwa Nuwaila mugun kallo ma kiga mai zan miki".

Ya wuce yana mitar, "baku bar mutum da abin da ya dameshi ba kuyi ta sa shi hayaniya".

Nuwaila kuwa ba k'aramin sosa mata zuciya maganganun Azzah suka yi ba mik'ewa tayi kawai ta shiga d'akinsu tana kuka.

"Wallahi sai Allah ya saka min mugu azzalumi kawai" Azzah ta fad'a tana kuka iya k'arfinta.

"Ya zama dole na koyawa Azzah girmama ni, ta soma wuce gona da iri idan ba haka ba wata rana zan illatata ko kuma na yi mata tsana irin wacce ba'a zato ba kuma zan tab'a son haka ba" Nuwaila ta fad'a a zuciyarta lokacin da take kwance tana share hawayenta.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now