BABI NA GOMA SHA TAKWAS

89 10 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

18

A tsakar gida suka tarar da Mama Dije Mommy ta zauna kusa da ita nuwaila ta gaisheta,dak'yar Azzah tafi k'arfin zuciyarta  sannan ta gaisheta fuskarta babu fara'a ko kad'an.

Jikin Mama Dije yayi sanyi sosai ta bi Azzah da kallonta, palon Azzah ta shiga ta kwanta kan kujera ba tare da ta nemi Hajiya ba.

Abinci aka kawo musu palon suka zauna suna ci banda Azzah saida Hajiya ta kalleta tace, "Azzah sauko ga abincin mana".

"su ci kawai Hajiya bana jin yunwa".

Shiru suka yi suna kallonta bata juyo ba har suka tsakuri abincin suka Tashi duk da uwar yunwar da suke ji.

Fita Azzah ta yi daga gidan ta koma can waje ta zauna tana ganin jiri saboda yunwa, Hisham ya biyo bayanta dan yaga lokacin da ta fito daga gidan suna zaune palon tsoho.

"haka za kiyi min Azzah?, kinsan yadda nake ji azuciyata?, har ciwo nayi akanki dan Allah ki tausaya min"

Kamar jira take sai ta fashe da kuka, yayi shiru yana kallonta saida ya barta tayi kukan sannan ya zauna kusa da ita, cikin kukan ta fara masa manana.

"ciwon da kayi badan ana nema a rabamu bane na cire rai akanka nakuma tabbata kaida mahaifiyarka bakwa k'aunata, saida  ta bari sonka yamin kamun da bazan iya jure rashinka ba sannan zata k'i amincewa da aurenmu kaima Ka k'ara bada gudunmawa wajen nesanta kanka Dani, Ka kuwa san irin halin da hakan ya jefani?"

"hakanne kad'ai zanyi na iya shawo kanta Azzah, karki manta an mata laifi dole ne zata nuna fushinta ki yi mata uzuri, Wallahi ni shaida ne itama tana son aurenmu".

"tayi fushinta iya tsakaninta da Daddy mana" ta fad'a tana turo baki.

Murmushi kawai yayi yace kafin yayi magana sai ga Nuwaila ta fito Jamil kuma ya shigo yana sauri, A tare suka mik'e suka nufi wurin su Jamil d'in.

"kawo jakar na rik'e miki gimbiya muna sauri karmuyi letti".

"zamu je rakiya" inji Hisham.

Bai kalle su ba suka fita shida Nuwaila, su kuma suka bi bayan su, gaban motar Jamil ya bud'ewa Nuwaila ta shiga Azzah da Hisham suka shiga baya, saida suka fara tafiya  sannan Jamil yayi magana.

"wai ku ba an rabaku ba? Shegen naci waya ce ma ku biyo masoya?".

"muma masoya ne shiyasa muka fito saboda tafiyar ta masoya ce, kuma mu ai mai rabamu sai Allah daya had'amu ".

Shiru Jamil yayi lokacin suka iso wani babban shago da ake siyar da k'ananan kaya da atamfofi da leshi.

Azzah ta staya daga gefe tana kallon kayan da Nuwaila dake ta zab'o kaya ita da Jamil, basai Sun fad'a ba ta gano lefe suke had'awa kallon kayan taci gaba da yi.

Hisham yaji tausayinta dan haka ya janyo mayafinta yana cewa.
"kema zo muje ki zab'o naki kinga ma sai mu rage aiki".

Dad'i ya kamata dan haka ta shiga d'ebo kaya yana kallonta shima yana zab'o wanda suka burgeshi, har suka zo sashen inner wears, ya D'an saci kallonta yaga ta shiga d'aukar abinta bata damu dashi ba, sizes d'inda take d'auka ya bashi dariya amma ya danne.

Kusan siyayyar da tayi motar ma zata d'auka ba, Jamil da Nuwaila sakin baki sukayi suna kallon kayan.

"ka nemi motar da zata d'auke ku da wannan kayan malam".

"karku damu yanxu na kira wani abokina zai zo ya dauke mu da kayan".

Kallo ya dawo kansu lokacin da suke shigo da kayan palon tsoho, zama kusa da kayan sukayi suna hutawa, dama ita Nuwaila Mommy tasan zasu tafi kuma shi Jamal zai tafi da kayan gidansu ne akawo lefen wani sati dan asaka ranar aurensu.

Azzah bakinta kamar zai yage dan murna, Mama Dije mamaki ya cikata tana kallon yadda yara zasu fi k'arfinta, kallon Mommy tayi race, "zainabu d'an zo muyi magana".

Fita daga palon sukayi suka shiga d'akin Hajiya.
Mama Dije ta kalli Mommy tace,"Zainabu kina kallo yara zasu kasheni da Raina? Kice Daddy ya kira baban kaduna in yaso sai a had'asu da Nuwaila inba haka ba yaran nan koda zamu duba har kayan d'aki Sun siya".

Hawayen farin ciki suka zubo idon Mommy suka rungume juna.

Koda sati ya zagayo anyi magana aka kawo lefen Azzah da Nuwaila abu kamar a mafarki. Gaddafi sai bayan sati d'aya sannan aka Gama had'a lefensa aka kai komai ya tafi yadda ake so.

Date kawai ake jira afara gudanar da biki, sunata shirye shirye, Hisham ya shigo Kano dan haka yana Gama aikin daya kawoshi ya tafi wurin Azzah makaranta.

Zareena an fara nauyi suna zaune ita da Azzah a motar Azzahn Hisham ya yi parking dai-dai su, komawa motarsa Azzah ta yi suna gaisawa wayarta ta yi ringing ta duba sai ta d'ago ta Kalli Hisham, shima kallonta yake.

"ki d'auka mana".
"bana daukar numbern da bansaniba" tabashi amsa.

Wannan Karon tana yin ringing ya rigata d'auka, wayar yasa a kunnensa, Saifullahi  ya yi K'asa da murya.

"Haba Azzah bai kamata kimin haka ba tun jiya nake kira kin k'i d'agawa".

Gabansa ne ya shiga fad'uwa bai ce mata komai ba yasa wayar aljihunsa sannan ya yi mata sallaama, jikinta yayi sanyi haka dai ta fita daga motar tana kallonsa har yabar department d'in.

Dama basuda lectures sai suka kama hanyar komawa gida, saida ta sauke Zareena sannan suka yi sallama ta wuce gida.
Gabanta ya fad'i ganin Hisham zaune a palon Dan sam bata lura da motarsa a waje ba.

Follow me on wattpad @Safiyyahgaladanchi16.

BAYA DA K'URAOnde histórias criam vida. Descubra agora