The Beginning and the End of Me

9.5K 371 36
                                    

*Happy New Year*
Allah yasa mun shiga a sa'a ameen

*💔 JIDDA 💔*

*By*

*Maman Maama*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu alaikum masoyana da masoyan littattafai na. Kamar yadda nayi alkawari tun kafin in fara *Tagwaye* cewa zanyi su su biyu da *Jidda* to alhamdulillah an kammala Tagwaye ga kuma Jidda nan yazo muku, ina kuma fatan zaku karbe shi kamar yadda kuka karbi Tagwaye koma fiye da haka.

Dan dai idan nace *Jidda* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *Jidda* ba zan iya cewa an barki a baya. It is going to be a hit, that I promise you.

Tafiyar *Jidda* da banbanci da sauran littattafai na, banbancin kuwa shine about 70% na labarin Jidda is based on true life events, musamman daga farkon sa zuwa tsakiyar sa, karshen sa ne kawai zai zama fiction yadda zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shine from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share hawaye, so get ready to do both.

Littafin Jidda na siyarwa ne kamar yadda na riga na fada tun kafin fara Tagwaye. Da farko nayi niyyar sai na gama gabaki daya zan fara posting, but I found out cewa ba zan iya ba, without your motivation I lost my courage, wannan ya tabbatar min idan babu readers babu *Maman Maama* dan haka zamu fara a haka.

Sai dai ba za'a ke samun posting kullum ba saboda alhamdulillah kullum responsibilities suna kara yi min yawa ne, I guess wannan shine girman ko? Lol. Za'a ke fashin kwana dai dai, misali in akayi Saturday ba za'a yi Sunday ba sai Monday. Yes, nasan wadansu ba zasu iya jira ba and I advise them to wait sai anyi nisa ko kuma ma su bari a gama sai su karbi document. Please in kinsan ba zaki iya jira ba kar ki biya, don't pay and be pressuring me please. Fashin kwana dai dai so that you will have well arranged and well edited episodes insha Allah. I assure you that ba zakuyi dana sanin siyan Jidda ba, it is going to be one of your best dan for me *Jidda* already ya kere wa saura a zuciya ta.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only

Again dai ina tunawa nasu siyan online novels cewa copyright (hakkin mallaka) na marubuciya ce, ita kadai take da right din copying da kuma sharing littafin ta, duk wanda yayi hakan bayan ita to ya shiga hakkin ta kuma duk munsan cewa Allah baya yafe hakkin wani har sai shi ya yafe da kansa.

Allah yasa mu gane ameen.

Akwai 15 free pages insha Allah

Asha karatu lfy

*Episode One........The Beginning and the End of Me*

Free page

A duk lokacin dana duba rayuwata, kamar in inaso in bada labarina, na rasa dalilin da yasa bana iya farawa ta farko na, bana iya farawa ta lokacin da aka haife ni ko kuma ince lokacin da na bude idona na ganni a duniya. A kowanne lokaci in na duba bayana ina farawa ne da ranar dana fara ganinsa, a gurina wannan ranar, wannan hour din, wannan minute din da kuma wannan second din da idanuwan sa suka shiga cikin nawa a lokacin ne rayuwata ta fara. A lokacin ne kuma rayuwata ta kare.

Ranar visiting day ce a makarantar yammata ta garin Taura dake jahar Jigawa. Kasancewar yan ss3 ne kadai a makarantar suna zaman extension wanda ake yi lokacin zana jarabawar karshe ta secondary ya saka makarantar take shiru ba kamar sauran ranakun visiting ba.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now