Pilot

2.8K 154 6
                                    

Tun da muka fito daga makarantar, na juya ina kallon gate din amma sai naji bana jin wani excitement kamar yadda nayi tunanin zan ji. Na yi ajjiyar zuciya tare da mayar da kaina na kwantar a jikin tagar mota tare da lumshe idona.

"Bana son in rasa ki a matsayin kawa"
"He has left a trail of broken hearts"
"You will do what is right"

Wadannan maganganun su suke ta yi min yawo a kaina. Muryar yaya Tahir naji "ban taba ganin wadda bata murna da zuwa gidan su ranar candy ba sai ke. Unbelievable. Wai kuka kike yi?"

Na dago kai ina kallon sa, sannan na kalli yaya Muslim da yake driving, na dan goge idona ina kallon hawayen da ban ma san sanda suka fito ba nace "ina murna mana yayana, ina murna sosai da sosai, kawai dai ina jin babu dadi ne zan rabu da kawaye na dana saba dasu shekara da shekaru, wadansu fa shekarar mu shida tare kaga kuwa ai sabon mai yawa ne"

Yaya Muslim yace "to ba kina da numbers din su ba? Ai zaku ke waya ko? Kuma kina zaki sake wasu kawayen da har zasu mantar dake wadannan. Ni yanzu few abokai na na secondary school ne yake da contact dasu, duk kowa ya kama gabansa" sai suka cigaba da hirar abokai a tsakanin su, tunda kusan duk abokan su daya, ni kuma na koma na kwanta na rufe ido na ina ganin fuskarsa "smile please" na danyi murmushi sai kuma na bata rai, shin da gaske abinda Mufida ta fada min akan yayanta haka ne ko sharri take yi masa? Amma kuma akan wanne dalili zata yi masa sharri? In kuma gaskiya ne mai yasa ta gaya min? Kamata yayi ace ai ta kare image dinsa a matsayin sa na yayanta dan na tabbatar cewa tafi sonsa a kaina.

Amma dai whatever the case warning ne tayi min, ya kamata kuma inyi wani abu a kai, Amma me zanyi? Tace ba ta so yayi breaking heart dina, abinda ya kamata nayi shine in nisanta kaina dashi dan kar in fada cikin soyayyar sa but Oops! am already in. Sai dai zan iya fita tun kafin in nutse har kai, tun kafin inyi drowning. Menene abinyi?

Zan bawa Farhan labarin sa, nasan kuma in muka hada kai ni da ita zamu samu mafita..........amma me yasa in na hango rabuwa dashi a matsayin mafita sai inji zuciyata tana min zafi? In kuma na hango cigaba da alaka dashi a matsayin mafita sai inji murmushi yazo kan fuskata?

******************************************

Sunana Jidda. Sunan Mahaifina Alhaji Habib Mahmud wanda yake haifaffen cikin garin kano ta bangaren uwa da uba gabaki daya, malamin makaranta ne wanda a halin yanzu yake da matsayin principal a daya daga cikin manyan makarantun secondary school na jeka ka dawo na maza dake garin kano. Alhaji Habib yana da rufin asirinsa dai dai gwargwado dan gidan mu bamu taba rasa ci ko sha ko kuma wasu basic needs na rayuwar duniya ba, duk wadansu bukatun mu Abban mu ya dauke mana su dai dai gwargwado.

Ba zamu kira kanmu direct da masu kudi ba, kamar yadda ba zamu amsa sunan talakawa ba. Mata biyu Alhaji Habib yake dasu, Hajiya Maryam ita ce uwargidan sa wadda muke kira da Hajiya, sai kuma Hajiya Ayesha wadda muke kira da Umma, ita ce kuma mahaifiya ta. Mu goma sha biyu Abba ya haifa, takwas daga ciki yayan Hajiya ne wadanda suka hada da Sa'adatu (Mama Sa'a), Hadiza (Mama Hadiza), Yaya Shamsu, Yaya Aminu,  Yaya Hudallah, Yaya Mukhtar, Yaya Muslim da kuma Aysha (Farhan) wadda take takwarar Umma kuma autar Hajiya.

A dakin Umma kuma mu huɗu ne, Yaya Tahir ne babba, sai Mahmud (Abbah) sannan ni Hauwa'u (Jidda) sannan autar mu Maya (Amira) wadda take autar gidan gabaki daya.

Mahaifiya ta Ayesha, yar asalin kasar Ethiopia ce, duk da cewa bata taba taka kafarta zuwa kasar ba har yanzu. Mahaifinta, Amadi, ya baro kasar su ne ya taho neman kudi har ya sauka a Nigeria kuma ya kafa kasuwancin sa anan Kano, Allah yayi anan abincinsa yake, saboda son ya koma gida ya saka iyayensa a lokacin suka nema masa auren kakata Maya, takwarar Amira, dan suna tunanin idan suka yi masa aure zai koma gida, sai dai ya koma din amma ana daura masa auren sai ya dauko matar tasa ya taho da ita Nigeria itama, suka ci gaba da zamansu anan a dole yan uwa suka hakura ya zamanto tsakanin su da juna sai dai ziyara da kuma ta hanyar waya.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now