Bashir

2K 160 7
                                    

Bai dawo ba har bayan sati daya, shima kuma Musa bai dawo ba. A cikin satin nan gabakidaya hankali na a tashe yake kusan kullum sai nayi wa Farhan mita a daki "yayi fushi dani Farhan. Watakila ma ya dauka yaudarar sa nake yi Musa nake so, bai san a lokacin da ya gan mu da musan ma ina gaya masa bana son shi ba ne ba"

Ita kuma sai tayi dariya, ita abin wai dariya yake bata "lallai Jidda kinyi zurfi da yawa, wai ke din ce kike tada hankali akan namiji? Jiddan dana sani ce kuwa? Ni ina ganin wannan dama ce a gare mu da zamu gane in da da gaske yake son ki, dan ni a ganina dan wannan abin bai isa ace ya barki ba, sai dai in dama ba da gaske yake ba" tabbas gaskiya ta fada, sai dai in dama ba da gaske yake ba, amma anya kuwa? Rashin sa yana nufin rashin chance dina na karatu.

Kusan kullum sai na kira Mufida munyi ta hira duk da nasan basa tare amma na fahimci hakan yana kwantar min da hankali dan nasan lafiyar sa kalau, ko dai ya fasa ne ko kuma yayi fushi sosai.

Kullum kuma ina saka ran inji ko Mufida zata yi min maganar sa amma shiru. Ina ta tunanin ko ni inyi mata in gaya mata yazo kuma ga yadda muka yi dashi ko da kuwa ban nemi shi ta bangaren ta ba at least ban rufe ta da komai ba, kar daga baya taga kamar na munafunceta. Amma still na kasa yi mata maganar. Ranar nan kuma sai gata tayi min da kanta "yanzu mutumin ki ya kira ni wai dan Allah in tura masa hoton ki, nace nima bani da shi" ta karasa maganar tana dariya. Naji wani sanyin dadi a raina amma sai nace "wanne mutumin nawa kenan?"

Tace "kya ji da shi ma can, na sani ai kuna tare da yaya Doctor amma kina ta wanibasarwa ko?" Na dan yi murmushi "to kinga laifi nadan na basar da shi? Ji nake kanwarsace ta bani shawarar in rabu da shi" sai ta danyi shiru, na dauka zata chanja topic amma sai naji tace "Yaya Doctor ne yana da wuyar sha'ani Jidda, ke kuma ba experience kuke da shi akan samari ba shi yasa na baki shawarar rabuwa da shi dan banyi tunanin da gaske yake ba" nace "amma me yasa kika yi wancan tunanin? Mai yasa kike tunanin yaudara ta zaiyi?" Tace "shi yana daukan irin wannan relationships na yammata da samari ne kamar wasa, in yayi budurwa sai kun gama sakin jikin ku da ita sai ya tubure yace shi fa ba da gaske yake ba kawai friendship ne. Ni wannan abin na gudar miki."

"A yanzu haka Mama babu abinda take so irin taga yayi aure, ita da kanta take samo masa yammatan da take ganin maybe zai so amma sai yace shi basu yi masa ba. Kinga kafin ya tafi India akwai wata second cousin din mu da Mama ta hada su sukayi dating sosai har mun fitar da anko fa, kawai bawan Allahn nan sai yaje ya samu Baba wai Mama zata yi masa auren dole"

Ta karasa maganar tana dariya nima sai naji maganar ta bani dariya "wallahi yarinyar baki ga yadda kowa ya ringa tausaya mata ba yadda kika san zata mutu akan sa amma yace shi wallahi baya son ta, haka ya hada kayansa yayi tafiyar sa India, haka Mama tayi ta bawa iyayen yarinyar hakuri. To irin haka nayi gudun kar ya faru dake shi yasa nayi warning din ki a kansa, saboda yana da saurin shiga rai musamman ke da babu kowa a zuciyarki, bana so kiyi ending up like cousin din can ta mu" na gyada kaina ina fahimtar ta kuma ina jin dadin abinda tayi min sannan na bata labarin so far abinda ya gudana tsakani na dashi, har form din da ya kawo min da zuwan da yayi gurin Abba na.

"Yanzu still kina tunanin ba da gaske yake ba?" Tace "I can't say gaskiya. Ina tsoron in bada shaida a kansa kuma yazo ya bani kunya" ta karasa tana dariya, sai kuma tace "amma dai abinda zan iya cewa shine ban taba ganin yayi going this far ba, ban taba ganin yayi getting involved with iyayen yarinya ba. I think ya kamata in bawa Mama wannan labarin...." Nayi saurin katse ta "na shiga uku rufa min asiri. Ki bar maganar a tsakanin mu please, in yana so Mama ta sani da kansa zai gaya mata" a haka muka kare maganar. Sai dai ni bata kare a zuciyata ba haka nayi ta bitar maganganun Mufida a raina. A karshe sai na yanke shawarar in Umar ya gama fushinsa ya dawo to zansan yadda nayi na tambayeshi game da relationships din da yayi a baya dan inji nasa side of the story din.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now