A Blessing or a Curse

1.8K 250 20
                                    


Rayuwa ta cigaba kamar ba ayi komai ba, Umma bata kuma ta yar min da maganar Jamila ba haka ma Farhan tunda ta ga bana so bata kuma yi min maganar ba, tsakani na da Umar ma ko sunanta bamu kuma ambata ba sai ma wani shafin na soyayya da mu ka sake budewa. Mutum daya da take maganar ita ce Hajiya. Ita kuma a nata bangaren tana kokarin tabbatar wa cewa duk wamda yake family din mu ya san maganar Umar da Jamila. Haka kawai in tayi niyya sai ta fito tsakar gida ta saka kujera ta zauna ta dauko wayarta tana ta kiran yayanta suna maganar suna dariya. Raina ya kan baci in tana yin haka amma ban taba tanka mata ba kamar yadda nake yi kullum ba dan halin ta ba ko dan tsakani na da Farhan.

Abu daya da ya chanja shine gwoggo Habibah da yayanta kaf sun janye jikinsu daga gidan mu, sun kuma janye daga duk shirye shiryen bikina bayan an saba duk bikin da za'a yi a gidan mu tare da su ake yin komai. Umma tayi kokari gurin rarrashin gwoggo akan tayi hakuri ta manta da maganar amma taki tace ita ba wai auren ne bata son ayi ba, taso ne dai Abba yayi wa Umar fada ya nuna masa bai kyauta ba kafin ya bashi ni din. Tunda akayi abin bamu hadu da yaya Jamila ba, amma naji ance wai duk ta chanja tayi wani iri har makaranta ta daina zuwa, duk da ban tabbatar hakan ko gaskiya bane ba ko kuma exaggeration ne irin na Hajiya.

Mu kam shirin bikin mu muke tayi, Mufida da Farhan ne suka fitarda anko na kawaye kuma sune suka gayyaci duk kawayen mu na school da na unguwa da kuma dangi. Umar ma kuma ya kammala duk shirye shiryen sa, ya gyara gidan sa dai dai da yadda yayi suiting taste din mu ni da shi. Sannan muka tsara duk yadda muke so bikin ya kasance. Umar ya saka a saka daurin aure ranar Friday "saboda albarkar ranar so nake ta bi auren mu ni da ke har abada".

Allah ya dora Umma akan Abba biki saura sati uku ya bar ni na tafi gidan Aunty Afia na zauna a can, ita kuma ta bude min sababbin lessons take dora min kullum akan aure da duk abinda ya kunsa.

"Shi aure da kike ganin sa Jidda hakuri ne yake rike shi. Duk matar da kika gani a gidan mijinta to zaman hakuri take yi da shi haka zalika shima mijin hakuri yake yi da ita. Shi kuma namiji da kika ganshi to tamkar sarki yake a gidan sa, babu abinda namiji yafi so fiye da komai a gurin matarsa irin ladabi da biyayya. Wannan girman da Allah ya dora musu to har a cikin halittar su haka suke, su dai suna son ayi musu ladabi kuma babu abinda suka tsana irin a raina su. Komai son da mijinki yake miki idan raini ya shiga tsakanin ku sai kin fita daga ransa. Duk abinda yace miki kar kiyi masa musu ki bishi a haka in yaso daga baya a hankali cikin dabara sai kiyi masa bayanin yadda kike so bawai ki nuna masa ke lallai ba zaki yi abinda yace ba ke abinda kike so zaki yi"

"Ki zamanto mai rike sirrin mijinki ba mai kwakwazo da yada duk abinda yafaru tsakanin ku a idon duniya ba, musamman a gurin kawaye ko yanuwansa ko naki. Kar kuma kike nuna kwadayin abin hannunsa, in ya baki ki karba ko mai kankantar sa kiyi masa godiya in kuma bai baki ba sai ki hakura, kar ki yarda kike rokonsa abun duniya sai lallai abinda yake hakkinki ne yayi maki kamar ci da shada sutura, suma kuma kinsan dai dai aljihunsa kar ki dira masa abinda yafi karfinsa. Ballantana ma ke tunda ya samo miki makaranta kuma muna saka ran zai barki kiyi aiki, sannan aikin health albashin su mai kyau ne dan haka zaki ke daukewa kanki wasu yan tsarabe tsaraben na mata ba sai ma ya sani ba"

"Kar kuma ki dora wa kanki mugun kishi akan mijinki ki ce ke lallai dake kadai zai zauna ba zai kara aure ba, in yanason karawa ki barshi ya kara din in dai har je ya sauke miki naki hakkin da yake kansa shikenan. Kema kuma sai kiyi kokarin ganin kin sauke nasa hakkin da yake kanki wajen kula da tsaftarsa data gidan sa, kula da abincinsa, kare mutuncin kia cikin gida a makaranta da kuma wajen aikin ki, sannan da tabbatar da kin biya masa bukatar sa a kan gado"

Na rufe fuska ina jin kunya sai tayi dariya "to au wannan shine yafi komai muhimmanci a aure, na saka shi a karshe ne saboda ina son inyi miki bayani sosai a kansa. Kinga mazan nan? To da yawa daga cikin su babu abinda suke girmama wa a cikin aure kamar wannan abin, duk da dai halitta halitta ce. Wani yana da bukata sosai wani saffa saffa wani kuma bai ma damu da abin ba, amma majority sun damu da abin. Kuma kinsan babban sirrin abin?"

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now