Matters of the Hearts

3.7K 168 10
                                    


Free Episode

Ita zuciya, annabi yace wata tsoka ce a jikin mutum wadda idan ta gyaru to dukkan sauran jiki ya gyaru idan kuma ta baci to dukkan sassan jiki ya baci kenan. Idan muka yi amfani da wannan maganar zamu iya nada zuciya a matsayin sarauniyar gabaki dayan jikin mutum, wadda kuma a lokuta da dama tana gudanar da mulkinta ne bisa son kai da son zuciya (lol) musamman in aka samu cewa shi mamallakin zuciyar baya iya juyata ya sakar mata ragama tana yin abinda ta ke so, to ina kuma ga ni? Ni da zuciyar tawa gabaki daya na riga na danka wa wanda bai ma nemi in bashi din ba, bai ma kuma san cewa na bashi din ba.

Tun ranar dana fara ganin sa, ranar visiting day, ban kuma jin cewa na dawo dai dai Jidda ta yadda nake kafin idanuna su shiga cikin nasa ba. Sau da yawa nakan samu kaina ido biyu bayan karfe biyun dare ta wuce, kuma ba wai akan sallaya ina sallah ba ba kuma wai da littafi a gaba na ina karatun jarabawar da aka kawo ni makaranta dan in karanta ba, a'a, na kan samu kaina ne a zaune akan gado na na jingina baya na da pillow staring into nothing and smiling.

In kuma nayi yaki da zuciyar tawa na samu na dauki littafi na kunna fitila da niyyar karatu to bayan wasu mintuna kadan zan iya samun kaina ina zana abinda zan iya tunawa na daga fuskarsa a bayan littafin da ya kamata ace karantawa nake yi. Idan kuwa class muka tafi da niyyar sauraron extra lessons din da coppers din makarantar sukan shirya mana kusan kullum dan shirin taryar jarabawar waec din da take gaban mu, to na kan samu kaina da rafka tagumi da hannu bibbiyu, idanuna tsaf a kan malamin, faffadan murmushi akan fuskata amma kuma sam babu abinda nake ji ko gani a abinda yake yi kuma yake fada, sau da yawa fuskar yayan kawata na kan gani a fuskar mai koya mana karatun, da kuma muryarsa yana cewa "smile, please".

Those were the good days....

On the bad days kuma ji nakan yi duniya tayi min zafi, in ji na tsani kaina for feeling what I was feeling, inyi kokarin tursasawa kaina daina jin abinda nake ji din amma sai inji kamar kara hura wutar abin nake yi a zuciyata. Nakan zauna inyi kuka a bayan idon kowa. Dama ni kuka babban abokina ne. Babu abinda nake so illa in sake ganin sa, ko in sake jin muryar sa, ko kuma at least in ji ko da labarin sa ne, ko da hirar sa ne ayi min. Sai dai kuma duk da halin da zuciya ta take ciki ba zan iya karya kambu na na yarinyar da tafi duk sauran yammata aji a set din mu ba, ba zan iya gayawa Mufida feelings dina a kan yayanta ba. Wannan zub da class ne right?

Wannan tunanin ya sa na tafi gurinta da niyyar in bugi cikinta ko zam samu abinda nake so, sai dai kuma matsalar daya ita ce tun ranar da na ganshi din sai ya zamanto tamkar anyi min chanjin babbar kawa ta Mufida ne da wata mai kama da ita amma ba mai halinta ba. Mufida yarinya ce mai shegen surutu, fadi ba'a tambaye ka ba, da son iyawa. Yana daya daga cikin abinda take so shine ta tara mutane tayi ta basu labarin gidan su da yan gidan su, kusan kaf set din mu babu wanda bai san yan gidan su Mufida ba, babu wanda bai san Yaya Doctor ba, amma tun ranar da yazo din sai ya zamana kamar ta saka sealtape ta like bakinta.

Na jawo kujera ta kusa da tata, nayi gyaran murya, ta dago daga karatun da take yi tayi min murmushi, nace "na gaji da karatu wallahi, kaina ya toshe" ta dafa goshinta tace "same here, kawai yi nake yi kar kuce bana yi" ta karashe maganar tana dariya. Nace "ni kaina ma ciwo yake yi" tace "ke ce fa health prefect, nasan ba zaki rasa magani a jakarki ba" nace "haka ne. Daga naji ciwo nake shan abina" na danyi shiru sai kuma nace "kuma a gida ai kunji dadin ku, gaku da Dr a gida, daga kun fara ciwo ba sai kunje asibiti ba sai kawai ya duba ku" ta dan yamutsa fuska "eh fa. Haka ne" Sai ta ja kujerar ta baya ta mike, "bara in dan zagaya insha fresh air ko kaina zai dan bude" na bi bayanta da kallo. She has been acting like that tun ranar visiting, what's up?

Haka na cigaba da jinyar zuciyata ni kadai, telling my self that the feelings will go away, but they never did, har yara suka dawo daga hutu muka kuma fara WAEC. Paper din mu ta farko bayan mun gama practicals ita ce geography, muka shiga muka fito ba tare dana tabuka komai na kirki a ciki ba, ni kaina nasan ko ni za'a bawa marking din paper ta ba xan bawa kaina credit ba indai ina so inga annabi. A cikin hall din na yanke shawarar cewa in dai ina son kaina da arziki kuma ina son inga abin kirki a result dina har in samu tafiya nursing school din da naji Abba ya ambata to kuwa dole in tattara Dr Umar Faruq dashi da idanuwan sa da murmushin sa in ajiye su a gefe. But how ......

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now