Musa

2.4K 148 2
                                    

*💔 Jidda 💔*

*By*

*Maman Maama*

*Episode Four : Musa*

Bayan mun gama ne naje nayi wanka na chanja kaya zuwa atamfa riga da skirt da dankwali, suna ta yabawa da sabon kitsona ni kuma ina complain din zafi yake min, sai Umma ta ce inje in gaishe da Hajiya sannan in shiga makota duk in gaishe su kafin Abba ya dawo.

A dakin Hajiya na tarar da ita tare da Mammy babbar yar mama Sa'a, lokacin sunyi Junior candy shine tazo zata kwana biyu a gidan.

Na gaishe da Hajiya, ta amsa babu yabo babu fallasa "an gama jarabawa ko? Allah ya bada sa'a. Saura aure kuma ko? Sai dai ke naga kamar har yanzu babu wani tsayayye, to Allah yayi zabin alkhairi"

Farhan da  take zaune a kan hannun kujerar da nake kai tace "ameen" tana kallo na da dariya, ni kuma na harare ta cikin wasa. Hajiya ta kalle ta tace "ke kam dai ai na roki baban ku ya bar min ke kiyi makarantar nan dai kema, kuma insha Allahu Allah zai dora ni a kansa tunda dai ke ce auta ai ba zai hana ba, ballantana yadda kike da kokarin nan dan Alhaji Kabiru ya gaya min ana saka ran zaki ci jarabawa sosai".

Farhan tace "insha Allah zan ci Hajiya. Kuyi tayi mana addu'a ni da Jidda mu tafi jami'a tare" Hajiya ta rike baki "Jidda kuma? Ke ma kinsan Jidda aure za'a yi mata musamman yadda tayi girman nan haka. Ita ma umman ta ai zata so taga nata jikokin tunda a kanta zata fara samu, su zo suyi ta danne ta itama" ta karasa tana ture Mammy da ta dora kanta akan cinyarta tana danne danne a yar karamar wayar da take hannunta.

Muka yi dariya gabaki daya, ta mike zaune tana bata rai sannan ta kalle ni sama sama tace "sannu da zuwa. An gama school. Congratulations" "thank you" nima na bata amsa a takaice. In da sabo na saba da rashin kunyar Mammy amma bana taba kulata saboda gudun karin raini a tsakanin mu.

Farhan ta karbe wayar hannun Mammy "marar kunya. Bani inga abinda kike aikatawa a wayar. Haka kawai mu manyan yammata ba'a bamu waya ba sai ke yar ficiciya da ke, wani in ya gani sai ya dauka ubanki wani abu ne a Kano" ta fada tana duba screen din yar karamar wayar data karba daga hannun Mammy. Ina kallon Hajiya tana hararar Farhan a fakaice, dan babu abinda ta tsana irin a fadi aibun wani nata a gaban mu ko wani wanda ya shafe mu, kullum nunawa take yi tamkar yayanta sunfi kowa komai bayan mun san ba haka bane ba.

Dariyar da Farhan tayi ce ta dawo da hankalin mu kanta, ta nuna min wayar "kinga, wai facebook take yi, dan Allah ji wani hoto da ta saka ita a dole yammata ce" na karba ina kallo, taci kwalliya an sha jambaki da uban gilashi, ga maza nan sun dage sai comment suke yi mata "WOW" "wow" "wow" sai kace wata jiniyar motar asibiti. Na rike baki nima ina dariya. Ta taso ta warce wayarta daga hannuna tana kunkuni ta shige cikin daki.

Farhan tace "kar dai ki zage mu, marar kunya, kin san ni yanzu sai in fasa miki baki wallahi, kuma wannan hoton kamar a kunnen uwarki, gwara tasan me kike yi da wayar". Ganin Hajiya har yanzu tana ta harare harare yasa na mike tare da cewa "bara inje in gaishe da Abba naji kamar ya shigo" tace "okay, wannan maganar sai kin tashi mayi" nayi murmushi, tatsuniyar gizo dai bata wuce ta koki, ba zai wuce zancen wani sabon saurayi ba ko something like that. Tun muna yra Farhan ce yar soyayyar cikin mu, kullum zancen ta baya wuce na samari ko aure ko wani abu mai kama da haka.

Ina fita na tsaya ina kallon saman Abba, kofar falon sa a bude take nasan yana ciki amma  gabana faduwa kawai yake yi dan ban san da wadda zai tarye ni ba. Haka muke ni da Farhan kullum fargabar zuwa gaishe shi da safe muke yi, in mun tafi a hanya kuwa munyi ta tunani ko akwai wani laifi da mukayi wanda ba'a yi mana fada a kansa ba. In kuwa dama mun san munyi laifi har kirkirar ciwon karya muke yi mu kwanta a daki mu ki zuwa gaishe shi amma har dakin ya kan biyo mu yayi mana fadan ko da kuwa muna karkarwar zazzabi ne.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now