The Sweetest Thing

2K 140 6
                                    

Na dan boye fuskata kadan a jikin kujera, yayi murmushi mai sauti sannan ya taso ya kuma dawowa kujerar kusa da tawa yace "amma gayamin, dan Allah wai Mufida bata san gidan nan ba? Kuma wai da gaske bata da number din da za'a same ki? Ni fa jikina yana bani wasa tayi min da hankali. Tana sane ta wahalar dani a banza"

Na dan juyo ina kallon sa ina tunanin ta yadda zan kare kawata. Wata idea ta zo min sai na sunkuyar da kaina nace "jiya ma munyi waya da ita. Suna can Lagos ko?" ya hada yatsunsa suka yi kara yace "I knew it. Yarinyar can ta shiga uku a hannu na, sai na yayyanka naman ta na cinye duk sanda na kama ta. Nace "kawar tawa? Besides, shi abu mai daraja ai dama sai an sha wahala ake samun sa ko? Duk abinda aka samu cikin sauki to anfi saurin wulakanta shi"

Ya rufe fuskarsa da hannu daya yana dariya a cikin kirjinsa sannan ya bude idonsa yana kallo na, ni kuma na rufe tawa fuskar sai yace "na gane, sai yanzu na gane komai. Issoryt. Wato kun hada kai ne dan ku ja min aji ko? Duk abinda nake ciki ashe kina sane ko? I like it, ina fatan dai naci test din?" Nace "ai ba test bane ba, screening ne dan muga how far you can go. Kayi passing first phase saura phase na biyu"

Na mike tsaye, shima ya mike da sauri "dan Allah, kar kice gida zaki koma. Ki barni na cigaba da ganin ki" nace "ganin kama da nayi yanzu a matsayin mai laifi nake. Ba'a gani na sai an samu izni daga Abba na. Ka neme shi, ka ganshi, kayi masa bayanin dalilin da yasa kake son ganin yarsa sannan in ya amince maka sai ka dawo' na juya zan shiga gida naji ya kira sunana "Jidda" na tsaya amma ban juyo ba, naji ya tako xuwa bayana ta tsaya sannan yace "zan je inga Abban mu, sannan zanyi iyakacin kokari na dan in samu karbuwa a gurinsa sannan zan dawo in sake ganin murmushin ki da license dina a hannu na"

Sai da na kai bakin kofa sannan na juyo, muka hada ido yayi min murmushi na mayar masa sannan na shige cikin gida.

Daren ranar is one of my happiest. Dan har sai da Farhan ta gaji da jin hirar Umar ta rufe kunnuwan ta da pillow. Duk da haka kuma ban fasa bata labarin sa ba har sai dana tabbatar tayi bacci sannan na kwanta nima na rufe ido na, fuskarsa ta bayyana gare ni, nayi murmushi, tabbas nasan yau dole ne ma ya shigo cikin mafarki na.

Two days after that, da yamma muna tsakar gida muna cin abinci tare da Farhan da Amira sai Hajiya ta leko daga barandar Abba ta kira ni, na amsa tace in zo inji Abba. Gaba na ya fadi na juya ina kallon Farhan, itama ni take kallo tace "me kika yi?" Na bude hannu "nima ban sani ba" Amira tace "an kira ki a court dole kinyi wani abu da sanin ki ko ba da sanin ki ba ko kuma wani yayi wani abu a gabanki zaki bayar da shaida" na hadiye abincin bakina mukut cikin tsoro sannan na wanke hannu na na hau saman ina karanto duk adduoin da suke cikin kaina, na tarar dashi yana cin abinci, Hajiya tana gefen sa tana yi masa fifita.

Na zauna nesa dasu kadan nace "Abba gani" sai da ya jima yana kallona, jin Hajiya bata ce komai ba na san cewa bata san dalilin kiran ba dan da ta sani da tuni ta fara fada tun kafin Abba ya fara, sai daya gama kallona sannan yace "waye Umar?" na dago kai da sauri, jikina ya fara rawa kamar marar gaskiya nace "na'am?" Ya maimaita "waye Umar nace, wanda kika tura office dina" na sunkuyar da kai na fara wasa da band din hannuna ina murmushi cikin jin kunyar su, this is serious, wato har yaje kenan, lallai da gaske yake kuma wannan ya kuma samar masa space mai kyau a zuciyata.

Jin nayi shiru ya saka Hajiya tace "saurayin ta ne ko?" Yace "eh haka yace min, amma so nake in san a inda suka hadu dashi, yace min a gadon kaya gidan su yake, ita kuma bata da kowa a can, a ina ya ganta?" Hajiya tace "zai wuce a waya?" Ya ajiye chokalin hannunsa yace "waya? Yaushe Jidda tayi waya ban sani ba, waye ya siya mata?" Tace "a'a ba waya ce da ita ba, amma ai suna ɗaukar wayoyin mu suna amfani dasu, zata iya yiyuwa wayar Umman ta ta dauka tayi wannan chatting din nasu na zamani anan suka hadu, kasan yaran yanzu sai addu'a"

Na bude ido ina mamakin yadda za'a yi min sharri ina zaune da raina, nace "a'a Abba ba haka bane ba, yayan Mufida ne fa, yayan kawata ne" ya mayar da hankalinsa kaina yace "yayan kawarki? Yaushe kika je gidan su kawar taki har ya ganki? Ni dai ban san lokacin da kika tambaye ni cewa zaki je gidan su kawarki ba" na sunkuyar da kai na, "a makaranta ne, ranar da muka gama makaranta yaje daukan ta ni kuma na raka ta mota, shine .......shine......kuma sai yazo nan shekaran jiya sai nace yaje  ya same ka"

💔 JIDDA 💔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora