The Wedding Night

2.1K 155 9
                                    

Gidan Umar yana rijiyar zaki, flat ne madaidaici dai dai karamin family. Falo ne madaidaici, a cikin sa akwai kofofi guda uku, daya zata shiga da kia guest room mai hade d guest toilet, daya zat shiga da kai dining room wanda ta cikinsa zaka shiga kitchen, a cikin kitchen din akwai store da kuma dan karamin dakin yan aiki sai kuma kofar da zata fitar da kai backyard, daya kofar kuma ta falo zata shiga da kai corridor din da daki na dana umar suke kallon juna.

Komai na gidan ni dai zance yayi min, dan Umar yayi iyakacin kokarin sa gurin tabbatar wa yayi komi dai dai da zamani sannan nima iyaye na t nadu bangaren sunyi matukar kokari gurin zub kayan da suka dace da gidan, komai yaji sai san barka sai kuma fatan alkhairi.

A falo su Aunty suka ajiye ni akan kujera, suka zauna suma ta hira da barkwanci da yan gidan su Umar waɗanda suka zagaye ni suna ta tsokana ta da neman lallai sai sun bude min fuskata, ni kuma na kankame mayafina na kuma takure a jikin aunty ina karasa sauran kukan da ban gama ba, tsoro na Allah tsorona su Aunty su ce zasu tafi. Ai kuwa basu wani jima sosai ba suka fara shirin tafiya haka suma yan uwan Umar banda su Mufida da suke a matsayin kawayena, nan na sake bude wani sabon babin na kuka kawayena suna ta tsokana ta.

Farhan tace "munafuka, Aunty ganin ku ne fa ya saka take wannan abin, bara ku gani yana zuwa zaku ganta tana ta zagba masa murmushi, idan da zaku ce tazo ku tafi tare da ita cewa zata yi ba zata bi ku ba" Mufida tace "wallahi kuwa, kukan munafurci ne. Kuma wallahi in yazo naga hakorinki a waje sai nayi miki hoto na nuna wa kowa ya gani" yaya Hudallah tace "kar ku takura mata, wa yaki auren soyayya? Auren soyayya ai dadi ne dashi. Kana son mijinka shima kuma yana sonka me yafi wannan dadi?"

Maryam tace "ballantana miji irin yaya Doctor. Gaskiya Jidda tana daga cikin mata masu saa a duniya. Ta samu miji ga kyau ga kudi ga tarbiyya ga ilimi uwa uba kuma gashi yana balain sonta"

Sai hirar da juya ta koma akan irin dacen da nayi da miji, duk a kokarin su na making me feel better kuna naji dadin sosai dan ina so inji ana yabawa Umar. A haka sukayi ta zame jiki suna tafiya.

Bayan sun tafi ne na dan bude fuskata da kumburarrun idanuwa na, Farhan ta matsa min wai lallai sai na sake wanka ni kuma naki yi tunda da zamu taho bayan magrib sai da nayi wanka kuma yanzu bayan ishai sai in sake wani? Sai kace kwaduwa? Banyi wankan ba dai amma na dan gyara fuska ta, sai kuma barin turare da Mufida tayi min a jiki kala kala ta ringa fesa min a kowanne loko na jikina, suka hadu suka gyara gidan fes suka kuma saka turaren wuta a ko'ina yadda daga ni har gidana duk kamshi muke yi, sai kuma zaman jiran angwaye.

Anan falo muka zauna jiran su, su Mufida su uku, Farhan da Aira, Maryam, sai kawayena na school of nursing su uku. Angwayen ba su zo ba sai tara da rabi, kamar yadda muka yi tsammani classy abokan sa bisa jagorancin Bashir su suka rako shi, tun daga waje muka jiyo hayaniyar su daga dukkan alamu tsokanar sa suke yi, muka yi sauri muka shirya Farhan har da kara rufe min fuska tana tuna wa sauran kawaye irin kudin da zasu karba a matsayin na siyan baki.

Sai dai suna shigowa Umar bai bi ta kan kowa ba ya doso inda nake gadan gaban, ina jin kawayena suna retaliating, Mufida har da zuwa gabana ta tsaya tare da rike kugu, yana zuwa ya saka hannu daya ya ture ta gefe sannan ya saka hannu biyu ya kama nawa hannayen ya mikar da ni tsaye sannan ba tare daya jira komai ba ya jawo ni zuwa kirjinsa ya rungume.

Ina jinsa ya sauke sassanyar ajjiyar zuciya yana kara matse ni a kirjinsa, sannan a hankali yace "welcome home Baby" naji murmushin da Farhan take cewa zanyi yazo fuskata sannan a hankali nayi rising hannayena da suke sides dinsa na hade su a bayan sa tare da cewa "thank you dearest". Sannan na lumshe idona ina shakar daddadan kamshin sa.

Ihu da sowar yammata da samarin ne ya saka ni bude ido na, sai kuma na sake shi ina kokarin ture shi cikin jin kunyar su. Ina jin Farhan tana cewa "munafuka na dauki hoton ki ai sai na nuna wa Aunty da Umma" na juya side din ta ina yi mata alamar roko. Umar ya sake ni shima sannan ya rike hannuna muka juya muna kallon su, kusan kowa da waya a hannun sa yana daukar mu hoto, a raima mace na shiga uku shikenan za'a ga hoto na a rungume a jikin namiji, sai wata zuciyar ta tuna min cewa namijin ai miji na ne kuma Umar dina ne and I felt I don't care, the whole world can see it.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now