The Wedding

2K 105 8
                                    

Tana fita Farhan ta shigo, kallo daya tayi min ta taho inda nake da sauri tana dafa kafada ta "me tace miki? Ni banga shigowar ta ba wallahi sai fitar ta na gani, wani abin ta gaya miki?" Nayi saurin girgiza kai na duk da masan kamanni na kadai sun isa su tabbatar mata karya nake yi. Sai dai maganar gaskiya ba zan iya gaya wa kowa maganar nan ba not even Farhan, kuma nasan sanin hakan ne ya saka itama Yaya Jamilar ta gaya min, wannan kuma ya saka zuciya ta ta cigaba da gaya min cewa karya take yi.

Farhan ta zauna a kusa dani tana dafa ni, "me tace miki Jidda? Menene zai bata miki rai haka a lokacin bikin ki?" Na danyi gyaran murya dan magana ta fito daga makogwarona da nake jinsa a toshe "babu abinda tace min, kawai dai maganganu ne irin nata akan wai yadda Umar ya yaudareta and other stuffs" Farhan tayi tsaki "na sani dama, na san sai ta tayar da maganar a bikin nan wallahi kuma gashi gobe a gidan su za'a yi kamu yadda zasuyi ta fadar maganganu ita da yan uwan ta, ni wallahi da an chanja venue din gobe ma" sai ta mike tayi hanyar fita "bara inje in gaya wa Aunty Afia"

Kamar zan hana ta kuma sai na barta dan ina son in samu quietness din da zanyi magana da zuciyata. Zuciyar da naji tana tsatstsagewa gunduwa gunduwa. Na saka yatsuna na kuma toshe kunnuwana da har yanzu suke amsa amon maganar ta "I gave him myself" na runtse idona tareda girgiza kai na. "Karyar banza" na fada a fili. "Karyar wofi" na maimaita. "Muguwar ƙatuwar karya" na fada da dan karfi tare da yin jifa da pillown da yake kusa dani, a dai dai lokacin da Aunty Afia ta bude kofa suka shigo tare da Farhan "shashancin me kike yi haka Jidda?" Ta fada tana kallona. Na sunkuyar da kaina ina jin numfashi na yana fita da sauri "babu komai Aunty" ta rufe kofar "babu komai kike jifa da pillow?" "Babu komai" na sake fada ina jin hawaye yana tahowa idona.

Sai ta karaso ta zauna a gefe na Farhan ma ta zauna a daya side din, haka suka yi ta tambaya ta amma naki gaya musu komai, it would have created a scandal idan na fada ko da kuwa anyi finding out cewa karya ne to kuwa wasu ba za su yarda cewa karya ne ba.

Haka ranar na karasa wuni a daki, duk wanda ya ganni da safe sannan ya ganni bayan zuwan Yaya Jamila tabbas zai fahimci chanjin yanayi a tare da ni, wadanda suka san abinda yake tsakanin mu sunyi guessing ita ce silar chanjin mood dina, wadanda kuma basu sani ba sai suke tsokana ta da cewa ko har ma fara tunanin rabuwa da gida ne.

Tun bayan tafiyar Jamila Umar yake ta kirana a waya, ina jin wayar kuma nasan shi yake kira amma ko kallonta banyi ba ballantana in dauka, kawai bana jin zan iya yi masa magana yanzu duk da cewa kaso casain na zuciyata yana gaya min cewa karya tayi masa dan ta rama abinda take tunanin yayi mata, but duk da haka sai naji ina bukatar break from him. Daga karshe dai dole ya hakura ya daina kira

A haka har aka watse daga taron, har akayi magrib, ina yin sallar na koma na kwanta akan sallaya ta na rufe idona kamar mai bacci duk da ba baccin nake yi ba kawai dai bana son ake yi min magana ne. A haka naji wayata ta cigaba da ruri na kidan da na saka musamman saboda Umar, sai a lokacin na tuna da cewa munyi alkawarin zai zo yaga kunshina yau da magrib. Na mika hannuna na dauko wayar sannan ba tare da na ko kalli sunansa ba na katse kiran sannan na kashe wayar gabaki daya na cusa ta a kasan pillow na, a raina ina jin bazan iya ganin sa ba har sai na goge wani dan digo da nake ji a zuciya ta na cewa Jamila gaskiya ta fada.

Naji an murda kofar dakin an shigo, na daga kai ina kallon Farhan da ta shigo da plate din abinci ta ajiye a gaba na tana magana kasa kasa duk da bana jinta amma na san mita take yi akan yadda banci abinci ba tun rana.

Wayarta tayi kara ita ma, ta daga tana murmushi "ango kasha kamshi" nayi saurin kallonta dan na fahimci da wanda take magana. "Wallahi ka ganta nan tun azahar a kwance" "eh Yaya Jamila ce tazo, bamu san me ta gaya mata ba shikenan mood dinta ya chanja take kwance" "ta tafi tun dazu, tana zuwa ko five minutes bata yi ba ta fita" "a'a dan Allah kar kaje gidan su, kaga yanuwan mu ne fa, wannan ma sabanin da aka samu so muke a gyara shi" "okay gata" ta fada sannan ta dora min wayar a kunne na.

💔 JIDDA 💔Onde histórias criam vida. Descubra agora