Ummi

2.3K 137 7
                                    

Kafin in bashi amsa ya bude kofa ya fita, na jima a zaune, na kasa ma yin addu'a dan lugude kawai kirjina yake yi, anya kuwa sauran amare haka suke jin tsoro irin wannan? Anya kuwa ni nawa tsoron bai yi yawa ba?

Amma kuma shima kansa Umar din is not helping matters at all, shine ma yake kara tsorata ni wallahi. Misali yanzu, menene na wani cewa in tashi mu tafi yanzu, making me think of what will happen in munje gidan.

Na tashi na nade sallayar sannan na fara kokarin gyara fuska ta. Aunty ta shigo "ashe tafiya zakuyi Jidda? Yanzu naji Umar ya aiko wai ki fito in kin kammala"

Na dauke kaina gefe na juya idona, wato yasan in ya aiko zasu matsamin in fita tunda yana jira na,amma in ba haka ba ai ya gaya min already kuma zai iya kirana a wata ya sake tuna min.

Na juyo ina kirkirar murmushi, "eh Aunty, tafiya zamu yi" sai ta jani muka zauna a bakin gadon ta sannan ta jawo drawer ta dauko wata leda ta miko min "kinga wannan sister ta ce ta kawo min, sai naga da amare yafi dacewa shine nace bara in baki" na karba jikina yana bani ko menene a ciki, nayi mata godiya.

Sai kuma ta sake karba ta bude tana yi min bayanin yadda ake using. "Kinga wannan ma ance kamar yanzu za'a sha, bara in hada miki ki shanye kafin ku tafi dan in nace in kunje ki sha ba lallai ne ki sha ba" ta fita sannan sai gata ta dawo da cup a hannun ta ta bani ta ce in shanye, ina cikin sha ya shigo dakin yana duba agogon hannun sa, Aunty tace "gata nan zuwa sarkin gaggawa, wannan kai da maye ne in ka kama mutum sai ka kai shi lahira zaka rabu dashi" sai yayi murmushi kawai bai ce komai ba ya fita.

Muka fito palo nayi wa Mama sallama, sai ta bani wata leda ita ma ta gaya min spices ne a ciki na girki, "in akwai wani abun da kuke bukata a gidan ki kira auntyn ku ki gaya mata, kar ki kira gida, shi kuma in kin gaya masa ba lallai ya san inda zai samo muku wani abun ba, a hankali kema zaki san inda zaki samu komai. Na bayar ma za'a yi muku garin kunu tunda yana so, za'a aiko muku da shi" na durkusa nayi mata godiya na kuma yi mata fatan Allah ya kiyaye hanya.

Afnan tazo ta zauna a kusa dani tana yi min rada "Aunty zan biki kinji?" Na shafa kanta nace "maza dauko kayanki mu tafi" sai ta mike da sauri tana murna "mommy ki hada min kayana aunty Jidda ta yarda zan bita" Affan ya mike "wallahi nima sai naje mommy" Aunty ta girgiza kai "kuna da school gobe, ku bari sai da weekend sai kuje kuyi musu two days" Mama tace "da weekend din ma suna da islamiyya, sai dai in anyi hutu" suka fara rikici, sai na rarrashe su da cewa ai an yi hutun sai suje suyi min two weeks.

Sai dana fadi haka sannan suka fara murna, a lokacin ne kuma naji ana maganar Ummi ita ma bata nan akayi bikin sai anyi hutu zamu hadu, ban gane wacce Ummi suke nufi ba kuma ban tambaya ba.

Umar ya sake lekowa. Ya tsaya kawai a bakin kofa ya saka hannu a aljihu yana kallon mu. Hajiya ta taba ni "tashi maza ku tafi yana jiran ki, kinsan unguwar ku da nisa" ina mikewa ta kwalla wa Mufida kira tace tazo ta karbi kayan hannuna sannan ta dauko mana abinci a kitchen mu tafi dashi tunda bamu yi dinner ba. Mufida ta fara buga kafa tana shagwaba, "Mama ita ta dauko mana da kanta" Aunty tayi dariya "yayarki ce dai yanzu ko kin ki ko kinso" ta juyo tana harara ta ni kuma na yi mata gwalo sannan na sake yiwa su Mama sallama na fita.

Yana cikin mota a zaune, sai na tsaya a jikin motar ban shiga ba, na sauke glass yana kallona amma bai yi magana ba, nace "Mufida nake jira, zata kawo min kaya inji Mama" sai ya dage glass din. Sai naji ni bana son wannan shirun nasa, fushi yake yi dani na sani. Na hadiye yawun tsoro.

Mufida ta fito tare da Muhsina, suka saka mana kayan a mota sannan mukayi sallama na bude gaba na shiga na rufe.

Bai ce min komai ba ya tayar da motar muka fita muka hau titi, na juya ina kallon sa ta hasken street light ina jujjuya hannuna nace "kayi hakuri" ya juyo yana kallo na "hakurin me fa?" Na mayar da kaina kasa, "naga kamar kayi fushi ne" yace "fushin me zanyi?" Nace "akan abinda nayi" yace "me kika yi" na ji kamar zanyi kuka "dana boye maka gaskiya" yace "gaskiyar me fa?" Na fara yarfa hannu na "aika san maganar da nake yi wallahi kawai so kake ka nuna baka sani ba"

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now