The Denial

1.7K 131 8
                                    

Wahalar da nasha a attack din dana samu yayi exhausting dukkan karfi na, hakan yasa duk da halin da zuciyata take ciki sai da bacci mai nauyi ya dauke ni a jikin Farhan.

Sanda na tashi ni kadai na ganni a dakin, daga alama rana ta fito sosai

Na mike zaune nayi salati tare da dafe goshina, ko kadan ban manta abinda ya faru ba duk da cewa ganin shi nake yi kamar a mafarki, ina tunawa da yadda Abba yayi biris da maganar yayi kamar ba wani abin da za'a yi doguwar magana bane ba a kansa, na kuma tuna da hukuncin da ya yanke a karshe, wai Umar zai iya auren mu mu biyu ni da yaya Jamila in dai yana son haka shi bashi da problem. Na mike tsaye da sauri dan tabbas ni ina da problem da haka.

A palon Umma na same ta a zaune da kayan abinci a gabanta, daga dukkan alama bata dade da gama breakfast ba, babu kowa a tare da ita dan nasan Amira tana school. Na zauna a gefenta cikin matsanancin sanyin jiki, ta bini da kallo har na zauna sannan tace "ya jikin?"

Na gyada kai kawai ina jin babu isasshen yawu a bakina balle in amsa mata, ta dauko flask din gabanta ta zuba min kunu sannan ta miko min "ungo ki sha" na karba na ajiye a gabana ina zagaya dan yatsa na a rim din kofin sai ta fara magana

"Nasan kinji maganar da gwoggon ku tazo da ita, farko ni ma kamar yadda hankalin ki ya tashi haka nawa hankalin ya tashi akan maganar amma kuma da baban ku ya sauko ya yi magana sai naji hankali na ya kwanta" na dago kai da sauri ina kallon ta sai tace "ba wai na yarda da maganar sa bane ba ko ina goyon bayan abinda yace ba a'a ina nufin na fahimci abinda ya faru.

"Jidda ke yarinya ce amma duk da haka nasan zaki fahimci cewa namiji ba mijin mace daya bane ba, da wahala ki ga saurayin da yake da budurwa daya, bance ba'a samu ba amma da wahala, haka zalika shima mai auren da wahala ki ga wanda bashi da wata budurwar kuma, haka Allah ya halicce su shi yasa ya basu damar auren mata har hudu in dai zasu iya"

"ba abin mamaki bane dan Umar yana soyayya da ke kuma da Jamila a tare, watakila nufin sa ya aure ta bayan ya aure ki, kuma ba zamu ce yana da laifi ba akan hakan tunda addini ya bashi dama, amma abinda nafi tunani nima kamar babanki shine bai san dangantakar da take tsakanin ku ba, bai ma san kunsan juna ba. Sai dai abinda ban yarda dashi ba a maganar babanku ita ce na cewa zai iya hada ku, kamar yadda Habibah tace ba zata bar hakan ta faru ba ni ma ba zan bar hakan ta faru ba dan tabbas zai iya raba zumunci a tsakanin ku"

"Dan haka yanzu tunda Allah yasa lokaci bai kure ba sai mu dauki mataki, ki dauki waya ki kira shi kice kina son ganinsa, in yazo ki tambayeshi game da Jamila ki kuma fada masa dangantakar da take tsakanin ku sannan ki tabbatar masa da cewa ba zaku zauna kishi ba, ki bashi dama ya zaba ko ita ko ke. Idan  ke ya zaba to ki tabbatar masa cewa iyayen Jamila ba zasu bashi ita ba indai ya aure ki, tsakanin sa da ita sai dai mutunci a matsayin ta na yaruwarki. Idan kuma ita ya zaba to ya janye maganar aurenki ya kuma aiko a karbar masa kudinsa da sauran kayansa, ke kuma Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi".

Na gyada kai na da sauri ina yadda da hukuncin ta, amma kuma wani bangare na zuciyata yana cike da tsoro "what if ya zabe ta? Zan iya rayuwa babu shi anya kuwa?"

Na mike da wayata a hannu, sai Umma ta dakatar dani tare da nuna min kunun data zuba min, na zauna na shanye ina bata fuska kamar mai shan magani, ina gamawa na dauki waya ta na koma dakin mu. Missed calls din Umar na gani har guda biyar a dai dai time din daya saba kira na kullum dan yaji yadda na kwana.

Nayi dialing number din sannan na saka a kunne na. Seconds biyu ya dauka

"Hey Baby"

Na lumshe ido na na bude ina jin muryar sa tana taba zuciyata. "Hi" na fada da muryar da naji kamar ba tawa ba.

"What's up Baby. Naji muryar ki wani iri ko yanzu kika tashi daga bacci?" Na girgiza kaina kamar yana kallo na ina jin hawaye yana kawowa ido na, nayi kokarin boye emotions dina nace "lafiya lau. Kana ina?" Yace "ina office, nayi ta kira dazu ai kina ta bacci ko? Are you sure you are okay?" Nace "ina so ne in ganka yanzu, if you are free, akwai maganar da nake so muyi" ya danyi shiru sannan yace

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now