Engaged

1.9K 127 1
                                    

Soyayya muke yi da Umar mai ratsa zuciya da ruhi, Umar baya iyayin kwana uku ba tare da yazo gidan mu ya ganni ba haka nima duk inda ya kwana biyu bai zo basai inji ko abinci ma baya tafiyar min sosai.

Cikin kankanin lokaci duk jama'ar gidan mu da wadanda suke cikin gidan da kuma wadanda basa ma gidan a lokacin amma sun san labarin Doctor Umar saurayin Jidda, a lokacin na kuma fahimtar abinda ake kira da yan'ubanci dan kiri kiri Hajiya da yayanta suke nuna rashin jin dadin su da irin saurayin da na samu, a inda ita kuma Umma take sakin bakinta tayi ta mayar da magana a duk lokacin da aka jeho mana ita. Amma wannan sam bai taba amintakar mu da Farhan ba, su suna harkokin su mu muna namu.

A bangaren Umar shima a yanzu duk yan gidan su sun san da zama na kuma sun san abinda yake tsakanin mu, dan ranar nan kawai sai ga Mama ta kira Umma a waya wai ta kira ta su gaisa, haka Aunty ita ma ranar nan ta kira. Mufida ma yanzu ta fahimci yayanta da gaske yake dan haka ta saki jiki da maganar musamman yanzu da suka gama hutunsu a Lagos suka dawo Kano Umar ya samu damar yin amfani da ita wajen yin waya dani, ya kansa ta kirani in karbi wayar mu gaisa sai yace in rike wayar kar in mayar wa da Umma sai shi kuma ya kira ni da layinsa.

Soyayyar Umar mai dadi ce, irin mai tsayawa a rai din nan ce, kalaman sa masu dadi ne dan zan iya cewa Allah yabashi baiwar tsara kalamai yadda duk wanda aka gayawa sai sun shige shi kamar yadda kullum suke shiga ta.

Kamar yadda Umar yayi min alkawari haka ya tsaya kai da fata, da karfinsa da lokacin sa da kuma aljihunsa wajen ganin yayi min securing admission a school of nursing, har Allah ya taimaka aka samu din. Sanda aka samu da kansa ya dauki takardar ya kuma dauki mota ya tafi office din Abba yaje ya kai masa, Abba yayi murna sosai ya kuma saka albarka. Sai kuma Umar ya sake rokonsa wata alfarmar daban "Abba nace idan babu damuwa idan kuma ka amince ina roka mata alfarmar ta fara rike waya, saboda harkar makaranta idan babu waya a hannunta karatun ba zai tafi mata dai dai ba, saboda yanzu ma in taje registration dole akwai inda za'a bukaci number din ta kuma......." Abba ya daga masa hannu "na sani, nasan duk wadannan tsarikan. Doctor Umar kana son Jidda ne zaka aure ta?" Umar ya sunkuyar da kai yana shafa keya, sai da Abba ya maimaita tambayar sannan ya amsa "eh Abba haka ne" sai Abba yace "to in ka koma gida ka turo min magabatan ka muyi magana da su".

Yana komawa gida nima ya aika aka kirawo ni "banyi niyyar aurar dake a yanzu ba Jidda, niyya ta sai shekara mai zuwa zan aurar daku ke da yaruwarki, kuma har yanzu ina kan wancan niyyar sai dai dole a danyi wani motsi dan bana son ki fara makarantar nan haka kai tsaye, gwara ko babu aure ace da baiko" ya miko min admission letter din tare da yar karamar Nokia phone. Na saka hannu biyu na karba, ya cigaba "kin samu makaranta ga takarda nan dazu Umar ya kawo min,ga kuma waya nan dan zaki bukace ta a hidimomin shiga makarantar, sannan kuma sanda ya kawo min na gaya masa nace ya turo magabatansa dan muyi magana dasu" na kasa cewa komai dan na kasa tantance menene nake ji a zuciyata.

Ya cigaba "ina fatan dai har yanzu shine zabin da kike dashi a zuciyar ki? Ko kin chanja?" Na girgiza masa kai a hankali. Ya daga hannunsa "shikenan, tashi kije, zaki iya amfani da wayar amma da sharadin in har na kama ki da laifin yin amfani da ita ta wata hanyar da bata shafi karatu ba to ba wayar kadai zan karba ba har makarantar zan hana zuwa".

Nayi godiya sannan na tashi na sauka kasa ina jin wani iri a raina.

A falon Umma na same ta ita da Amira na ajiye mata kayan hannuna a gabanta sannan nayi mata bayanin duk abinda Abba ya gaya min. Ta dauki takardar tana dubawa, fuskarta tana nuna jin dadin samun makaranta "kai! alhamdulillah, Allah mun gode maka. Kai wannan yaron Allah yayi masa albarka. Hausawa dama sunce juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta wannan jumaar alamu sun gama nuna mana mai kyau ce insha Allah. Allah yasa kin shiga a saa shi kuma da ya tsaya Allah ya saka masa da alkhairi".

💔 JIDDA 💔Où les histoires vivent. Découvrez maintenant