The Visit

2.3K 136 2
                                    


Episode Five : The Visit

Free Episode

Ranar dana kwana goma a gida ne na gaji da jiran kiran wayarsa nayi deciding zan kira Mufida watakila ko zan samu wani labari a kansa a gurinta, duk da dai nasan cewa pride dina ba zai barni in tambaye ta shi ba. Na dauko slum book dina na nemo number din ta na kira a wayar Umma, bugu biyu ta dauka "Hello?" Nace "hey Mufida" sai tayi dariya cikin murna tace "Jidda? Wow. Ko da yake nayi fushi, ke da mukayi da ke cewa kina zuwa gida zaki kira ni amma sai da muka kwana goma sannan zaki kira?" Nayi murmushi "kiyi hakuri yammata, ko da yake ai bai kamata in baki hakuri ba tunda kema ai kina da number din Umma mai yasa baki kira ni ba? Dan haka laifin ba nawa bane ba ni kadai" sai tayi dariya kawai.

Muka yi ta hirar mu, kowa yana bayar da labarin abinda ya faru bayan zuwan mu gida, a lokacin ne take bani labarin zasu tafi Lagos suyi hutu gabaki dayan yan gidan su "banda yaya doctor tunda shi yana aiki" a wannan statement din ne kawai ta ambaci sunan sa, ban nemi karin bayani ba kuma nima ban ambace shi ba har muka yi sallama. At least dai naji cewa he is fine, sai dai wannan ya saka na sake shiga wani tunanin, tunanin dalilin da yasa bai neme ni ba har yanzu.

A ranar ne kuma da yamma muna cin abinci tare da Umma da Amira, sai ga Abba ya shigo falon, ya zaro kudi daga aljihunsa ya ajiye akan kujera yana kallona yace "ki shirya gobe da safe ki tafi ki zagaya gidajen yan uwanki, mazan kowa kiyi masa kwana biyu matan kuma kwana daya, sannan ki je gidan Aunties dinki Habiba da Afia suma kiyi musu kwana dai dai. Na amsa da "to" kaina yana kasa ina jin babu dadi a raina, duk yayyen nawa ba wani jin dadin juna muke yi ba dan haka ba dadin ziyarar zanji ba, Umma ta gyara zama tace "amma da an barta tayi wa Afia kwanaki da yawa, yaushe rabonta da ita? Ba ka taba barinsu suje su kwanar mata ita kuma nata yayan duk hutu sunanan gidan. Dan Allah ka barsu suyi sati ita da Amira. Ita kadai su ke da ita a matsayin dangin uwa" direct yace "kwana daya nace, kuma ita kadai, idan kwana dayan bai yi ba to tayi zaman ta" ya juya ya fita. Duk muka yi shiru kowa ransa babu dadi sai kuma muka ji shi ya dawo yana kwalla wa Farhan kira yace "ki shirya ki bi Jidda zaku zagaya yan'uwa" sai kuma ya sake fita.

Umma tayi dan karamin tsaki. Wato ya hada ni da Farhan dan kar in ki yin yadda yace. Amma ni sai naji dadin hada ni da Farhan din da yayi, at least zan fi jin dadin tafiyar akan ace ni kadai ce.

Umma ta dauki kudin daya ajiye tana kirgawa sai ta sake wani tsakin "wannan ai ba zai ishe ku ba, tunda ku biyu ne yanzu, sai dai inya dawo ita sai ta je ta karbi nata tunda wannan ke kadai ya bawa" Amira tace "gashi inda zasu je babu mai basu kudin mota, sai dai ko gidan Aunty Habiba da gidan Mami" Umma ta tabe baki tace "su samu abinda zasu saka a cikin su first kafin suyi tunanin a basu kudin mota. Su kansu nema suke ballantana su bawa wani".

Ban kuma tabbatar da maganganun Umma ba sai da muka je, gidan Mama Sa'a muka fara zuwa, ƴaƴan ta shida, Mammy ce babba kuma tana jss3 a lokacin, amma sai da muka kirga yaya sunfi ashirin a gidan, duk yayan kishiyoyi da mijin yake aura yana saka ana tarawa Mama Sa'a su, ita ma kuma abinda muke tunanin ya saka take gidan har yanzu shine saboda yadda take daukan duk wani wulakancin sa dan tasan in ta mayar masa ya sake ta to bata da gurin zama a gidan mu ita kanta ballantana ƴaƴan ta, ita kuma yadda take sane da yanayin gidan ba zata iya tafiya ta bar yayanta a cikin wannan halin ba.

Mugu ne na karshe, daga matan har yayan tsoronsa suke ji kamar wani dodo, sai dai jin dadin su daya shine basu rasa ci ba ba kuma su rasa sha ba, ba dai za'a ce suna da komai ba amma basu da yunwa. Sai dai yawan yayan da kuma rashin kulawa daga uban ya saka rasa tarbiyya. Idan kaji yaran suna zabga ashar zaka dauka yayan maguzawa ne, basu kyale kowa ba har matan uban zagi suke yi uban ne kadai basa zaga shima kuma dan sun san jikin su ne zai gaya musu.

Kallo daya zaka yi wa Mama Sa'a ka fahimci cewa ba jin dadin zaman take yi ba, bakin ciki ne fal a zuciyarta babu wanda zata iya budewa zuciyarta.

💔 JIDDA 💔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang