The Ladies' Doctor

1.9K 148 11
                                    

Kamar yadda yayi alƙawari haka ya dawo washegari da yamma ya kawo min form din, sai dai cikin sauri yazo ina karba ya juya ko godiya bai tsaya nayi masa ba. Na shiga gida da takardar a hannuna jikina a sanyaye dan bansan abinda zai biyo baya ba. A cikin daki na samu Umma tana sorting kayan da aka kawo daga gidan wanki, na zauna a bakin gado tare da mika mata takardar. Fuskar ta da alamar tambaya ta karba tana dubawa tare da tambayar "takardar menene?"

Nayi shiru ban amsa ba sai da ta karanta heading din sannan tace "wannan ai kamar form ne na school of nursing" na gyada kai "eh Umma, Umar ne muka yi magana da shi nace ina son nursing sai kawai ya siyo ya kawo min, kuma yace in cike kafin ya dawo zai karba" ta fara girgiza kanta "kinsan babanku ba zai yarda ba, babanku ba zai bari ba, me yasa kika karba?" Naji hawaye ya taho min,

"Umma kawai na gaya mishi ina son karatu ne, kawai na gaya mishi ina son nursing ne, shine ya siyo min. Umma yanzu in ban cike ba in yazo karba me zance masa kuma?" Ta ajiye takardar tare da cigaba da jera kayan da take yi amma daga ganin fuskarta kasan a cikin tunani take, sai ta juyo tana kallo na sannan tace "idan baban ku ya dawo in an jima, in yana zaune shi kadai kije ki same shi ki kai masa takardar ki gaya masa yadda kuka yi da Umar din, sai kiji abinda zai ce, in Allah ya dora mu a kansa sai ki ga ya bari tunda naga kamar yana son Umar din, in kuma bai bari ba sai ki hakura ki gaya wa Umar din gaskiya ba'a barin ku kuyi karatu a gida sai in kunyi aure, in yaso in da gaske yake maganar auren da kuma maganar karatun sai ya bari in kinje gidan sa sai ya saka ki a can".

Na share hawayena tare da gyada kaina, already har na fara karanto adduoin da zaku dora ni akan Abba dan ban san yadda zanyi wa Umar bayanin bama karatu sai a gidan miji ba, it will sound like ina gaya masa aure za'a yi min yayi gaggawar fitowa, ni kuma pride dina bazai barni in fadi haka ba.

Ina daki naji shigowar Abba bayan Sallar magrib, ina ji kuma Hajiya ta hau saman ta kai masa abinci, amma nasan zai sauko yaje masallacin isha itama kuma zata sauko kuma in ya koma sama zai ji labarai ita kuma zata yi kallo a kasa ba zata koma ba kuma sai goma da rabi zuwa sha daya. Wannan lokacin shine target dina.

Sama sama naci abinci, Farhan kuma tana waje tana zance da Sulaiman, ina jin Abba ya dawo ya koma sama sannan naji ya kunna radio, na tashi na shiga daki na dauko form din na saka hijab dina na fita, na jima a tsaye ina karanto adduoi sannan na hau. Yana baranda yana kwance akan karamar katifar da ake shimfida masa anan musamman idan babu nepa, nayi sallama ya amsa sannan na durkusa daga dan nesa da shi kadan.

Ya rage radion sa kadan sannan yace "Hauwa'u? Ya akayi?" Na fara inina "Abba dama.......uhm dama zuwa nayi.....uhm takarda ce dama.....? Ya mike zaune "ki gaya min abinda kike so ki fada, ko kuma ki tashi ki koma in kin shirya sai ki dawo. Wacce takarda kike magana akai?" Nayi sauri na mika masa Form din hannuna inajin hawaye already yana tahowa, na tsani wannan saurin kukan nawa amma hali na ne a jikin rai na yake.

Ya karba yana haska touchlight dinsa a kai, nayi saurin cewa "Umar ne ya kawo min dazu, nima ban san zai kawo ba kawai dai nace masa naji kace kana so inyi nursing shine ya kawo min form" ya dago ya kalle ni sannan ya mayar da kansa ya na karanta takardar, jin yayi shiru kuma bai wurgo min takardar ba ya saka na samu courage din cigaba. "Shine na kawo maka dama in gaya maka, sai in ka yarda kuma kace in cike sannan sai in cike, in kuma kace a'a sai in mayar masa" ya ajiye takardar yace "wannan takardar wahalar samu ne da ita, ya akayi ya samu cikin sauki?"

Nace "akwai abokin sa a gurin, kuma shima kaga kusan duk harkar su ce" ya sake yin shiru yayin da zuciya ta take bugawa. Sai kuma ya gyara zama yace "naga kamar da gaske yake, tunda har sai daya bi ta gurin aboki na sannan yazo gare ni. In har aurenki zai yi da gaske to zabin sa ne kiyi karatu ko a'a, amma ni inaso kiyi din, sai dai nafi son kiyi a gidan mijinki" ya miko min takardar "ki je ki cike ki bashi, sannan in har yayi kokari ya samo miki admission din to ki karba, amma duk sanda nayi niyyar aurar dake kuma aka ce masa ya fito yaki sannan wanda yazo da gaske zai aure ki yace baya so to zaki ajiye karatun duk da ina so kuma kema kina so amma aure yafiye miki komai".

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now