part 2

151 20 2
                                    


*BA NIDA LAIFI!*

_Top_Notch_

02.     Free page

✍️Ayshatuuu

Ta kusa awa daya tana tafiya, Kuma gudu take akan titi, ban ma fahimci tana gudun ba seda naga uban kilometers din da muka rufa a awa daya, ta samu gefen titi tayi parking tare da hade kanta da steerer wheel tana Kara sakin kuka, na lumshe idanuna Ina jin wani irin Tsoro cikin zuciyata, na dubeta a tsanake nace

"Sister dan Allah ki fada min abinda yake faruwa, me ya faru? Abu ya samu Dadaa ne? Kinki magana se kuka kike Kuma na tambaye ki kinki kice komai, haba mana sister!"

Ta Dan dago ta dubeni sannan ta maida kanta ga window tare da fadin

" Bazan taba son ace daga Baki na Zaki ji ba, Amma Kuma ni daya kike da a duk duniya Dole ni Zan fada Miki!"

Na dubeta cikeda kosawa nace

" Whatever may be duk yadda abin yake Dan Allah ki fada min, ji nake zuciyata kamar zata buga sister"

Ta rike hannuna cikin nata tana kallon fuskta me cikeda rauni da Kuma tashin hankali tace

" Auren ki da Hashir Bai yiwu ba..."

Tamkar saukar aradu Haka naji, tamkar an tsula min bulala Haka naji, nayi shiru dumbfounded, naji komai ya tsaya ko Kara bana ji, tamkar zuciyata ta daina aiki, se Kuma can naji kamar an tsikare ni, nayi saurin kallon sister Dake girgiza ni tana fadin

" A'isha! Talk to me! Ki na jina?"

Na Yi saurin kallon ta Ina kyafta idanu nace

" Menene?"

Se ta Kara kallona ganin na dauke kaina with a blank emotion a fuskata tace

" Nace Miki an fasa auren ki da Hashir, kiyi kuka kinji?"

Na girgiza Kai nace

" Sister! Ina son nayi magana da Dadaa ki maida ni gida'

Ko kafin ta bani amsa se ga Kira ya shigo cikin wayar ta, kusan lokaci daya muka Kai hannun mu saboda idanuna sun gane min Dadaa ne me kiran, sede ta rigani dauka, maimakon tayi swiping ta Kara a kunnen ta kawai se ta katse kiran, nayi shiru Ina kallon ta, na rasa tunanin me zanyi, Bai hakura ba ya sake Kira wannan Karan nayi saurin dauka na Kara kunne na

" Nasiba!"

" Dadaa!"

Na fada a take hawaye ya balle min daga fuskata,

" A'isha! Are you the one? Kuna ina? Kuna tare da Nasiba?"

Na Kara sakin kuka Ina kallon ta, cikin muryar kuka nace

" Dadaa ta tafi Dani, bansan inda muke ba Kuma, Taki ta fada min"

Muryar shi a tausashe kamar ko da yaushe yace

" Kiyi shiru, bawa Nasiba wayar! Lemme talk to her"

Se na Mika Mata Babu musu, Dan bana tunanin a iya rayuwa ta na taba yiwa Dadaa musu,  ni din nasan ko Bai fada ba ni 'yar albarka ce, yaran da ake alfahari dasu. Na cigaba da goge hawayen dake min zarya, Ina jin wani irin tukukin bakin ciki Yana zagaye min ilahirin zuciya ta, bakina daci yake, idanuna har yaji suke saboda ni kadai nasan abinda nake ji. Babu Wanda zai San menene azo daurin aure a fasa, wanne irin tozarci ne wannan? Wanne bakin ciki yafi wannan a duniya.

" Ina Kika kaita? Ina kuka je? Are you in your right senses Nasiba!"

Shi ne abinda ya fara fada Mata tana karbar wayar, tayi saurin bude motar ta fita ta barni zaune tamkar mutum mutumi.

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now