part 12

83 16 2
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

12.       Free page

✍️ Ayshatuuu

Duk yadda ake Mata nasihar ta fawwallawa Allah Taki to bana ce Taki ba, ta tada hankalin ta da komai akan rashin haihuwar da batayi ba, muna karbar result din da Kuma counselling da likitan yayi musu ta Sha kukan ta ta gode Allah, yayi ta lallashin ta Yana nuna Mata kowanne Dan Adam akwai abinda Allah ya tsara Masa, kowa akwai kaddarar shi

" Haba wife, bansan ki da Haka ba, Maryam din Dana sani me tawakalli ce, kukan ya Isa Haka Mana"

Cikin kukan tace

" Haihuwa fa, sun ce bazan haihu ba fa"

Ya safe Kan shi Dan shi Dadaa abu kadan ke saka rikicewa yace

" I know! Su Allah ne da zasu ce ba Zaki haihu ba, ko ban da shekara hamsin idan Allah yayi Zaki haihu Zaki haihu, so ki daina kuka"

Ina hango su Amma bana Jin abinda suke cewa, ganin tana kuka yasa duk naji Babu dadi. Daga airport straight gidan su Dadaa muka wuce, da murna ta wadda ta bawa hatta Dadaa mamaki na Shiga na fada jikin Inna, itama ta rungume ni tana shafa kaina tace

" Yaya A'isha ta Dan girma!"

Ya kalle ni, da gaske na Dan Yi tsawo sannan Naga na Dan ciko kadan.  Yace

" Ai inaga LA Zan maida ita, Inna Ina wuni? Mun same ku lafiya?"

Inna ta amsa cikeda Jin Dadi, Ammi ta gaida ta, ta amsa dukka muka tambayi Baffa Jafaru tace ai shi da Yaya Faisal sun je Gwaram Hajja Muna ce Bata da lafiya! Mukai Mata addua na koma can gefe Ina tsakurar sinasir din da aka zuba min da taushe.

" Inna kinsan mun je saudiyya ganin likita ni da Maryam ko?"

Inna ta gyada kai, idon Ammi kamar zai fado kasa saboda batayi tunanin zai fada ba

" Allah yasa an dace"

Ya Dan yi shiru, Ammi ji take kamar ta tashi ta ruga Dan tsoro, yace

" Sunyi bincike da zasu iya, matsalar daga waje na take, Amma sun ce idan nasha magani zaa iya dacewa"

Ammi tayi saurin kallon shi, ko kusa ko alama ba tayi tunanin abinda zai fada ba kenan, tayi tunanin zai fada yadda abin ya kasance ne. Inna ta dauki salati tana nuna alhinin ta, ta Kara musu nasiha ta cewa Ammi idan taga ba zata iya Zama a Haka ba she's free a raba auren. Tayi saurin girgiza Kai tace har abada ba zata taba yin wannan butulcin ba. Se dare Bayan dawowar su Baffa muka koma gida shima Nasiha yayi musu sosai Akan karbar kaddara sannan kamar hadin Baki yayiwa Ammi tayin rabuwa Dadaa Dan a ganin su wannan shi ne adalci. A Hanya nayi bacci Ammi yace da Dadaa

" Me yasa kayi twisting maganar?"

Ba tare da ya kalle ta ba yace

" Saboda hankalin ki ya kwanta"

Ta Dan kwantar da kanta a kafadar shi hade da riko hannun shi tace

" I love you so much! Thank you so much!!"

Yayi murmushi Yana shafa fuskar ta yace

" You are always welcome wife!"

Bata kuma cewa komai ba dukda a ranta tana  ayyana shekara kusan shida zuwa bakwai Bai taba cewa Yana sonta ba, Amma Bata damu sosae ba saboda Yana kokarin Kare hakkin ta da dukkan abinda ya kamata mace ta samu. Har muka karasa gida, ko Ina a gyare wannan aikin Anty hafsa ne, ita tazo ta gyara Mana ko Ina, idanuna half open half close na Shiga daki da taimakon Dadaa, ko alwala banyi ba nayi bacci, ya saka min net ya gyara min kwanciya sannan Kuma yayi min addua, yayi tucking net din sannan ya juya ya tafi.

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now