part 11

75 21 1
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

11.      Free page

✍️ Ayshatuuu

Cikin hukuncin Allah buwayi gagara misali, rayuwa ta cigaba da tafiya, Ammi ta dawo daidai, Zama na da ita se kowa yayi misali dashi, tun da akai wannan daya ba'a Kuma dukda wani lokacin tana Saba min, Amma ni na kasance mutum ce me uzuri so bama na Bari ya dame ni, musamman da bani da lafiya nafi Tafiyar da rayuwa ta a hankali. Duk wani kokari da Dadaa yake to akai na ne, gidan mu zaiyi wuya ka shiga kaji sauro saboda da zarar na fara zazzabin malaria se crisis, wannan yasa nakan Jima ban samu ba. A bangaren magani duk inda Dadaa yaji labarin magani to Yana iyakar bakin kokarin shi wajen ganin ya siya min. I remembered a wajen aikin su suna Hira yake cewa ai ni SCD ne dani, se wani ya Masa suggesting ana cin Naman kunkuru ko baa warke ba to tana jimawa Bata tashi ba. Ranar kuwa munyi sport a school an canja Mana class na shiga basic five, akace dukka se munyi gudu, ni dai Ina can gefe da sport wears Dina a jiki, class teacher din mu yazo yace na tashi nayi joining, na dube shi nace

" Sir I cannot run!"

Ai se ya fara fada

"A'isha you must run, if you didn't I'm going to deal with you"

Dama mutumin ya takura min, tunda ya fahimci bana son magana to duk wani Abu da zaayi na magana se ya saka ni, ko Kuma indai abin wahala ne to dama se yasan yadda yayi ya saka ni, ni Kuma ban Saba ba, gaba data kana kallona kasan cewar ni nafi karfin a Kira ni da ajebo ma, ni Yar Madara ce, wahala kadan zanyi se ciwo ciwo, shiyasa nake mugun lallaba kaina. Na mike a hankali har lokacin Yana tsaye a kaina, dama tun dare Ina jin ciwon kafa, Kuma na lura kamar jini na yayi kasa, ban fadawa Dadaa ba saboda bana son hankalin shi ya tashi. A hankali na gyara shoe lace dina, na tako a hankali zuwa track din, Jidda dake can gefe wadda tayi 50m ta dawo tana kwankwadar ruwa daga cikin water bottle, tana hango ni na tsugunna tayi saurin karasowa tana fadin

" A'isha ba dai gudu zakiyi ba?"

Na Dan kalle ta tare da gyada Mata kai, kafin ta karaso yayi blowing whitsle aikuwa na daddage na kwasa a guje, abin mamaki ni ce akan gaba Muna karasawa naji kamar an harde kafafuna Babu shiri na Fadi a kasa, ga Rana ta kwalle track din yayi zafi, na Dan saki Kara a hankali saboda azabar da naji, gaba daya har shi ma suka yiwo kaina a guje, kowa ya fara kokarin daga ni, duk na kurje a gwiwar hannuna da Kuma gwiwa ta da tafin hannuna, da kyar na iya tsayawa kowa se sorry yake ce min, kafata kamar zata karye Haka nake ji. Na zauna aka kawo min ruwa na Sha kadan Ina ta yatsina fuska Wanda ya tabbatar musu ciwo nake ji, daga nan muka tafi sick Bay duk hankalin Uncle a tashe, kafin mu karasa se habo, na taba Naga jini Yana disowa daga hanci na, ya rabbul alamin na ayyana a Raina. Muna zuwa sick Bay tasa na daga kaina Bata ma damu da tambayar abinda ya faru ba, tasa min kankara saman goshi na sannan yayi packing hancina da cotton, bayan ta zauna ta dubi teacher din mu tana fadin

" Me ya faru da ita? Dazun na ganta fa Naga she looks pale, nace idan an tashi tazo, what happened"

Uncle ya zauna ya fada Mata abinda ya faru, ta fara ihu tana fada

" How could you tell her to run, you should know she's a sickle cell patient"

Shi dai Bai ce komai ba, ya rasa meye yake Masa Dadi, na kalla nurse din nace Mata jikina ciwo yake, tayi saurin ballo magani ta bani na Sha Amma a banza jinin Bai daina zuba ba, Dole aka fadawa headmistress din mu, se gata kuwa tazo da Anty charity, Anty din mu ta kindergarten, ita ta Kira Dadaa a waya, yace su taho Dani asibiti shi ma zai same su acan, Muna zuwa a school bus da kyar aka samu jinin ya tsaya, nayi wani irin dashewa ga ciwo da nake ji, hankalin Dadaa yayi balain tashi, dama idan crisis yazo Ina kuka to ciwon Bai Kai ya kawo ba, Dadaa yasan wannan Amma da zarar nayi clutching bedspread ko rigar shi, ko na kankame hannun shi Ina numfarfashi to yasan tabbas ciwon bazan iya jurewa ba, yau din ma hakan nayi, na damke hannun shi cikin nawa Ina numfashi daddaya, idanuna kamar zasu fito waje, Dadaa ya shafa kaina yace

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now