part 15

278 28 4
                                    

*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

15.        Last Free Page

✍️Ayshatuuu

Tana zaune ya same ta a daki, a bakin gado tana only God knows what, ya ja stool din gaban vanity table ya zauna, cikin tattausan murya Dan Bai kasance me hayaniya ba yace

" Maryam me yake faruwa tsakanin ki da A'isha? Do you have problem whatsoever da ita? Ko kin gaji da rikon ta ne ki fada min?"

Ta dago ta kalle shi, kamar yadda yake kallon ta Haka itama take kallon shi, duk kokarin fahimtar yanayin ta abin ya faskara,

" Baka ganin abinda take min?"

Da mamaki ya maimaita abinda tace kafin Kuma yace

" Ok naji! Maryam fada min asalin abinda A'isha tayi Miki"

Kawai se ta daga murya

" Titsiye zakai min? Saboda ni ban haihu ba..."

Shima ya daga muryar shi idanun shi har sun Yi jawur yace

" Don't dare! Kice Dan ba Kya haihuwa me nayi Miki da zai Yi justifying Haka? Haba Maryam you're being too selfish, A'isha marainiya ce ba se na Kara fada Miki ba kin sani, Babu iyayen da zasu so barin yayan su a duniya. Why are you like this? Idan Abu ne ya faru ki fada min ni Zan gyara abin, idan Kuma kinsan kin gaji da rikon ta ki fada min, I promise you a way out Amma ba Zan dauki abinda kike Mata ba..."

Kalaman da yasa ta fara kuka sosae, ran shi a mugun bace Amma Kuma kukan ta baya ma kunnuwan shi dadin saurare, hakan yasa ya janyo ta jikin shi ya fara rarrashin da baiyi niyya ba, seda tayi shiru tace

" Adda Nana ce tace Wai zaka iya auren ta"

" Auren wa?"

Tace

" A'isha!"

Babu shiri ya saki Ammi yace

" Ke Kuma se kika yadda? Kin taba ganin uba ya auri Yar shi? A Ina Kika taba gani? Haba Maryam Ina hankalin ki ya tafi?"

Da Haka dai sukai resolving abin, lokacin da ya fito na Jima a daki, seda yaje kitchen ya tarar na maida abincin kitchen na rufe, ya Kira sakina yace ta turo ni Dan ya dade da daina shigowa daki na se de idan akwai kwakwaran dalili mostly idan bani da lafiya, hijab na saka na fito na same shi a zaune, tundaga fitowa ta yake kallo na har na karaso na  zauna inda yake zaune, fuskata ta Dan tashi saboda kukan da nayi, ya nuna min gefen shi na zauna ya fara tambaya ta abinda yasa nake kuka har haka? Nace Masa Babu kawai dai bana Jin Dadi ne. Yayi min kalami masu Dadi da Suka saka Na dan Ware har nayi murmushi, yace na dakko abinci naci Babu musu saboda tsakani na da Dadaa bana tunanin na taba musu Kuma dai, Haka nan naci sannan Kuma na mike Zan tafi se Kuma na dawo nace

" Dadaa kaji ko?"

Yace

"Menene?"

Na danyi shiru Ina tunanin tune din da zanyi amfani da shi wajen Masa magana Dan ya yadda da kuduri na, ya Kara tambaya ta yace

" Fada min ko menene?"

Nace

" Dama Dadaa sister ce tace zata je Lagos, Ina son nabi ta"

Yayi murmushi yace

" Kin gaji da Zama damu ne?"

Nayi saurin girgiza Kai na nace

" Not at all Dadaa, waye yake gajiya da gidan su?"

Yayi murmushi impressively yace

" It's ok! Yaushe Nasiba zata tafi?"

Nace

" Jibi"

Yayi Mana addua yace zai Kira ta taje tayi Mana booking flight, dakin Ammi na wuce na same ta ta fito daga toilet daure da bath robe, ta kalleni se ta maida Kan ta zuwa daukar karamin towel, ban zauna ba nace

" Ammi kiyi hakuri! Dan Allah kiyi hakuri kinji?"

Ta Jima tana kallona tana mamakin dalilin hakurin da nake bata dukda ta san ban yi laifi ba amma Kuma hakanan dai nake Bata hakuri, tace

" It's ok, kije kici abinci ki Sha magani ki kwanta"

Nace

" Tohm, zanje Lagos jibi"

Tace

" Gurin su Hajiya?"

Na gyada Kai tace to Allah ya kaimu na amsa Amin sannan na fito na koma daki na. Ina kwanciya Dadaa ya Kira sister ta tabbatar Masa Tafiyar ta jibi, yace ta turo account details din ta zai tura Mata kudin flight din mu. Cikeda murna Dan ban taba zuwa Lagos ba Kuma tana son nasan cewa Dadaa ba mahaifi na bane ba. Hakan ce kuwan ta kasance Dan kuwa washegari Bayan mun Yi breakfast na dakko wani novel fugitive in love Ina karantawa Dadaa yayi calling attention dina, yace

" A'isha na Baki labari?"

Na gyada Kai na Ina rufe littafin bayan nayi marking inda na tsaya na bashi dukkan wani attention dina. Yayi murmushi ya fara bani labarin iyaye na, Yana Yi Ina sauraron shi yayinda Ammi ke gefe tana Jin labarin da itama Bata taba ji ba, labarin soyayyar Abba da Kuma Mamana, se daya kawo har zuwa rasuwar su yace

"The died and left behind beautiful souls"

Dukkan labarin ban masan yadda yake related to ni ba, hakan yasa nace

" Su waye Dadaa? Labarin abin tausayi"

Bai ce min komai ba ya mike zuwa dakin shi, na dubi Ammi da tun safe Bata son hada idanu Dani nace

" Ammi whose story is this?"

Tace

" Ban sani ba A'isha, wannan shi ne karon farko da nake ji. Wait for him"

Aikuwa se gashi ya fito rike da wani album, ya Miko min Babu musu hannuna na rawa na amsa Sega pictures wasu black and white ne ma tsabar suna Dade, anan Naga wannan hoton sak Dana gani a dakin sister Amma wannan Kuma har da wani Mai yanayi da Dadaa Amma kammanin sa kamar Faisal din Baffa Jafaru, na dago Ina kallon Dadaa Dan yayi min Karin bayani akan pictures din, na kalle shi questioningly nace

" Dadaa parent din sister ne?"

Ya gyada Kan shi tare da Kara fadin

" Har dake, the woman in the picture is your mother and man is your father?"
Maimakon yaga mamaki ko wani reaction kawai se yaga na fara dariya nace

" Kai Dadaa!"

Se ya dawo gefe na yace

" A'isha bani na haife ki ba, ke Yar Uncle Ismail ce da Anty A'isha, ke sister Nasiba ce"

Ban Kara karya ta shi ba saboda nasan ba Wasa yakeba Amma Kuma na kadu yadda me karatu Bai tunani, na Kuma Yi mamakin hakan, na juya na dubi Ammi Dake kallo na come da tausayawa nace

" Ammi kice Dadaa Wasa yake, ni ku kadai ne iyaye na"

Ta matso kusa dani ta rungume ni tace

" Wannan haifar ki kawai suke, Amma kada ki manta Dadaan ki zai zame Miki uba har izuwa karshe kinji?"

Nayi kuka sosae ranar, na koma daki rike da album din Ina bin pictures din Ina musu addua kamar yadda Dadaa yace min nayi Haka nayi tayi. Bayan kwana daya muka tafi Lagos har lokacin ban ware ba Ina ayyana yadda akai Dadaa yake matsayin cousin ba Wanda ya haufe ni ba, Dana fadawa sister se tace da gaske ne, ta nuna min Dadaa ba karamin zumunci yayi ba da ya iya rike ni, Kuma haza ta canja zani ba Dadaa is a father saboda ni shi ne uban Dana sani ba wani ba Kuma!

BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258 or 0813 026 9641 or +234 813 731 1900.

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now