part 6

103 19 1
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

06.    Free page

✍️Ayshatuuu

Dukka wannan ban sani ba, a cikin rayuwa ta Dadaa kawai na sani, kamar yadda Mamana ta bukata, Dadaa shi ne uwata, ubana, aboki na, shi ne komai nawa na duniya, ko minti talatin mutum yayi tare dani zai fahimci who Dadaa is, da yadda na bashi matsayin na gaske a rayuwa ta. Babu wani mutum a duniya da matsayin shi ya wuce na Dadaa a gurina, Babu shi, kowa Bayan Allah da annabin sa to Bayan Dadaa yake gurina, he's all I have!

Watanni shida nayi Ina karbar zallar Madara kafin akai min introducing solid foods, ranar da na cika wata shida da wuri ya dawo daga gurin aiki seda ya tsaya ya siyo min dukkan wasu processed food da yaro zai iya ci kafin ya karaso gida. Anyi min wanka an shirya ni cikin brown din Kaya masu bakin stripes a jiki, kaina an tsaga gida hudu an daure kowanne da band, Yana sallama na fara waige waigen ganin daga Ina naji muryar shi, ya karaso ya karbe ni hannun Yaya hafsa Yana murmushi yace

" Thank you hafsa"

Tayi murmushi, ya tambaey ta inda Inna take, ta sanar Masa Inna na daki, ya aje kayan hannun shi ya wuce ciki har lokacin Ina hannun shi, Dan tunda ya dawo ba lallai na Kara yadda wani ya dauke ni ba kuma, Haka yace min wai indai baya nan zaa zauna lafiya Dani Amma da zarar naji muryar shi an gama magana. Da sallama ya shiga dakin, tana zaune tana jera gwangwanayen da aka shigo dasu, ya tsugunna ya gaishe ta cikin girmamawa sannan ya zauna tana tambayar shi aiki, ya amsa Mata da alhamdulillah, yace

" Ta karba abincin kuwa da aka bata?"

Inna ta dube ni tana fadin

" Sosae kuwa! Ai naji Dadi"

Ya gyada Kai tare da mikewa Yana Kara Mata godiya zai fita, ta Dan Kira shi hakan yasa ya dakata da fotar ya dawo ya zauna, bayan ya zauna tace

" Babana!"

" Naam Inna, akwai wani abunne?"

Ta gyada Kai tace

"A'isha na bukatar uwa, ya kamata kayi wani abun idan tayi wayo zata gane ko wacece a tare da ita ba ita ta haife ta ba"

Ya Dan gyara zaman shi yace

" Inata kokari Inna, kinsan Ina neman wata yarinya acan potiskum ko? To gaskiya Dana Mata maganar A'isha ta nuna ita ba zata rike kowa ba, se nace Mata to mu hakura kawai, bazan iya Zama da Wanda ba zai rike A'isha ba"

Inna ta nuna rashin Jin dadin ta akan abin amma Kuma tayi commending dinsa akan hakan me kyau ne duk wadda zata zauna dashi se ta yadda zata rike ni. A hankali na cigaba da rayuwa ta na tare da na San me ma yake faruwa a rayuwar ba, all what I know Babana Dadaa ne, Kuma na samu uban nunawa a duniya. A hankali shekara ta wuce wata tazo ta Kara wucewa har lokacin Dadaa na baiyi aure ba, kowa Kuma se ya fara Masa korafin hakan musamman na shigo shekara ta uku har an fara kokarin kaini makaranta, dangin Mama na kokari da gaske wajen zuwa gani na da Kuma yimin hidima, sister ce akace min bamu hadu da ita ba seda na kusa shekara biyar.

Ranar da aka fara kaini makaranta, Dadaa Bai je aiki ba excuse ya dauka, Yaya hafsa ta yimin wanka aka dakko sababbin Kaya na uniform aka saka min, lunch box Dina an saka min sandwich, an saka min tea cikin karamin flask se ruwa da lemu. Yaya hafsa ta raba min kaina biyu ta tufke shi da band sannan aka shafa min bon bon malazia a jikina, Ina Jin muryar Dadaa na bar socks din da ake saka min na nufe shi da gudu, Amma gudun ma a hankali nake, gaba daya ni idan aka kalleni I'm a very weak person ko kadan bani da karfi, Yar karama ce ni rashin lafiyar Mamana lokacin da tana da ciki ta shafe ni sosae. I'm very fragile kamar da ka taba ni Zan karye Haka nake, shiyasa mutane ke tausayi na, saboda yadda halitta ta ke Haka yasa nake Kuma shiga ran mutane

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now