part 13

76 17 2
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

13.             Free page

✍️Ayshatuuu

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, aka kawo Naman kunkuru Ammi ta dafa min, ban masan Naman meye ba naci saboda an saka Masa yaji Kuma ni dama naturally Ina son ayi peppering abu, na daddage naci da rana, daddare aka bani nace

" Na koshi"

Se Suka barni aka seda na jera sati Ina ci a lokuta daban daban. Magunguna sosae aka dage min dasu and before you know it se alhamdulillah jiki na yayi sauki, na kusan shekara Babu crisis din sede Dan ciwo kadan kadan. Wannan yasa Dadaa cikin farin ciki madaukaki. Bayan na Gama primary direct Suka bani admission zuwa secondary school din su Dake nan ring road. Amma kafin na fara se aka Mana hutu me Dan tsawo, Dadaa ya same ni a daki sakina na daura min net ni Kuma Ina zaune gaban study desk dina Ina tilawa, shigowar Dadaa yasa na mike na fara fadin

" Dadaa!"

Yace

" A'isha, sit"

Na zauna shi ma ya zauna opposite dina ya karba Qur'an din yace na karanta, na fara karantawa Babu Bata lokaci, seda na kammalla tas sannan ya dubeni looking impressed yace

" Barakhallahu fikh!"

Nayi murmushi sannan yace

" Zaki je London wajen Nasiba?"

Nayi exclaiming a hankali nace

" Ohhhh Dadaa sister Wai?"

Ya gyada Kai yace

" Eh ita"

Na gyada Kai na, Amma Kuma se na Bata Rai nace

" Dadaa Kai Kuma fa?"

Yace

" Zan raka ki, nayi kwana biyu Se na dawo"

Da da farko naki yadda se daga baya na yadda, saboda Ina ganin yadda Zan tafi wata yes duniya na rayu babu Dadaa,  Bai takura min ba, Amma kullum se yace Wai ni Yar kauye ce bana son Naga turawa, bana son naga kasar waje, daga karshe dai na amince zanje cikin kankanin lokaci aka nema min visa da komai muka wuce London wajen sister, wannan ne Karo na farko da na Kai Mata ziyara sannan Karo na biyu da muka hadu da ita. Bama cikin London suke ba a Lancaster suke, jirgin mu da daddare ya sauka a airport, gaba daya a gajiye nake, idanuna sun fara canja kala, dama tun a jirgin se bubbuga kafa ta nake Wanda ya ankarar da Dadaa, Babu shiri ya ballo min magani na sha, shi ne na danji sauki, saukin abun munyi trans in a turkey har na awa goma Sha biyu na huta sosae kafin mu Kara boarding jirgin zuwa nan. Muna sauka muka bi dukkan wasu protocols, bansan har se yaushe darajar Dan Nigeria zata girma a idanun sauran kasashe ba, mune zuciyar Africa Amma halayen mu sun sa mun Zama koma baya, yadda akai daidai da kayana komai se da aka zazzage kafin Kuma na shiga wani secluded daki aka caje ni tas Haka shima Dadaa, duk na firgita Amma Dadaa yayi min bayanin akwai Wanda suke safarar hard drugs zuwa kasar shiyasa ake hakan. Muna fitowa daga cikin arrivals ba zaka taba tunanin biyun dare bane, zakai tunanin tsakiyar Rana ce. Na dinga wurga idanu Ina kankame jikina saboda wani irin sanyi da nake ji, Dadaa ya tsaya ya cire rigar shi suit ya saka min a jiki na, ya janyo ni jikin shi muka tafi, se can muka same su a tsaye, Sister na fara hangowa ta rugo da gudu Dadaa yace

" Ga Sister din ki"

Bana son ko kadan na matsa daga jikin shi saboda sanyin ji nake kamar bazan iya bearing ba, kafin nayi yunkurin tarar ta har ta karaso, I wonder yadda ta ganemu a wannan Daren, ta fado jikina, Dole na fito da hannuna na rungume ta, dukda ta girme ni sosae Amma see na ganni wata Yar karama a gabanta, ta girma tayi tsawo ta Zama cikakiyyar budurwa, ta sake ni sannan ta Kama hannuna fuskar ta dauke da murmushi ta gaida Dadaa, Yana murmushi me hade da gajiya ya amsa, Uncle Auwal ya karaso, na gaishe shi ya amsa Yana fadin

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now