part 10

76 18 1
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

10. Free page

✍️Ayshatuuu

Babu jimawa muka koma gida, ranar a dakina Dadaa ya kwana, lokacin da na Gama dinner Wanda noodles nace Ammi ta dafa min da baked beans hade da sweet corn a ciki se scrambled eggs. Ina gamawa na dakko school bag dita, Ammi na tsaye taga na zauna na Ciro books din, ta dawo kusa dani tace

" Homework zakiyi?"

Na danyi murmushi nace

" Eh Ammi"

Tana zaune Ina Yi a hankali tana kallona har na kammalla, lokacin Dadaa ya fito da system a hannun shi, na kammalla zura books din cikin jaka, seda na aje na matsa gefen shi na zauna, ya matsar da system din ya janyo ni jikin shi Yana fadin

" Babyn Dadaa, ya akai?"

Na dubi Ammi da dukkan hankalin ta yake Kan kallon wani tsohon Indian movie na Amitabh batchan maard, nace

" I want to sleep!"

Ya mike Yana dauke dani muka nufi dakina Ammi ta bimu da kallo har Muka shiga, Yana zaune na canja Kaya zuwa na bacci, duk wannan abubuwan na iya, har na hayo Zan kwanta yace

" Bakiyi alwala ba"

Nayi saurin rufe bakina na sauka daga gadon na shiga toilet nayi alwala na dawo na kwanta ya dauki wani katon story book na Prophets, tun daga Kan annabi Adam ya fara min yanzun Muna labarin annabi Ibrahim dashi, Yana min Ina Masa tambaya se bacci ya dauke ni, ya Jima Yana karantawa kafin yaji numfashina a hannun shi, ya rufe littafin a hankali tare da kokarin kwantar Dani daidai se yaga hannuna na rike da rigar shi, yayi murmushi tare da shafan Kai nayi juyi na rike hannun shi, se ya fara min addua Yana tofa min, a Haka shima bacci ya dauke shi. Ammi ta Jima a parlon har aka gama movie din shiru Dadaa Bai fito ba, ta mike ta karakshe komai ta nufo dakin, cak ta tsaya tana kallon yadda muke bacci peacefully, se kawai ta rage Mana fanka ta kashe wutar dakin ta juya zuwa dakin su, tayi addua ta kwanta Amma se ta gagara bacci, tai ta juyi tunani iri iri na zuwa Mata, wani lokacin tana Jin gajiyawa dukda tasan Dadaa na balain kokari akan ta, Yana Bata dukkan abinda ya dace har ma beyond yadda take expecting, takan tuna ya aure ta Bata son ta, ita ya taimaka ya aura tunda ita ke son shi, Amma yadda yake min wani lokacin abin Yana taba ta. A hankali taji saukar hawaye a fuskar ta, tayi saurin gogewa amma se kuka ya turnike ta, tayi ta kuka a hankali kafin bacci yayi gaba da ita!

Washegari Dadaa ya farka, hannun shi a Kage saboda matashin Kai da nayi da hannun, ya Dan daga Kai na, yayi addua sannan ya lulluba min karamin duvet dina ya Kara min addua, ya shiga toilet Dina yayi alwala ya fito Yana mamakin yadda akai yayi bacci tare dani, yanzun Bai fiye son kwana Dani ba saboda na fara girma, na Kai shekaru takwas, ya nufi dakin su shi da Ammi ya samu har lokacin bacci take, ta takure acan gefe daya, ya karasa ya Dan bubbuga Mata gefen katifa yace

" Maryam! Asuba tayi"

Dake Bata da nauyin bacci se ta farka, ta tashi ta zauna ganin Haka Bai ce komai ba ya fita zuwa masallaci, kafin ya dawo har ta shiga kitchen, Yana dawowa seda ya fara tashi na sannan ya same ta a kitchen, tana gaban gas tana soya Irish, ya Dan rungume ta kadan hakan yasa ya juyo fuskar ta Babu wani yabo Babu fallasa tace

" Dadaan A'isha Ina kwana?"

Yace

" I'm fine wife, jiya Baki tashe ni ba, kikai bacci ke kadai"

Tayi shiru, ya fara Bata traces na kisses Wanda yake neman karya lagon ta tace

" A gaban mai nake fa"

Yayi saurin sakin ta yace

" Sorry! I missed you Baki ji gadon ya Maki girma ba? Baki tashe ni ba"

Cikin kulewa tace

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now