part 5

110 21 2
                                    

*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

05. Free page

✍️Ayshatuuu


A hankali Kuma se ya fahimci kunyar shi take ji, Kuma gashi ya saba da yadda take on and off akan shi, da gaske ya fahimci komai da take Amma Bai San commiting kanshi a kanta ko ya bata false hope. Amma yanzun Yana zaune se yaji kewar ta yake, ya mike daidai shigowar uncle Auwal yace

" Wai ni Kam Ina A'isha ne? Kwana biyu bana ganin ta"

Ya yadda takaddun hannun shi da ya shigo dasu, tare da Zama gefen katifa yace

" Tana can karatu take, ta fara exams!"

Babana yace

" Da gaske? Wait wai me take karantawa ne?"

" Pharmacy ne, shit irin naka course dinne"

Se yayi murmushi yace

" Allah ya bada saa"

Ya amsa da Amin, da yamma ta fito ta shimfida abin sallah ta hada littatafai a gaban ta tana ta karatu kamar yadda ta saba, ya Jima Yana kallon ta daga daki kafin Kuma ya fito ya nufo inda take, turaren shi yasa ta Dan tsaya kamar me tunani se Kuma taji footsteps din sa, ta Dan waigo se karaf idanun su Suka hade, tayi saurin dauke Kai tana tunanin ta tashi ta koma ciki Amma Kuma ai tana son ganin shi itama, kafin ta gama tsara yadda zatayi se taga ya zauna kujera tare da daukar daya daga cikin books din gaban ta yace

" Ban taba sanin abinda kike karanta ba kenan"

Ta dube shi tace

" Kaima pharmacy kayi?"

Ya gyada Kai Yana ce Mata wanne course zasuyi gobe, ba tare da ta dube shi ba ta fada Masa, kokari take sosae wajen ganin tayi controlling bugun zuciyar ta, waye yace Mata heartbeat voluntary activity ne? Ita kanta zuciya nada intrinsic factors dake sata bugawa ita daya. A hankali ya fara Mata tambayoyin tana bashi amsa, se ya koma Yana tambayar ta inda Bata gane ba, Suka zauna har aka Kira sallar maghrib kafin ya wuce masallaci ita Kuma ta tattare gurin tayi ciki, alwala tayi ta dawo daki ta kalla madubi, a take murmushi ya kubce Mata Wanda tayi yafi a irga! Kamar Wasa kullum se sunyi karatu, wannan karatun da suke ba karamin faranta musu zukatan su yake ba, kafin wani lokacin sun fara shakuwa  ta ban mamaki, kowa a gidan kallon su kawai yake, idan suna Abu ko baa fada maka ba kasan ba karamin son juna suke ba, Amma sun kasa furtawa . A Haka kwanaki Suka shude har ta bar ajin da take ta koma level 3 shi Kuma a lokacin ya kammalla service dinsa da yake Yi a wani babban pharmaceutical company cikin Lagos din. Ranar da yayi POP washegari da zai tafi kowa yayi tunanin aljanu ne da ita yadda ta dinga kuka kamar ranta zai fita, shi Kan shi baiyi kuka ba Amma ji yake kamar numfashin shi zaa yanke Masa. Tafiyar shi tasa ta koma kamar wata marar lafiya, Hajiya tun tana lallashin ta had ta fara Mata masifa

" To ki hada kayan ki ki koma can Gwaram din Mana, ni Naga jaraba tukunna meye tsakanin ku dashi da har kike neman zaucewa akan shi"

Tana kuka akan gado tace

" Hajiya son shi nake"

Hajiya ta dafe kirjin ta, idanu a waje, a wañnan lokacin mace tace tana son namiji ai babban abu ne, Hajiya ta Gama sallallami kafin Kuma ta zauna tace

" Kina da hankali kuwa? Kinsan me kike fada?"

Mamana ta share hawayen ta tace

" Ni dai na fada Miki Allah son shi nake, ji nake kamar kaina zai tabu"

Wasa Wasa karamar magana se ta Zama babba tun kakana Bai San abinda ke faruwa ba har Hajiya ta fada masa, to shima Abba na abinda ke faruwa dashi kenan, bansan waye yace musu shakuwa, soyayya abun Wasa bace. Shima ya sauke abinda yake ji ya samu mahaifin shi ya fada Masa. To cut the long story short, Mama ta auri Abba. Ya samu aiki anan pharmaceutical company da yayi service dasu, su sukai retaining din shi. Dan Haka cikin aminci ya koma Lagos ya zauna da Mamana. Tana karatun ta Yana aikin shi, bana tunanin se na fada muku yadda suke kaunar junan su, fada ma batawa. Shekara biyu tayi kafin ta Haifa sister, sunan ta Nasiba Bayan haihuwar ta da shekara bakwai sannan aka samu ciki na, tunda Mama ta samu ciki take rashin lafiya, so far rashin lafiyar da tayi ajalin ta kenan. Hakan yasa Hajiya ta dauki sister daga gidan ta take zuwa makaranta komai da komai, ita Kuma Mamana tana gida tana fama. A hankali tana turawa takai wata biyar, Abba aka tura shi wani aiki ikeja zaiyi kwanaki hudu, tunda Mama taji zancen Tafiyar take kuka, dukda bawai shi ne karon farko da yayi tafiya ba a shekara kusan bakwai da sukai aure, dukka hankalin shi ya tashi, kamar Kar yaje Amma Hajiya ta nuna mishi jinyar da take ne, ba wani Abu. A Haka ya tafi suna communicating, ranar da zai dawo taji karfin jikin ta sosae Dan har girki tayi da kanta, ta shirya tayi kyau dukda rama da Kuma rashin kuzari. Sede suna tafiya mota ta lalace cikin daji, tamkar wani setup Sega bandits daga only God knows where Suka kashe su. Shiru shiru Babu Abba Babu labari har washegari nan hankalin Mama da kowa ma ya tashi, pharmaceutical company din kanshi kokarin ganin sun samo masaniya akan hakan suke se a kwana na biyu zuwa uku sannan aka tsinci gawar wasu daga ciki a can cikin dajin, Haka aka zo aka fadawa kowa wannan mummunan bakin labari, ance daga nan Mamana ta daina magana, kullum kuka take, Babu mhmmm Babu uhm uhmm! Har aka fara tunanin ko shafan aljanu ne, da Baban Abba yaji hakan Suka tafi da ita rukiya kala kala Amma shiru, se da Baffa Muhammadu ya ganta sannan yace ba aljanu bane Post traumatic stress disorder, wadda muka fi kira da PTSD. A hankali ya hada Mata session da psychotherapist shi ne ma ta fara kokarin yin magana. A hankali cikin ya dinga girma har ya Isa haihuwa, daf da zata haihu Uncle Auwal ya samu aiki a embassy na Nigeria Dake UK, da zai tafi da matar shi Ummaah se ya dauki sister ya tafi da ita.

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now