part 7

69 17 6
                                    

*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

07.   Free page

✍️Ayshatuuu

Rabo wani Abu ne me karfin gaske, na yadda da idan Abu rabon ka ne, I guess duk inda kake to tabbas zaije ya same ka, idan ya wuce ka dama tun can ba naka bane. Na yadda duk inda mijin ka yake to tabbas zai zo ya same ka ko da a wata kasa kake, ko shi yazo ko kaje ko ku hadu a hanya wannan shi ne magana, so I don't believe ayiwa mace gorin aure, saboda komai timing ne.

Kafin mu karasa seda muka tsaya wani store Dadaa ya siya min gift anan reception akai Mana wrapping sannan muka dauki hanya zuwa gidan su Jidda, Muna tafe Yana ce min wai zanci cake din birthday? Na Dan kalleshi na girgiza Kai, tun can Ina yarinya bana son zaki, yace min

"To idan na dakko ki Zan siya Miki chicken, grilled ko roasted?"

Na Kara kallon shi with a bright smile nace

" Grilled!"

Ya shafa kaina, daidai lokacin muka tsaya gaba gidan su Jidda, Yara na ta shiga, wasu duk Yan class dinmu ne se Kuma kadan da ban sani ba Wanda nake ganin relative din su ne, da Kan shi ya sauke ni Yana tunanin yadda zaayi a Shiga Dani, dama ya sani ya taho da ko Anty Bilkisu ko Anty hafsa Amma se ya taho shi kadai, Yana tsaye Yana kallon wristwatch din shi, ni Kuma Ina Wasa da hannunshi se Muka ga an bude kofar gate din, ya dago idanu yana kallon wadda ta fito, she looks beautiful, tana sanye da atamfa me bakin background da Kuma jajayen flowers, ta kalla Dadaa se Kuma ta Yi kokarin wucewa Dadaa yayi saurin tsayar da ita, ta tsaya Suka gaisa yace Mata

" Please Zaki koma ciki?"

Ta dube ni bayan na gaishe ta ban Kara yin komai ba se hannuna Dake cikin na Dadaa, tayi murmushi tace

" Eh Zan koma ciki, wani abun ne?"

Yayi murmushi shima yace

" Dan Allah, here is my daughter A'isha, Zaki kaita wajen su Jidda"

Ta Miko min hannun ta tana murmushi tare da fadin

" Why not! A'isha zo muje"

Na dubi Dadaa ya gyada min Kan shi alamar na bita, nabi bayan ta tana rike da wrapped gifts din, na Dan juyo na kalleshi, ya sakar min murmushi tare da min waving hannun shi, shima hakan yayi min, rayuwa is funny gaskiya, waye zai kawo wani abun zai faru nan gaba, to Amma Babu Wanda yasan gaibu se Allah azzawajal!! Muna shiga naji duk na takura saboda ban Saba shiga cikin mutane ba, da kanta tasa min cap sannan ta matsar Dani wajen Jidda da Junaid, dukkan su sunyi murnar ganina, har Anty din mu, aka yanka cake ko da na matsa se ta dawo Dani, seda aka Gama naje can gefe na zauna se gashi tazo tace nazo Dadaa na yazo, nayi saurin mikewa na bita, hannun ta rike da leda me kayan sourveniers din, Yana cikin mota ta bude ta saka ni a ciki sannan ta aje min kayan da ta taho dashi, Dadaa yayi Mata godiya ta koma ciki tana Jin Dadi. Na gaishe da Dadaa ya Miko min foiled paper me grilled chicken din, Yana Kuma tambaya ta yadda birthday din ya kasance, na zauna Ina cin kaza Ina Masa Hira har muka karasa gida. Muna zuwa gidan da alamar anyi baki, na nanike jikina a gurin shi, se kawai ya tsugunna ya dauke ni sannan muka shiga ciki, a parlor na tarar da Inna zaune da Kuma su Anty Bilkisu se Kuma bakin fuskoki su hudu, na kalla Dadaa dake ta murmushi ya zauna suka gaisa, dattijuwar tana ta kallona tace

" Zo nan shatu!"

Na kalla dadaa, Yana murmushi Yana kallona da yimin alamar naje, na sauka daga jikin shi na nufi hajiyan Lagos, ta bude hannun ta tana fadin

" Mashaaa Allah! Ismail Haka A'isha ta girma"

Inna Dake murmushi tace

" Mu bamu ganin girman ta ma wallahi!"

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now