part 14

96 21 1
                                    

*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

14.  Free page

✍️Ayshatuuu

Cif wata daya nayi sannan Dadaa yazo tafiya dani, a wañnan zuwan Suka taho shi da Ammi, se dare suka karaso dama yace kada a fada min zai zo Amma da gaske na kosa tunda nayi sati uku shikenan na fara Jin gajiyawa, na daina yawan magana kullum mukai waya da shi se nayi kuka nace Masa

" Ni Dadaa kazo mu tafi"

Ranar dai yace min

" A'isha ke da Zan kaiki boarding..."

Kafin ya karasa na bare Baki na fara kuka,me zaiyi Banda dariya yace

" To is ok Wasa nake Miki, Zan zo kinji?"

Nace Ina sassauta kukan

" Yaushe?"

" Soon!"

Shi ne amsar shi, daga wannan ranar na fara irgawa kullum kunne na a bude yake hoping naji daga gare shi Amma shiru kake ji Wai malam yaci shirwa, se da safe na tashi nayi wanka na Sha magani na shirya cikin skirt peach da Kuma milk din long sleeve top, na daura bakin dankwali sannan na fito, nasan sister ta wuce makaranta har su Imsal ma. Haka ma Uncle Auwal ba lallai Yana gida ba, I'm sure ya tafi office sede Mamaa ce kilan kawai a gidan, Ina fitowa idanuna na sauka cikin na Ammi wadda ke rike da mug alamar breakfast take, a take wani farin ciki ya cika ni, na kwasa a guje nayi kanta, Midway naji dariyar Dadaa, ai kuwa na juya na nufe shi na fada Kan shi, sukai ta yimin dariya ya matsar dani daga jikin shi yace

" A'isha kin girma fa, Baki San nauyi ne dake yanzun ba?"

Nayi pouting lips di na nace

" Dadaa oyoyo! Ammi good morning!"

Tana dariya ta amsa, Mama tace naje na dakko breakfast dina, bana so na matsa ma daga gurin balle na dawo na tarar Basu nan, Amma Haka dai nayi sauri na dakko plantain da tea se soyayyan kwai, suna zaune hanaklin Ammi Naga Babyn Mama Dake rarrafe yayin da hankalin Dadaa ke kaina, na Gama cin abincin taa sannan na fara musu Hira a hankali, daga baya Muka fita kafin sauran su dawo.

A hankali bayan mun koma rayuwa ta Kara afuwa, jikina yayi sauki sosae bana samun crisis me firgitar wa nan, idan ma yazo da zarar Dadaa ya Kira Dr Ismail se yazo gida ya ganni shi ne mafarin da yake zuwa gidan mu. Da farko Ammi ta cewa Dadaa ya canja min school daga NTIC zuwa saint Louis, se ya nuna Mata yafi son NTIC din ai kuwa na cigaba na shiga js1, lokaci lokaci na Kan Yi zazzabi Amma da zarar an min intervention se ya tsaya a Haka. A Haka na Gama js3 na danyi kiba kadan nayi tsawo irin na Mamana. A wañnan shekarar sister ta Gama law a UK ta dawo Nigeria Dan yin course din da zai saka ta samu licence din practicing a Nigeria. Har wannan lokacin bansan cewa Dadaa ba mahaifi na bane ba, Babu Wanda ya taba fada min ko da kuskure, ko da Wasa, kullum Ina daukar su Hajiyan Lagos matsayin dangin Mamana kawai Haka nake dauka, I was so naive ko hoton ta ban sani ba.

Wani yammaci na dawo daga islamiyya, fuskata tayi kulas kana kallona kasan akwai abinda yake damuna, tayi haske kamar bani da jini. A hankali na tako kafafuna zuwa gida, Ammi na zaune ita daya a parlor tana yankan farce, sakina na gefe tana ninke min kayana. Da sallama na shiga parlon, dukka Suka dago idanun su suna kallona tare da amsawa, na gaida Ammi sannan na amsa gaisuwar da sakina ke yimin. Daga Haka naje kitchen na dakko ruwa nasha na dawo Zan nufi daki na se naji muryar Ammi tace

" A'isha!"

Na Dan juyo a hankali na kalleta, yace

" Zo nan!"

Na juyo Baki daya na karasa inda take, tayi saurin aje blade din hannun ta, tasa hannunta ta gwale idanuna, idanun yayi fari alamar rashin jini, ta taba wuyana taji zafi rum, ta dago tace

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now