part 3

118 20 0
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

03. Free page

✍️Ayshatuuu

Kawun shi ya matsa kusa da maaikacin yace

" Idan da wani matsala yaro, ka fada kada ka bari a cutar da yarinyar mutane!"

Shi Yasan irin wannan information din is highly confidential, leaking information din marar lafiya ko client a asibiti is a punishable offence under court of law, dukkan wani Abu da ya shafi marar lafiya to sirri ne da Bai kamata a fada aji ba, to Amma Kuma kilan sunyi zargin hakan shiyasa suka dawo yin gwajin at the very last  minute. Hashir yayi shiru, ya rasa a wanne yanayi yake ciki, yanayi ne na tsoro, firgici da Kuma tashin hankali, gumi se karyo masa yake, he's drenched in his own sweat! Idanun shi sunyi jawur, wayace Masa karya ana cin riba, waye ya fada Masa karya tana 'ya'ya? Sede tayi fure. Sanin Babu wani abu da zai CeCe shi face ya fadi gaskiya da bakin shi yasa ya zube kasa, dukkan gwiwoyin shi a kasa,  sanye yake da farar shadda wadda A'isha da kanta ta fada Masa ita take so yasa a irin wannan ranar, ya Manta a laboratory yake,  inda dukkan wasu kwayoyin cuta zasu iya samun matsuguni, dukda Babu alamar jini, ko wani abu makamancin sample a flooring din, Amma dai munsan kasan nan bazaiyi rabo da microbes ba. Dadaa ya kalle shi, shima  Dadaa take kallo da kowa dake gurin a tsorace yace,

" Kuyi hakuri! Dadaa ka yafe min"

Dadaa ya runtse idanun shi Yana tsoron abinda kunnuwan shi zasu iya jiyo masa, kawun shi ya daka Masa tsawa tare da fadin

" Mu zaka mayar mutanen banza, me kake boyewa?"

Ya fada tare da wartar paper dake hannun Lab scientist din, ya bude, a take idanunshi sukai Ido hudu da HIV SEROPOSITIVE a rubuce, yayi shiru, Yana Kara blinking idanun shi, Dan tabbatar da abinda ke rubuce a jiki, Dadaa ya amsa takardar Yana dubawa kowacce kalma da yake furtawa bugun zuciyar shi na daduwa, ya dago idanun shi jawur Yana kallon Hashir, hannun Dadaa rawa kawai yake Yi saboda kasuwa, dakin yayi shiru dukkan su suna saurarar Hashir da Kuma Dadaa, Hashir bakin shi na Bari yace

" Nasan ni me laifi ne, kuyi hakuri ku yafe min. Dan Allah Dadaa!"

Dadaa ya riko hannun Hashir yasa Masa paper a ciki, cikeda bacin Rai Wanda zakaji a Amon muryar shi dukda ba ihu yake ba, yace

" Hashir ka sani tuntuni ka boye Mana? Me yasa Kai Haka?"

Idanun shi sun Kara yin ja yace

" Ban sani ba wallahi Dadaa, ban sani ba, ban sani ba se ranar da naje yin gwaji kafin lokacin da zamuje da A'isha, kawai aka fada min cewar I'm infected da virus din, bansan ya zanyi na fada muku ba, bansan yadda zanyi ba idan na janye..."

Kowa Banda nanata Inna lillahi wa inna ilaihil rajiun! Babu abinda suke, Baffa Muhammadu yace

" Me yasa baka fada ba, na tabbatar lokacin zaa iya gyara wani abun"

Ya Dan lumshe idanunshi, shi kadai yasan yadda zuciyar shi take, ji yake kamar duniya zata kife dashi, kamar an kwashe Masa dukkan kayan jikin shi, tamkar tsirara yake Kuma kowa na duniya na kallon shi,

" A'isha Ina son ta, bana son na sata Kuka, lokacin da na fahimci I was HIV positive already an saka rana, kiris ya rage ayi aure, Ina yawan tambayar ta zata iya aurena a kowanne Hali nake se tace eh, ni Kuma tausayi take bani bana son nayi breaking zuciyar ta, Dan Ina ganin idan ta rasa ni ba zata Kara trusting wani ba Kuma, shiyasa nayi Haka Dan Allah ka yafe min"

Dadaa ya gyada Kai yace

" You're mistaken Hashir...ko Dan zamuyi magana daga baya, Amma ka sani bazan iya aura maka A'isha ba, wannan abin da kayi baka kyauta ba, Ina ma ka fada tuntuni da tuni ta warke da rashin ka, Amma se yau Hashir, da banzo na kawo ka ba Haka zaka cuce ta ka cuce ni?"

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now