part 9

87 16 0
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

09.            Free page

✍️Ayshatuuu

Na Sha jini bayan ya Kare se nayi bacci kuma, a lokacin Dr Ismail yazo shi da Dadaa, ya Kara dubani sannan suka fita shi da Dadaa, Dadaa yace

" Doctor meye matsalar A'isha ne? Me yake faruwa da jinin jikin ta? Dama Haka kurum jinin mutum se ya Kare?"

Doctor ya girgiza Kai yace

" Ko daya, everything happens for a reason! Amma Kuma bawai se zubar jini kawai ke karar da jini ba. A yadda nake kallon A'isha Ina tunanin tana fama da sickle cell disease"

Dadaa yayi saurin kallon Doctor yace

"Sickler dai da nake ji ana fada?"

Doctor yace

" Eh Amma bamu tabbatar ba se mun Gama investigations tukunna, yanuzn dai jikin nata da sauki"

Ya koma ciki ya same ni na kankame bedspread Ina sakin siririyar Kara wadda yadda Baki na ke budewa da Kuma idan ka matso kusa Dani ne zaka fahimci hakan, Ammi na can tana dauraye min kayan da ta cire min saboda jini ya taba su. Yayi saurin karasowa Yana riko ni jikin shi yace

" A'isha menene?"

Ba tare da na bude idanuna ba nace

" Dadaa my legs!"

Ya Kai hannun shi kafafun nawa ya shafa, Amma ciwo se karuwa yake Haka ma Kuma ciki na da baya na. Ya Kira su Suka zo Suka min allura sannan na kwanta bawai Dan ya daina ba, se Dan ni din me juriya ce tun Ina yarinya, Ina da hakurin jure ciwo, se can Dan bacci ya silalo  ya dauke ni shi kenan Kuma se ciwon ya lafa! Dadaa ya saki ajiyar zuciya Yana fitar da huci me zafi daga bakin shi, ya riko hannuna Dan mitsitsi cikin nashi Yana ayyana irin ciwon da nake ji a jikina, fuskata tayi duhu saboda jini da aka Kara min, cikina ya Dan kumbura, nurse din da tazo tace tabbas signs din sickle cell disease ya fara bayyana a jikina. Se Bayan kwana biyu result ya fito, kamar yadda sukai tunani ita din ce wato SCD, Dr Ismail Bayan ya Gama going through result dina, ya zauna kujerar dake facing gadona, Ina jikin Dadaa Ina bacci yayin da Ammi ta tafi gida da wasu Kaya.

" Aboki na menene genotype dinka?"

Dadaa yace

" AA ne"

Dr Ismail ya danyi shiru Yana racking brain din sa kafin yace

" To nayi tunanin Kai AS ne maman ta AS, shiyasa kuka haifo SS"

Dadaa ya shafa kaina yace

" Ba 'yata bace, yarinyar Uncle Dina ce, dukkan su sun rasu ni na dakko ta Ina rukon ta ne"

Ismail ya nuna alhini tare da yiwa Dadaa adduar cigaba a rayuwa, a cewar shi ba karamin zumunci yayi ba da yake riko na tun kafin ma ya haifa nashi na Kan shi

"Ita dai sicker kamar yadda ake ce mata, ciwo ne na jini Wanda a iyakar bincike da akai Yana faruwa idan iyayen yaro suna da AS AS jini, to 75% na yaran su zasu Zama sickler yayin da 25% zasu tashi AS!  Babu wani takamaiman hanyar waraka sede ana bincike akan yiwuwar Bone marrow transplant wato a gaida ana ce Masa dashen bargon Kashi, tunda aikin shi ne producing blood cells ( yanzun ana yi, it's turning out a success, nace ba tabbas saboda Muna maganar lokacin Aisha na yarinya ne) shi ne ake tunanin zai iya Zama waraka, har yanzun turawa Basu Gama tabbatar wa balle yazo kasar mu"

Dadaa ya kalli Dr Ismail Dake ta bayani kamar a exam Hall yace

" So jinin ta zai dinga konewa kenan?"

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now