part 4

125 19 1
                                    


*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

04. Free page

✍️Ayshatuuu

Ina lokacin da zaka ji tamkar baka duniya, tamkar zuciyar ka zata fashe, tamkar the world will cripple at your feet? Haka naji, na kasa fahimtar a Ina nake, kwalkwalwata se aunawa take, Dadaa na aura? Dadaa a matsayin miji na? Meye Haka ? Meye yake faruwa? Wanne irin mummunan labari ne wannan? Se Kuma na fara tunanin to ko dai mafarki nake? Se na saki ajiyar zuciya with the hope mafarki ne Kuma Zan farka. Amma Kuma se ban farka ba in fact komai dake gabana is so real! A hankali na daura hannuna a idanuna na mirtsika Amma dai Haka dinne kowa da komai yana nan yadda yake, parlon yayi shiru Ina tunanin jiran ta inda Zan fara suke,Jin Shirin yayi yawa Dadaa ya karaso inda nake zaune ya riko hannuna, na dago na kalle shi, wannan dukka rayuwa ta baba na ne, da farko ban taba kawowa ba shi ya hafe ni ba, daga baya Kuma da na gane se na fara daukar shi uncle Dina ne, Amma daga baya se na fahimci we were only cousins!

*THROW BACK*

Sunana A'isha, kowa da kowa Haka yake cemin A'isha, bani da wani suna da ya wuce hakan Kuma na kasance Ina alafahari da sunana har gobe. Asalin mu Yan jigawa ne, da mahaifina da mahaifiya ta. Mahaifina Dan asalin Gwaram ne, family din shi sannanu ne sosae a ciki da wajen Gwaram da Kuma makwabtan jahohi, saboda akwai Wanda zaku ga tamkar sunyi gadon arziki ne, to family din babana kenan. Mahaifin su yayi gadon kasuwan ci da noma a gun iyaye da kakkani, suna safaran fata zuwa jahohi da wajen kasa, idan wajen noma ne Kuma sun shahara a noman auduga. Se ya kasance kamar idan kaje Gwaram ka tambaya Sarkin auduga bana tunanin ko karamin yaro zai gagara raka ka, an San gidan saboda fice da yayi. Wani abun armashi Kuma shi din Dan siyasa ne Wanda ke kokarin ganin ya taimaki talaka! So far they're famous. Matar shi daya Maimuna, ana kiranta hajja Muna, Kaka ta mace ce me karamci da dattako. Baffa Halilu shi ne babban Dan ta Wanda yayi karatu Kuma ya daura da noman auduga Amma ya Kara da wasu ba nan kadai ba. Se Baffa Jafaru Wanda shi ne mahaifin Dadaa na, Me bi Masa shi ne Baffa Muhammadu . Anty Amina ita ke bin Baffa Zubairu Wanda ke bin Baffa Muhammadu. Daga Anty Amina se mahaifi na Ismail, Wanda yaci sunan mahaifin shi, daga shi Kuma se Anty Fati wadda take matsayin auta a gidan. Dukkan su har matan Babu Wanda baiyi karatu ba, na Boko da na addini, sunyi karatu sosae da sosae Kuma arziki sun Tara su.

Mahaifina ban San shi ba na dai San hoton shi Kuma Ina jin labarin shi a wajen Dadaa da Kuma sister! Shi Kan shi Bai San an haife ni ba, Dan ko kafin Mamana ta haife ni Babana Allah yayi Masa rasuwa. Mamana sunan ta A'isha, sunan ta naci saboda tana Haifa ta ko kwana Bata Kara ba Allah yayi Mata rasuwa! I was brought up a complete orphan, Babu uwa Babu uba, uwa uba ga rashin lafiya! Kakana da ya haifi Abba da Kuma kakana da ya haifi Mamana dukkan su abokai ne na kusa, sunyi karatu tare Dan Haka da Abba ya kammalla makaranta, akai posting din shi Lagos nan yayi camping din shi a ikeja, bayan ya fito daga nan se ya fara serving anan Lagos din, da farko a corpers' logde yake na ma'aikatar daga baya da baban Mama yasan da shi se yayi kokarin ganin ya dawo dashi gidan shi, Bai so ko kadan ya koma ba saboda Bai fiye son Shiga mutane ba,  Amma baban shi yace ya kamata yaje kada ya ketare tayi. Shi ne yayi parking zuwa can.

Mamana ita ce 'yar shi ta wajen uku , a lokacin ta gama secondary ana kokarin ganin anyi Mata aure, saboda ita ce mace ta farko a gidan, Amma baban su Mama Yana ganin ya kamata tayi karatu, dukda lokacin gani ake ya bar yarinya katuwa yaki yayi Mata aure, ba lallai sunsan da zuwan zamannin nan ba, da aure ke farawa at the age of 25yrs, da zakaga mace ta Zama spinster batai aure ba. Kakata da ta haifi Mamana batayi karatu ba, so tana da limitations da yawa Wanda yasa take ganin gwara ace an bar Mama tayi karatu. A Haka dai sukai nasara ta samu gurbin karatu a university of Lagos! Dama ta Saba cudanya cikin su, itama ta goge da nacin karatu irin nasu. Sosae take karatu Dan ganin ta fitar da kowa kunya, zuwan Baba Bata ma San da zuwan nashi ba, Se da ya kusan sati daya bai hadu da ita ba, se cikin sati na biyu Yana zaune shi da brother dinta suna Hira, Uncle Auwal kusan sa'an Baba nane Dan shima lokacin Yana service sede stream din su ya banbanta. Suna zaune gaban gidan Hira tayi zafi, a lokacin ita Kuma driver ya sauke ta, ta fito hannun ta rike da handouts da wani katon text book Wanda a ka'ida ya kamata ace a gida yake ba yawo ake dashi ba, a haka nan dai take rike dashi, fuskar ta tayi maiko, idanun ta sunyi zuru zuru kana kallon ta kasan ta sha wahala Kuma a gajiye take, zamu iya cewa yunwa ma take ji. Tana bude kofa Suka dago suna kallon ta, Abba ya dube ta briefly ya dauke Kan shi yayin da Uncle Auwal ya dube ta yace

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now