part 8

80 19 1
                                    

*BANI DA LAIFI!*

_Top_Notch_

08.   Free page

✍️ Ayshatuuu


Mun dawo gida Bayan an sallame mu, jikina yayi sauki, Yan class din mu sun zo daga school sun duba ni, to Kuma Bayan min dawo Anty hafsa tayimin wanka, ta wanke min kaina, ta canja min kaya sannan nace Mata Zan Sha tea, ta shiga daki ta hado min tea me kauri cikin kayan tea dina, Dan daban Dadaa ke siyo min, ta kawo min cikin wata bottle Dita wadda tea kawai ake hada min a ciki, ko zafi banaji na fara zuka ta cikin straw, se Kuma na aje nace

" Anty Babu sugar!"

Ta kalleni tace

" Matsala ta dake kenan, kin faye shan Zaki"

Na Dan Bata fuska na aje bottle din, seda ta Kara sannan na dauka na shanye. Ina nan zaune da crayon hannuna Ina coloring letters a cikin alphabet book dina sallamar Dadaa ta saka na mike Ina murmushi, ya tsugunna na tafi wajen shi da fadawa jikin shi nace

" Dadaa na!"

Ya shafa kaina Yana tambaya ta ya jiki, na bashi amsa a hankali da sauki sannan ya kama hannuna muka shiga parlon Inna, tana zaune tana cin dafaffiyar gyada, Bayan ya zauna sun gaisa tace Masa

" Kaga na kusa manta babbar magana da nake son muyi da Kai"

Ya gyara zaman shi Yana Bata dukkan hankalin shi yace

" Wani Abu ya faru ne?"

Tace

" Eh, munyi magana da Alhaji ma. Ranar da aka kwantar da A'isha kazo ka same ni nayi bakuwa ko?"

Yace

" Eh Haka ne, wadda ta Kai hafsa asibiti ko?"

Inna ta gyada Kai ta cigaba da fadin

" Maman 'yan biyun ajin su A'isha ce'

Yace

" Ooh! Kuma fa Haka ne, sunyi Kama. Lafiya dai ko?"

Saboda ya kosa yaji me ya faru

" Mhmm lafiyar dai kenan! Wai akwai kanwarta Maryam, tace min Kun hadu sau uku da ita Wai"

Yayi shiru thinking hard ya tuna wacece Maryam? Yaushe Kuma Suka hadu da ita. Tasan ba lallai ya tuna ba hakan yasa ta fara Masa bayanin

" Wai ba tayi aure ba, kuma an damu da rashin auren saboda Bata kula kowa, anyi kokarin hadata da Yan uwa Amma taki yadda, shi ne bayan ta koma can Adamawar aka tambayeta ta fito da miji tace Wai Kai take so, ko sunan ka Bata sani ba tasan dai na A'isha!"

Tunda aka fara zancen so yake kallon Inna, to wacece ita? A yaushe ya ganta? How could she just start loving him Haka nan, to shi Ina ruwan soyayya, ita dai zuciya idan mutum yayi Mata ai kawai zata kissima maka ne kaji duniya Babu perfect mutum kamar wannan da kake so. Babu ruwan so da nisa, balle kyau, balle kudi balle Kuma asali, idan zuciya tana so tana so ne da dukkan karfin ikon ta na buga jini zuwa sassan jiki, kamar yadda take daukar sinadarin O² tana yawo dashi cikin jiki, Haka nan take daukar so, kafin wani lokacin dukka jiki zai dauka!

" Ba kace komai ba Yaya, ko baka raayi?"

Ya girgiza Kai yace

" Meye raayin ki Inna?"

Ta danyi murmushi tace

" Ka gwada ko zaa dace"

Ya gyada Kai yace

" Tohm na amince Zan aure ta"

Daga wannan maganar ya aje ni ya fita Yana amsa addu'oin da Inna ke Masa. Abu kamar Wasa yaje Adamawa, Bai tafi Dani ba na Sha kuka kuwa ranar, Dan har se da Inna tace an tsinko Mata bulala ta Zane ni, tunda ni na nuna su doddani ne, yaje ya ganta se lokacin ya tuna ta, ranar da ya fara kaini ya ganta ta kai twins school, se Kuma ranar birthday da ya Bata ni ta kula Dani, ta Dade tana Jin wannan yanayin Amma se take Jin kamar ranar ta daban ce da har yayi Mata magana tare da neman alfarma, taso kwarai ta daure, ta share kada ta Bari son da take Masa ya fito Amma ta kasa, ba zata iya ba, ba zata iya ba saboda Kan shi ta fara sanin so. Bayan Baffan ta ya tambaye ta mijin da take so, kamar ko da yaushe tace ita Babu, in fact Bata shirya ba, nan fa ya fara fada Yana fada Mata har se yaushe ta shirya yin aure? Ba taga shekarar ta Sha takwas ba, ta fara jami'a to me take son Yi, shi 'yayan sa, at 17years sun haihu se ita, to tabbas zai Bata duk Wanda yayi niyya, wannan threat din yasa ta furta Dadaa take so, Amma kunsan me? Ammi Bata San sunan shi ba, tasan mahaifin A'isha ne, A'isha class mate din su Jidda ce, yaran yayar ta. Tana fada Baffa ya Aiko nan Kano wajen Yar shi Dan a tambaye ta, da kyar ta gane ta Kuma samo adreshin mu, shi ne tazo gida dukda da farko Taki, tana ganin har yaushe mace zata ce tana son namiji, kamar hakan abun kunya ne a wañnan lokacin, dadin dadawa su Fulani ne da ya kamata ace suna da kawaici da kunya, Amma Kuma se Abban su Jidda ya nuna ba wani Abu bane, kowa Yana da zuciya Yana Kuma da right din da zai so Wanda yake so! To Kuma se gashi Allah yayi magana tayi nisa.

Ba Ni Da LaifiWhere stories live. Discover now