Free page (Chapter 1)

472 23 2
                                    



*PART OF OUR DESTINY*

*I DEDICATED THIS BOOK TO MY BEST FRIEND FOREVER HALIMA NURU MURTALA (AMEERA)*

*1/September/2023

*Free page*.
*Chapter 1*

(ABUJA NIGERIA)

*ASSIDIQUE ATTOM EL-FAROUQ CONSULTANT HOSPITAL*

Thursday 2:00 Am.
Wannan daren ya kasance wani irin dare mai d'auke da tsananin duhu, hadi da cushewar yanayi, kasantuwar  babu wata yalwatacciyar iska dake kad'awa had'i da kai komo acikin wani sashi na garin, wanda hakan yana daya daga cikin abunda yasa, ko ina yayi shiru, bakajin tashin sautin komai kasancewar garin babu wani annuri, saboda sama da tayi duhu dulum, babu hasken farin wata ko kad'an, haka ma taurari sun disa she, hakan yana d'aya daga cikin abunda yasa duniyar tayi duhu, yayinda ko ina yayi shiru babu motsin kowa, saboda adaidai irin wannan lokacin, kaso 70 acikin d'ari na daga mutanen dake rayuwa acikin k'asar ta Nigeria bacci suke, kasancewar masu iya magana sunce dare mahutar bawa, duk da kuwa ansan garin na Abuja darensu tamkar rana yake.

Sab'anin hakan ne ya kasance daga wani sashi mafi rauni, sashin da rauninsa ya rinjayi k'arfinsa.
Domin adaidai lokacin da wata zuciyar ke samun nutsuwa, daidai lokacin wata zuciyar ke bugawa cike da d'imuwa, hadi da tashin hankalin dake barazanar dakatar da rayuwar me dauke da wannan zuciyar.

For Almost 27 hours.
Numfashi ya gagari gangar jikin da tafi buk'atar macewa fiye da rayuwa, kasancewar ta share tsawon awanni batare da tasan inda hankalinta yake ba, idanunta sun rufe kirib, bugun zuciyarta kuwa na k'arayin k'asa acikin kowani minute,  irin na rayukan da ke kokarin barin gangar jikinsu.
Sam ta manta da duniyar da take, ta manta wacece ita, dama duk wani abu daya shafe ta, sakamakon tsawon awannin da ta share ba tare da wani numfashi na kai komo acikin k'irji da gangar jikinta ba, wanda hakan yana d'aya daga cikin abunda yasa take jin tamkar ba'a tab'a wanzar da irinta ba a doron k'asa.

After Some hours....
Wani abu k'alilan ne ya ragewa zuciyar mata tsayawa cak daga bugun da take yi, batare da sanin cewa akwai wata sauran rayuwa daya rage mata anan gaba ba, batare da saninta ba akwai rayuwar da zatayi me d'auke da mabanbanta k'addarori ba, rayuwar da bata isa guje mata ba, domin rubutaccen Al'amari ne da dole sai ya faru.
Bisa dole badan ta shiryawa hakan ba, cikin k'arfin hali had'i da fafutukar da zuciya da kuma gangar jikinta keyi, wani wahalallen numfashi ya soma ziyartar kirjin ta, had'i da kokarin daidai ta bugun zuciyarta, wanda bisa jagorancin hakan, ahankali ta soma motsa babbar y'ar yatsar k'afarta, dake sandare,  ta bushe tsawon lokaci tare da k'andarewa kamar jikin gawa.
Ci gaba da motsa yatsun k'afar nata tayi ahankali, batare da ta bud'e idanunta ba, taja wani irin dogon numfashi, sakamakon wani irin abu me tsananin ciwo da take ji na kai komo acikin gangar jikin ta.

Ahankali ta fara yunk'urin bud'e idanun nata dake kulle gam, amma abun ya gagara, dalilin wani irin hargitsewa da take jin k'wak'walwar ta nayi, lokaci d'aya wasu birkitattun tunani ke kutsowa cikin kwakwalwarta, sanadiyar haka yasa duniyar ke juya mata, duk da idanunta da suka kasance a rumtse, amma da azaban k'arfi komai ke juyawa agareta, wanda kuma hakan shi yayi sanadiyar fara dawo da ita cikin hayyacin ta, har yakai ga numfashin dake kai komo acikin kirjinta ya soma fita da sauri sauri.

"Haaaaaaahhh! Heeeeee!!"
Awahalce taja wani irin dogon numfashin, daya sanya ta sake yunk'urin bud'e idanunta akaro na biyu, wanda suka kad'a sukayi jajur gami da k'ank'ancewa, kasancewar tuni suka kumburo, tare da dunk'ulewa tamkar wanda aka watsa wa curin k'asa acikinsu.
Ci gaba da bud'e idanun nata tayi, tana jin kanta na wani irin juyawa, domin yanda ta dage sai ta bud'e idanun nata yasa hatta veins din dake rik'e da jijiyoyin idanun nata saida suka motsa, ji take wani kalan azaba da rad'ad'i na ratsa kowani gab'a dake sassan jikinta.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now