Free page (Chapter 11)

53 2 0
                                    


@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it, here is the account number for people that are willing to pay-2268498748 fatima abubakar uba bank, amount 500, WhatsApp number 07069917168)*

*Free page*
(Please don't forgot to follow me on AREWABOOKS @fatymasardauna)

*Chapter 11*

Jin haka yasa Saed driver karya akalar motar kaitsaye ya nufi Jabi Lake.

Koda suka isa bayan ya daidaita parking, shiya fito ya bud'ewa Dr. Emraan din murfin motar, wanda ya fito cikin nutsuwa ya nufi cikin babban mall din, yayinda Sa'id ke biye dashi, kasancewar shi yace ya biyo shi.

Akaron farko na rayuwarsa da zaiyi wa wata y'a mace sayayya, hakan yasa yake jin kansa wani iri, daurewa yayi ya nufi side din daya tabbatar zai samu abubuwan da yake so.
Kayayyakin sawa ya fara d'auka yana sawa acikin trollyn da Saed ke rik'e dashi, doguwayen riguna dubai an Egypt abaya's, duk da baisan size dinta ba, amma a idanunsa ya kamanta yanayin tsawonta, domin ba doguwa bace sosai haka kuma ba guntuwa bace, yasan ba zata tab'a wucewa size 57 to 58 ba, kayan yake d'iba batare da tunanin kudinsa ba.
Expensive Abayas masu matukar kyau da tsada ya dinga d'iba yana zubawa a keken, bayan ya gama da b'angaren abayas dinne kuma ya dawo kan expensive skirts, haka suma yayi ta kwasa wasu skirts din straight, wasu kuwa denim prairie skirts ne, sunray pleat skirts, sai kuma riguna irinsu, shirts, kimono, dolman, maxi, da kuma wanduna irinsu Pallazo pant, wide leg, stirrup, boot-cut flared, daganan kuwa b'angaren mayuka ya wuce, bai san mayukan mata da kayan kamshinsu ba, saidai yana amfani da suna wajen ganin ya dau abu me kyau.
Set na Supremÿa Baume ya dauka da kuma set na SK-||, and Victori's Secret set, sai kuma set na Fenty Skin, irinsu, Pre Show Glow, Overnight Recovery Gel Cream, Fat Water, Hydra Vizor, Total Cleanser, ab'angaren Liquid kuwa Strâtia Liquid Gold ya dauka, tare da set na CereVe, irinsu moisturising cream, foaming cleanser, moisturising lotion, hydrating cleanser, facial moisturising lotion, komai na amfanin mata saida ya dauka hardai perfumes, like, Mon Guerlain, Chanel N°5, Si Passione, Hypnotic poison na companyn Dior, Blue de Chanel, Flash Jimmy Choo, da kuma Libre (YvesSaintLaurent).
Bayan ya gama da b'angaren perfumes, b'angaren kayan ciye ciye ya nufa, chocolates, sweets and biscuits ya saya mata masu yawan gaske, duk da baida masaniya akan abunda take so, amma yayi imani fiye da rabin mata suna son ciye ciyen kayan zak'i.
Daga b'angarensa kuwa kasancewar yana jin yunwa, robar Boba tea ya dauka guda d'aya, still Sa'id na biye dashi suka nufi wajen biyan kudi, da k'yar Sa'id ke iya tura babban trolly din da Emraan din ya cika shi da kaya, wanda yawan kayan yasa ba k'aramin lokaci suka b'ata wajen biyan kudin ba, saboda kayan nada yawa, card d'insa ya bada aka cire kud'ad'e masu yawan gaske, sannan suka fito daga cikin mall din, anan bayan motansu aka loda kayayyakin.

Kafun Direct suka nufi gida.
Yana zaune acikin motor ya bud'e Boba tea din nasa yana sha, kasancewar sam shiba mutum ne me jure yunwa ba, shiyasa bai iyajin zai jure har ya isa gida batare da yasa wani abu acikinsa ba.
Tafiya me d'an tsawo sukayi kafun suka iso gidan, da yanayin kasala ya fito daga motan, kaitsaye ya nufi main parlorn nasu, yayinda Sa'id da sauran ma'aikatan gidan ke biye dashi da tik'a tik'an ledodin sayayyar, tura k'ofar yayi ya shiga bakinsa d'auke da sallama.

Aamma na zaune akan lallausan carpet din parlor'n tana matsawa Ammabuwa dake kishingid'e k'afafunta.
Jin muryarsa yasa ta d'agowa fuskarta asake ta amsa masa sallaman, tare dabin ledodin da aketa shigowa dasu da idanu.

"Ammana Barka da gida."
Ya fad'a adaidai lokacin da yake zama akusa da ita kan carpet din.

"Yawwa Emraan barka dai, ya aiki da gajiyar hanya?"

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now