Free page (Chapter 4)

86 7 0
                                    

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*free page*
*CHAPTER 4*

Sai alokacinne Kuma ta samu wani wahalallen bacci ya d'auketa.
Ab'angaren Khalty kam yanda taga rana haka taga k'arishen daren, domin zama dirshan tayi ta dinga kuka harsai da hawayen nata dan kansu suka gaji suka daina fitowa daga idanunta.

ASOKORO.
Duk da sassanyar iskan safiyar dake kad'awa had'i da sanyin A/C'n dake busawa cikin d'akin, hakan bai hana jikinsa tsattsafowa da gumi ba, kasancewar kuma babu riga ajikinsa shiyasa zufan nasa k'ara yawai ta, cikin wani irin mawuyacin yanayi yake nannad'e jikinsa, had'i da fitar da wani irin numfashi mai kama da nishin wahala, wanda daga jin yanda sautin ke fita, da Kuma yanda yake ta nannad'ewa waje d'aya tamkar maciji, zaka fahimci cewa ciwo yake ji acikin jikinsa, duk yanayin nasa yafi kama dana wanda baya cikin hayyacin sa.
Yana kwance ahakan ya soma jiyo wani irin
k'ara dake kokarin fasa kunnuwansa, azabure cikin tsoro had'i da firgita ya bud'e idanunsa dake rumtse k'am tare da tashi zaune, yana me k'arewa d'akin nasa kallo cikin matsanancin tashin hankalin daya bayyyana akan kyakkyawar fuskar sa.

Wani irin numfarfashi yake maidawa, tare da sanya hannu ya dafe kansa, ahankali cikin muryar sa da ta disa she ya furta kalmar.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajun!!"
Gami da jan wani dogon numfashin daya ida k'arasa dawowa dashi hayyacinsa.
D'an jim yayi na tsawon wani lokaci, yana jin mummunan mafarkin nasa na dawowa cikin brain dinsa filla filla,kansa dake ci gaba da sarawa ya rik'e, domin ko sau d'aya bayason tuna mafarkin nasa, dake kokarin tuna masa wanene shi, domin aduk lokacin daya tuna da hakan, ya kan samu kansa cikin matsanancin tashin hankalin, dake tafiya da duk wani nutsuwar zuciyar sa, akowacce rana ta duniya daurewa yake, domin tuna yana d'auke da wani rubutaccen k'addara acikin jini da b'argonsa ya kansa shi d'imaucewa.

Ahankali cikin rashin kuzari ya zuro da k'afafunsa k'asa, tare da mik'ewa tsaye,  cikin mummunan yanayin daya samu kansa aciki, kaitsaye ya wuce bathroom dinsa dan yin wankan, daya d'auke shi 30mn kafun ya fito d'aure da towel akan waist dinsa.
Agogon dake sak'ale asaman gadonsa ya kalla, wanda ya nuna masa 7:30 am daidai.
Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e tare da soma shirya Kansa, cikin wani dogon wandon Calvin Clein, da kuma t shirt na DIOR.
Yayi kyau k'warai cikin shigar da ta amshi jikinsa. White Sneaker shoe ya sanya ak'afafunsa, had'i da feshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi, agogonsa na companyn GUCCI ya sanya, tare da d'aukar wayarsa dake kan bedside, cikin tafiyarsa dake kama dana isa ya fice daga d'akin.

Ahankali yake sauk'owa daga kan matattakalan falon, inda jin k'aran takun tafiyarsa Yasa Aamma dake zaune acikin falon d'agowa ta kalleshi.
Fuskarta d'auke da kulawa tace.

"Emraan you're awake."

Kai ya jinjina adaidai lokacin da yake k'arasowa cikin falon, murya asake yace.
"Yes Aamma na tashi, baccin ne duk ya isheni, am going to the hospital ."

Da mamaki Aamman ke kallonsa jin yace asibiti zashi, domin asaninta ko wani weekend Yana k'aresa ne gida, baya zuwa asibiti har sai idan abun gaggawa ne ya taso.
Wannan yasa ta yi masa kallon tsab, da yanayi irin na tuhuma tace.

"What will you go there and do ."

Bai tab'ajin tambayar Aamman ta haifar masa da fad'uwar gaba ba sai yau, domin shi kansa yasan bashi da wani reason na zuwa hospital din, saidai yasan a can d'inne kawai zaije ya samu relief, had'i da y'ancin da zaiyi watsi da duk wani abu dake ranshi, idanunsa ya d'an lumshe tare da marairaice fuska kana asanyaye yace.

PART OF OUR DESTINY Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang