Free page (Chapter 7)

95 11 1
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*Free page*
*CHAPTER 7*

Jin maganan Ammabuwan yasa shi lumshe idanunsa da sukai jajur lokaci d'aya, tare da had'iyan wani abu me d'aci da ya tsaya a mak'oshinsa.
Kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa, da k'yar ya iya jan k'afafunsa da sukayi nauyi ya nufi saman.
Yana k'arasawa kuwa direct bedroom dinsa ya shige, wanka ya farayi, tare da shirya kansa cikin weat color Jallabiya dake tashin k'amshin Armani/Prive, kasancewar kuma an soma k'iraye k'irayen sallan magrib, hakan yasa tun daga cikin toilet din ya d'auro alwala yana gama shiryawa direct ya sauk'o dan wucewa masallaci.
Baisamu kowa a falon nasu ba, domin Ammabuwa cikinta na cika ta gudu d'akinta.

Kaitsaye masallacin dake d'an gefe da gidan nasu ya nufa, yana tafiya yayyafin da akeyi na sauk'a akan jikinsa.
Masallacin ya shigo yabi sahu kasancewar har sun tada sallan, suna cikin sallan wani ruwa me k'arfi ya kuma b'allewa, wanda hakan yasa dole limamin ya had'a musu sallolin biyu wato magriba isha, saboda ruwan yau d'in jeka ka dawo yake yi, sai an fara ya tsagaita, kafun wasu y'an mintuna kuma sai ya sake  dawowa.

Lokaci me dan tsawo suka dauka kafun suka idar da sallan, bayan kuma kowa ya kammala addu'oinsa, aka fara fita da d'ai d'ai, ganin haka yasa Emraan d'in tank'washe k'afafunsa, anutse yake kallon dandazon mutanen da ke ta fita daga cikin masallacin dan komawa gida.
Kallonsu yake da da raunatattun idanunsa, had'i da karyayyar zuciyarsa da sam bayason karayarta ta bayyana, har a k'asan ransa yake jin wani irin yanayi me kama da tarin damuwa.
Acikin wannan duniyar sau tarin lokaci yakan zauna ya kalli mutane, yana me sak'a wasu abubuwa da yawa acikin ransa.
Abayyane yake yiwa kansa fatan.
"Ina ma da ace yana d'aya daga cikin jerin mutanen nan."
Ya fad'a yana me lumshe idanunsa da sukayi ja.
Yayinda acan k'asan zuciyarsa yake magana da zuciyarsa.

"Duniyar mu cike take da tarin k'addarori, yayinda kowannen mu yake d'auke da kalan nasa k'addarar, amma shin me yasa shi nasa k'addarar ya banbanta dana sauran mutane, me yasa k'addararsa ta kasance me matuk'ar munin dake karyar masa da zuciya akoda yaushe? Shi kad'ai yasan yanda yake ji, acikin kowani rana ta duniya idan ya tuna da mummunan k'addararsa dake bibiyan rayuwarsa, me yasa ya samu kansa ahaka? Ya zamo na daban acikin mutane, kowa yana yi masa kallon cikakken mutum yayinda shi kuma yake yiwa kansa kallon bura gurbin k'wai marar amfani, shin ahaka zai tabbata?"

Yayiwa kansa tambayar dashi kansa yasan bashi da amsarta, ba kuma yi dame amsa masa ita, domin aduniya babu wanda yasan menene b'oyayyar k'addarar daya kwashe tsawon shekaru yana b'oye wa, shi kad'ai ya san komai daya dangance sa, kamar yanda shi kad'ai yasan abunda yake ji acikin kowacce rana ta duniya.

Idanunsa ya lumshe tare da d'an motsa labb'an bakinsa ahankali ya furta kalmar.
"Astaghfirullaha wa atubu Ilayh!"
A sirrance saboda gudun kada ya aikatawa ubangijinsa laifi, sakamakon tuhumar da yake yi, wanda yasan matuk'ar zai yawaita tuna irin k'addararsa, to fa watarana lallai zai kauce hanya, imaninsa zaiyi rauni.
Abu d'aya kawai yayi believing shine matuk'ar ya yarda da Allah, to ya zama dole ya yarda da k'addararsa me kyau da marar kyau.
Saidai har yaushe ne wannan zafi da radadin da yake ji ak'asan zuciyarsa zai warke? Yaushe zai daina jin kansa amatsayin bare, sai yaushe sanyi zai ziyarci wannan kirjin dake cike da tarin damuwar da yagaza iya bayyanata ga kowa?

Lallai ita destiny abune da muke rayuwa da ita yau da kullum, ta riga ta zamo wani sashi na rayuwa da kowani ruhi da gangar jiki ke rayuwa akan ta, amma abun tambayar shine, akwai wata rana da tasa k'addarar zata sauya? ance komai yayi farko yana da k'arshe, amma akan wannan yana da tabbacin cewa ba komai ne keda k'arshe ba, wannan k'addarar tasa bata da k'arshe, Idan kuwa tana dashi, to sai yaushe ne zaiji d'and'anon sanyi daga cikinta?
Sau da yawan lokuta yana da buk'atar nutsuwar zuciyar da zai iya tantance fari ko bak'i, haske da kuma duhun dake cikin rayuwarsa.
Yasani bazai tab'a iya tantance asalin abunda yake so ba, domin ya samu kansa acikin wani bak'on yanayi irin wanda bai tab'a ji ba aduk rayuwarsa.
Bai san dame zai k'irayi abunba.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now