Chapter 16

90 3 1
                                    


*POOD*

*16*
Idanunsa ya rumtse da k'arfi, cikin sauri had'i da matsanancin takaici ya jawo towel din nasa dake k'asa, ya d'aura akan waist dinsa.
Wani irin bak'in ciki da b'acin rai yaji daya san yashi zubawa yarinyar idanunsa, wacce jikinta ke faman kyarma hadi da wani irin karkarwan da yasa numfashinta sark'ewa.
Ji tayi tamkar an watsa mata tafasashen ruwan zafi ajikinta, lokaci daya batare da sanin me zatayi ba, cikin matsanancin tashin hankalin da ta samu kanta aciki ta fasa wani irin ihun daya karad'e gaba d'aya falon.
Har yakai ga kunnen Dr. Emraan, wanda jin ihun nata acikin kunnuwansa yasa shi fitowa cikin hanzari, wanda fitowar nasa kuwa yayi daidai da yankan jikin da tayi zata fad'i, cikin sauri ya rik'ota da yanayin matuk'ar mamakin abunda ya kawota side dinsu.
Hannayensa duka biyu yasa ya rik'ota sai dai Duk da haka bata fasa fad'uwan ba, luuuu haka ta tafi ta fad'a jikinsa, abunda ya matukar d'aga masa hankali kenan, cikin sauri ya soma jijjigata yana kiran sunan ta.
"Yacine! Yacine!!!"
Ya ciga ba da kiran sunan nata da yanayi na dan daga murya, still yana me girgizata domin atunaninsa suma ta yi.

Yayinda ita kuwa da ta fara fita hayyacin ta, jin muryarsa acikin kunnuwanta ne yasa ta sanya hannayenta ta k'ank'amesa da k'arfin gaske, tana me sakin wani irin k'yarmar tsoron, da yasan ya ko bud'e  idanunta ta kasa yi, wani irin mummunan gani tayi haka?
Dr. Emraan kuwa ganin irin rik'on da tayi masa ne yasa shi rud'ewa, lokaci d'aya yana me jijjigata ya soma fad'in.
"Oya bud'e idanunki Yacine, me kikeyi anan? meya sameki, bud'e idanunki kinji, bud'e idanunki ki fad'a min meya faru?."
Ya k'are maganar cikin matuk'ar rud'ewar da yasa, Yacine din sake mak'alk'aleshi, kana atsorace ta soma bud'e idanun nata, cike da fargaba hadi da fatan kada Allah yasa ta kuma yin tozali da abunda ta gani d'azun.
Ahankali takai kallonta ga bakin k'ofar, har yanzu yana nan tsaye d'aure da towel, hakan yasa tana d'ago idanunta ta jefasu acikin nasa idanun.

Wani irin azababben shock me tsanani ne taji ya shigeta, wanda hakan yasa afirgice cikin wani irin zabura ta janye idanun nata daga kallonsa, tare da sake mak'alk'ale Dr. Emraan, had'i da maida idanunta ta rumtse su k'am.

Da mamaki Dr. Emraan ya kalleta, kana ya dawo da kallonsa ga TAE wanda yake tsaye har yanzu a bakin k'ofar yana ganin ikon Allah.
Yarinya tayi masa laifi, ta kallesa tsirara shi baiyi komai ba, sai ita ne zatayi wani abu kamar me Aljanu.

"Kaine ko TAE? Me kayi mata?"
Dr. Emraan ya tambaya.

Fuskarsa ya sake had'ewa sosai, tare da gyara tsayuwarsa, cikin nuna halin ko in kula ya d'age shoulders dinsa sama, batare da nuna damuwarsa akan lamarin ba, murya adak'ile yace.

"Oho I don't know."
Yayi maganar yana me juyawa, tare da sanya hannu ya jawo k'ofarsa, ahankali ya saki siririn tsakin, da yake yawan yi idan ransa ya b'aci.

Ganin haka yasa Dr. Emraan kamo k'afad'un Yacine din, ahankali ya soma jijjigata, cikin tausasa murya yace.
"Is okay Yacine, bud'e idanunki kinji, bud'e idanunki ki kalleni, gashi duk kin b'ata jikinki da coffee, kalla har mug din coffee din ya fashe."

Yayi maganar yana me gyara mata rigarta data d'an bud'e ta k'asa, had'i da zuba mata idanunsa saboda ganin taki ware idanunta, sannan ta kuma ki sakinsa, gashi har yanzu jikinta rawa yake.
Kyawawan eye lashes dinta ya zubawa ido, yana kallonta har zuwa kan madaidaicin hancinta me d'auke da siririn kara, da ya zauna daidai akan kyakkyawar fuskarta, tare da k'arawa fuskar nata kyau, musamman ma daya kasance acan k'asan pointed noise din nata, akwai beautiful lips din da basu da girma sosai, saidai suna da d'an tudu kad'an, kana kuma suna da kala me burgewa, yayi imani cewa komai na fuskarta me kyaune, tun daga kan kintsatstsen eye brow dinta, har zuwa kan yalwataccen gashin daya kwanta agaban forehead dinta zuwa gefen kunnenta, ita din kyakkyawane ta sosai da sosai, wanda koda baka nutsuba zaka gane hakan, ballantana Idan ka k'ura mata ido, to anan zaka gane cewa tana da wani irin sirrin kyau me daukar hankali, musamman a yanayin launin jikinta, fara ce sosai, amma ba irin fari me launin ja kome surkin yellow ba, skin d'inta like milk kuma yana da taushin gaske, sai kuma tarin sumar kanta wanda ya kasance brown black color, wanda saboda tsabar laushinsa har nannad'ewa yake yi shi kad'ai.
Idan ka kalleta exactly tafi kama da Mauritanian, saidai ta wani fanni kuma tafi yanayi da Tuareg din Algeria, wanda kyaun nata ya samo asali ne kasancewar ta ruwa biyu.
Numfashi me k'arfi yaja, tare da kauda idanunsa daga kallonta, batare da yasake cewa komai ba, ahankali ya kamo kafad'unta tare da soma kokarin mikar da ita tsaye.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 04 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now