Free page (Chapter 14)

85 6 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay if you know you didn't pay please don't read it, here is the account number for people that are willing to pay-2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, amount 500, WhatsApp number 07069917168)*

*(Please don't forgot to follow me on Arewabooks @fatymasardauna)*

*Freepage*
*Chapter 14*

Akan strawberry'n dake cikin wani elegant potpurri bowl dake tsakiyan dining table din, ahankali yasanya strawberryn abakinsa, lokaci d'aya kuma yana me janye idanunsa daga gare ta, tare da kokarin danne abunda ke zuciyarsa.
Wanda yake neman samawa kansa muhallin da bai cancanta ba.
Hankalinsa ya maida kan abincin da Aamma ta zuba masa, wato Cajun Shrimp corn chowder, da kuma fried plaintain and egg sauce, azahirin gaskiya cin abincin yake yana ji kamar anyi masa dole, bawai kuma dan baya jin dandanon abincin bane, daddad'an d'and'anon hannun Aamman nasu dabanne, saidai kawai asalin matsalar daga zuciyarsa take, domin kuwa nema yake ya rasa sukuninsa akan komai.
Tun bayan daya fara sanyata acikin idanunsa ya rasa duk wani nutsuwarsa gaba d'aya, muskutawa yayi tare da sake satan kallon ta akaro na biyu, tana nan zaune har yanzu bata fara cin abincin ba, sai wasa kawai da take yi da y'an y'atsun hannunta.
Ganin haka yasa shi d'auke kansa, tare da dawo da kallonsa ga Ammabuwa, wacce ke nufowa dining table din, cikin jan k'afafunta da sukayi tsami, ganin haka yasa shi mik'ewa tsaye daga zaunen da yake, k'arasawa yayi ya kamo hannun Ammabuwa'n tare da zaunar da ita akan kujerar dake gefen nashi.
Atausashe yace.
"Jiya kuma wasu irin chocolates haka kika kwana kina sha?"
Ya k'are maganar yana me duban k'afafun nata.

Harara ta watsa masa, cike da masifa kuma gudun kada ya gano gaskiya yasa ta cewa.
"Bansani ba, ni fa bana son sa idon banza dana wofi, Allah ne ya daura min ciwonnan ba wani ba, saboda haka shi zai yaye min ba sanya idanun wasu ba, kuma shikenan sai ace Allah baya daurawa bawansa ciwo saida dalili, ko nasha ko bansha ba Allah yace dole sai k'afafun sun kumbura, sai naga wanda zai hana."

Murmushin daya bayyana kyawawan dimples dinsa yayi, atausashe batare daya kalleta ba yace.
"Hakane kam, amma me hali baya tab'a fasa halinsa, sannan marar gaskiya ko acikin ruwa ance gumi yake yi, anyway ni meye ma nawa aciki idan kika rasa k'afarki ai kinga kin huta muma mun huta, inaga sai kowa ma yafi samun nutsuwa."

"Eh dole kace haka, to ta Allah bataka ba, wallahi ni duk meson ganin baya na bazai gani ba, kuma ka daina wani kwane kwane, kawai ka fito fili kace ka gaji da ganina a duniyar, yo wannan ne kuma ko ubanka bai isa yace haka ba."
Ta k'are maganar tana me juyowa ta kalli Aamma, cikin yin kicin kicin da fuska tace.

"Samin abinci naci, gaba d'aya na kasa cin wancan wanda kika kaimin, wallahi da raina da lafiya ta ba zaku ta ciyar dani da abubuwa marassa dadi ba."

Idanu duk suka zuba mata jin tana kiran kanta me lafiya, matar da take fama da diabetes wai ita ke kiran kanta me lafiya, saidai kasancewar sun san halin fad'anta, yasa babu musu Aamma ta zuba mata abincin, tare da komawa ta zauna, abincin duk suka ci gaba daci atare, amma banda Yacine wanda sai yanzu ne ma ta d'au mug din tea ahannunta tana sha kad'an kad'an.

Bayan wasu y'an mintuna ahankali Aamma ta d'ago kanta ta kalli Abbou daya riga kammala cin abincin, maganar dake bakinta take son furtawa, duk da batasan zaiyi farinciki ko akasin hakan ba, amma ya zama dole zata fad'a, d'an gyara zamanta tayi kana cikin k'arfafawa kanta guiwa tace.

"Munyi waya da Taariq, yace gobe zai dawo, ina da tabbacin kuma yanzu idan ya dawo bazai koma ba."

Wanda jin abunda ta fad'a yasa Abboun tsayawa cak daga abunda yake, kasancewar bakinsa yake gogewa da tissue, tsawon seconds kamar zaiyi magana kuma sai yayi shiru, yayinda Emraan kuwa idanu ya zubawa Amman nasa, batare daya ce komai ba.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now