Free page (Chapter 3)

105 6 0
                                    

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*Free page.*

*CHAPTER 3*

Saboda girman kalmar, wacce koda sau d'aya bayason jin wani abu daya dangance ta, domin acikin yan kwanakin nan, gaba d'aya irin wannan cases din suke samu.
Jim ya d'anyi na wani lokaci, kafun ya tattare file d'in dake gabansa, had'i da folder'n nata ya tura acikin drawer'n sa, jikinsa amace haka ya mik'e tsaye hannunsa rike da wayarsa ya fice daga office din.
Kasancewar 1 pm ta cika harda wasu yan mintuna.

Direct parking space d'in hospital d'in ya nufa, domin yasan zuwa lokacin Sa'id Driver na nan yana jiransa.
Kamar yanda ya tsammata kuwa hakanne ta kasance domin Sa'id d'in ya jima da zuwa, wanda hangosa da yayi ne yasa shi tashi cikin sauri ya bud'e masa murfin mortar.
"Barka da fitowa Sir."
Sa'id driver ya fad'a alokacin da Dr. Emraan din ya k'araso.
"Yawwa."
Ya amsa masa agajarce had'i da shigewa cikin motar, wanda ganin hakan yasa Sa'id d'in shima shiga ahanzarce yaja motar suka fice daga cikin asibitin.
Kaitsaye shumfud'add'iyar hanyar da zata sadasu da Annor Mosque suka nufa, domin abune da Sa'id din yasani, kusan ko wacce jumma'a anan Dr. Emraan din keyin sallah, duk da cewa yau d'in sun d'an makara, wanda hakan yasa Sa'id na gama daidaita parking din motar, ya fito da hanzari hannunsa rike da bottle water, dashi yayi alwala tare da wucewa cikin masallacin kaitsaye.
Bayan an idar da sallan addu'o'i yayi kamar yanda ya saba, har na tsawon wasu mintuna kafun ya fito daga cikin masallacin, anan waje ya samu Sa'id tsaye ajikin mota, wanda already ya riga daya idar da nashi sallan.

"Mu tafi ko."
Ya fad'a yana me shigewa cikin motar, daga haka Sa'id yaja suka tafi.
Tafiyar wasu y'an mintuna sukayi, kafun suka iso cikin rantsatstsiyar unguwar Asokoro, wacce ta k'unshi kyawawan gidaje na gani na fad'a.

Anan cikin unguwar ta Asokoro, gaban wani rantsattsen mansion, daya amsa sunansa motar tasu ta tsaya, tare da soma danna horn, cikin y'an mintuna kad'an aka wangale musu gate d'in, wanda shi kad'ansa ma kan iya d'aukar hankalin mai kallo.
Atsanake Sa'id driver ya tura hancin motar cikin katafaren gidan, da kyau da had'uwarsa ya wuce tunanin mutum, domin kuwa babban gida ne me d'auke da dogon ginin zamani, me matuk'ar k'ayatarwa, wanda yake d'auke da babban compound  had'i da babban lambu, uwa uba babban Parking space da cikinsa ke cike da tarin tsadaddun motoci, tamkar wani karamin wajen saida motoci, daga can gefen dama kuwa wani tabkeken swimming pool ne, da aka k'awatasa da flowers had'i da kyakkyawan ruwa me burgewa, after swimming pool din kuwa wasu flat part ne guda biyu manya manya, da akayi musu ginin zamani.
Komai na cikin gidan ya tsaru iya tsaruwa, domin an cikasa da kyawawan shuke shuken, flowers kala daban daban da suka k'ara bayyana tsananin kyau'n gidan.
Acikin babban rumfar Parking Space d'in, Sa'id yayi parking motar.
Batare da wani b'ata lokaci ba Dr. Emraan d'in ya bud'e murfin motar ya fito.
Hannunsa rik'e da rigar suit d'insa da kuma wayarsa, ya nufi dogon ginin gidan nasu.
Tafiya me dan tsawo yayi kafun ya iso, babban balcony d'in da zai sada shi da babban falon gidan, hannunsa ya daura akan handle din k'ofar ya murd'a ahankali, Bakinsa d'auke da sassanyar sallama yasa kansa acikin, babban palor'n tare da ajiye k'afansa akan lallausan sofa'n da y'an yatsun k'afafun nasa suka lume acikinsu.

Ya ilahi na fad'a saboda ganin tsananin kyaun babban parlorn daya samu kansa aciki, wanda aka k'awata shi cikin Original Royal Sofa, masu matuk'ar kyau, da tsadar gaske, kyaun falon tamkar ba a Nigeria ba, bayan kuma babban tv plasma din dake ta aiki shi kad'ai babu kowa a falon.

K'arasowa cikin falon yayi, da yanayin dake nuna gajiya warsa, ahankali ya zube akan royal sofa'n, yana maida numfashi tamkar wanda yayi wasan tsere.
Idanunsa ya d'an lumshe, tare da bud'esu yana k'iran sunan.
"Aamma!"
"Aamma!!"
Da sassanyar muryarsa, had'i da maida kallonsa ga matattakalan dake cikin falon, domin yasan ba lallai wacce yake k'ira d'in ta jiyoshi ba, sanin hakan yasa shi mik'ewa tsaye da niyar haurawa saman.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now