Free page (Chapter 5)

89 7 0
                                    

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*Free page *
*CHAPTER 5*

Numfashi me k'arfi ya ja, tare da sake gyara kwanciyar nasa wanda ya share tsawon awa guda yana ahaka, batare da bacci ya daukesa ba, bawai kuma dan bayajin baccin ba, saidan rashin nutsuwar zuciyar daya samu kansa aciki.
Idanunsa dake cike da gajiya ya kuma lumshewa akaro na barkatai, wanda cikinsu ke haifar masa da wani irin yanayi na musamman da bayason aminta da hakan.
Aduk rayuwarsa wannan shine karonsa na farko, da idanunsa keyi masa gizo da idanun wata mace ta daban, yayinda sautin kukanta keyi masa yawo acikin kwanyar kansa, baisan me yasa yakejin hakan ba, domin ba abune daya saba ba, saidai wani sashi na zuciyarsa na fad'a masa cewa, dan ita din ta zamo patient dinsu ne shiyasa yake jin hakan, bayan wannan babu wani dalili da zaisa wata macen da baisan wacece ita ko daga ina take ba ta kutso masa kai cikin kwakwalwa.
Da wannan ya aminta har bacci ya d'aukesa, baccin da bashi ya farka ba sai wajajen k'arfe 5, alwala yayi ya wuce masallaci donyin sallan asuba.
Saidai koda aka idar da sallan bai dawo gida ba, a masallacin ya zauna yayi karatu, bai shigo gidan ba kuma har wajajen 7:30 am.

Direct d'akin Ammabuwa ya wuce, knocking k'ofar d'akin nata yayi har sau biyu, amma shiru babu amsa, tuna cewar maybe tana bacci yasa shi tura k'ofar d'akin ahankali ya shiga.

Kamar yanda yayi tunani kuma hakanne ta kasance, dan kwance ya hangota tayi d'ai d'ai akan gadonta tana ta sharar bacci, yayinda agefenta kuwa ledodin Dairy Milk and Bounty chocolate ne zube birjik akan gadon, da yawa daga ciki ta shanye su, yayinda wasu ko bata ma b'aresu ba, still agefen chocolates d'in ma magungunan ta ne daya kawo mata daren jiya, da kuma sauran tsofin magungunan dake nuna alaman cewa ta jima bata shasu ba, sabin sachets din kanma ko bud'esu batayi ba.

"Yah Allah wannan wace irin mata ce? wace irin mutum ce ke, kina matuk'ar bani headache, dan kinsa na fara tunanin anya kuwa bakiyi k'iriniya da kina yarinya ba?"

Yayi maganar yana me tattare tarin chocolates din, ya zuba acikin aljihun Moroccon Jallabiyar dake jikinsa, ahankali gudun kada ya tashe ta ya jawo bedside drawer'n ta, nanma fa wasu tarin chocolates din ya gani, da mamaki ya kalleta ya kuma kalli kayan zak'in dake cikin drawern, kansa kawai ya girgiza cikin sauri ya kwashe su, tare da maida mata drawer'n ya rufe.
Juyowa yayi gareta cikin nutsuwa ya gyara mata kwanciyar nata, tare da sake lullub'eta da blanket, ahankali ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, kafun ya fice daga d'akin.

Kasancewar kuma yau Sunday bashi da niyar zuwa aiki, wannan ya sashi wucewa Kitchen d'in gidan kai tsaye, domin ya tabbata adaidai wannan lokacin Aamman sa na kitchen tana had'a musu breakfast, domin su basu da wannan tsarin na rashin yin breakfast da wuri, tsanani basa wuce 9 am, ba kamar sauran al'ummar garin nasu ba da suke kai har 11 to 12 ba ayi breakfast ba.

Kamar yanda ya sani kuwa yana shawo kwanan kitchen din ya hangi Aamman nasa tsaye tana blending carrot.
Sanye take cikin doguwar rigar Turkish Abaya kamar ko yaushe, domin ita har kullum acikin ado take, tayi kyau sosai musamman da ta baza dogon gashin kanta daya sauk'o har tsakiyar bayanta.
Ahankali ya k'arasa shigowa kitchen din da yanayin sand'a ya matso kusa da Aamman wacce saboda k'aran blander yasa sam bata ji k'aran takun tafiyarsa ba, hannayensa duka biyu yasan ya ya zagaye cikinta, fuskarsa d'auke da murmushi yace.

"Good morning my beautiful."

"Oh wayyo Allah Emraan, me yasa zaka zo haka ko so kake ka tsorata ni?"
Aamman ta fad'a tana me juyowa garesa, wanda hakan ya sashi yin murmushi, fuskarsa d'auke da fari'a yace.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now