Free page (Chapter 9)

62 4 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917268)*

*free page*
*CHAPTER 9*

Ahankali ya k'arasa haurawa saman, kasancewar yana jin duk jikinsa amace, wannan yasa yana k'arasawa saman bedroom dinsa ya nufa.
Wayarsa dake hannunsa ya wurga akan gadon, tare da zare long sleeve din dake jikinsa, akasalance yabi gadon ya kwanta, idanunsa ya lumshe ahankali, yakejin bugun zuciyarsa na daidaita.
Hakanan yake jin kamar ya sauk'e wani nauyin da shi kansa bai san na menene ba, yayinda daga can k'asan zuciyar tasa kuwa wani bak'on lamari ne ke wanzuwa batare da sani ko Kuma yarda da amincewar shi ba.

Still sake gyara kwanciyarsa yayi, akaro na barkatai ahaka har baccin da bai shiryawa ba ya d'auke sa.

Yayinda acan k'asa kuwa sam Aamma ta kasa yin nesa da yarinyar, wacce take jiran farkawarta, gudun kada sai tayi nisa yarinyar ta tashi.
Kallon yarinyar take cike da ciwon sanin wani ya b'ata mata rayuwa da k'ananun shekarunta, hannunta tasa ta kawar da tarin hargitsatssen gashin yarinyar daya rufe mata gefen ido, wanda hakanne ya bata daman kallon fuskar yarinyar da kyau, tausayin ta me tsanani ne ya k'ara shiganta, domin atashin farko take jin yarinyar kamar y'arta ta cikin ta, duk da cewa Allah bai azurtata da haihuwar y'a mace ba, d'iya mace abune da take so, shiyasa ayanzu take jin Yacine din ak'asan zuciyarta.

Sauk'ak'akk'iyar doguwar rigar atamfar dake jikin yarinyar ta kuma kalla, wanda kana gani kasan bawai suna da isasbshen arziki bane saidai rufin asiri, komai na jikin yarinyar me sauk'in kud'ine in banda natural soft skin d'inta, Wanda yake d'auke da tsananin hasken dake nuna babu alamar wahala atarrare da Ita, kasancewar farinta irin me d'aukar hankalin nan ne, ga kuma tarin suma me tsananin laushi dake kanta, wanda tsawonsa ya kai har bayanta, tamkar Tuareg din Algeria haka take amma yanayin shape din fuskarta da kuma hasken fatarta yasa kaitsaye zaka iya danganta ta da Mauritanian🇲🇷.

Ajiyar zuciya Aamma ta sauk'e tare da janye idanunta daga kan yarinyar, wanda hakan yayi daidai da farkawar Yacine din, ahankali ta soma bud'e idanunta, da take jin duk sun rirrik'e, domin dama bawani iya gani take yi da kyau ba, saboda wahalan da tasha.
Idanunta ta ware bisa saman d'akin, kafun ahankali taja wani dogon numfashi tare da soma yunk'urin tashi dan tabbatar da inda take, domin duk da bata da cikakkiyar nutsuwarta ta tabbatar da cewa nan ba hospital bane.
Saidai kamar yanda taso ba hakan ne ya kasance ba, domin ajikinta babu wannan k'arfin da zata iya tashi, hasalima allurar da akai mata baigama sakinta ba, ji take yi komai na duniyar baya yi mata dad'i, wanda hakan yasa ta sakin wani irin kuka, cikin muryar ta dake shaking ta soma kiran sunan.

"Khalty! Khalty!!"

Da sauri Aamma dake zaune acan gefe, jin tana kiran sunan khalty yasa ta juyo, tare da matsowa kusa da ita, cikin kulawa tace.
"Sannu, kwanta ki huta kar kice zaki tashi."

Bak'uwar muryar da taji ta daki dodon kunnenta ya sata juyowa ahankali, ido hud'u sukayi da Aamman, wacce ganin idanun yarinyar yasa tajin wani irin matsanancin harbawan zuciya.
Domin aduniya awajen mutum d'aya take ganin irin way'annan k'wayan idon, duk da cewa Akwai wani d'an banbanci atsakanin nasa idanun da nata, amma shi kad'ai ke da irin way'annan idanun da cikinsu ke d'auke da rare grey.

Numfashi me k'arfi Aamman taja, tare da k'wak'ulo murmushi ta aza akan fuskarta, batare da ta samu da kallon da Yacine din keyi mata ba, atausa she tace.

"Sannu, har kin tashi ya jikin naki?"

Idanunta da sukayi narai narai ta zubawa matar, da fuskarta ya kasance bak'o agareta, wacece ita? inane nan kuma aka kawota?
Way'annan tambayoyin sune ke circulating acikin zuciyarta, wanda hakan yasa murya can k'asan mak'oshi tace.

PART OF OUR DESTINY Kde žijí příběhy. Začni objevovat