Free page (Chapter 6)

79 5 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*Free page*

*Chapter 6*

Washegari
Sassanyar safiya ce ke busawa me d'auke da tarin kyakkyawan yanayi, saidai kasancewar ranar yau din ta kasance Monday hakan yasa kafun 7:30 am ya gama shirya kansa tsab cikin black and white plain weave suit, da suka yi matuk'ar yi masa kyau,   kasancewar ak'afafunsa wasu black tassel patent shoe ne masu kyaun gaske ya sanya, wanda sukayi matching da kayan nasa, agogonsa na Rolex ya d'aura a tsintsiyar hannunsa, tare da feshe jikinsa da daddad'an turarukansa na ko yaushe.

Kyakkyawan agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla, wanda ganin time dinsa na tafiya ya sashi d'aukar briefcase da kuma y'ar k'aramar umbrella'n sa, saboda bayason kafun yazo shiga mota ruwa ya tab'a shi.

Da yanayi na d'an sassarfa yake sauk'owa daga kan steps din, har ya k'araso falon fuskarsa d'auke da murmushi yakai dubansa  ga Aamma wacce ke tsaye agaban dining table tana shirya masa breakfast, kamar yanda ta sabayi akowacce rana.

"Good morning Aamma."
Yayi maganar yana me k'arasowa kusa da ita, yana me d'an k'aryar da wuya kamar k'aramin yaro.

Abunda yasa Aamman yin murmushi cikin kulawa tace.

"Morning Bikir, yau har ka fito kenan."

"Eh banson na makara shiyasa akwai patients da yawa a hospital, Abbou ya fita ne?"

Ya tambaya alokacin da yake jan kujera ya zauna.

Yayinda Aamman dake kokarin saving dinsa tace.

"Eh ya fita, yace suna da meeting da zasuyi a Kaduna, kasan Abboun naku baya zama, yau meeting gobe meeting, sometimes ko time din kansa baya da."

Ta k'are maganar tana me turo masa kayan breakfast din gabansa, wanda cheesy garlic bread ne, da kuma pepperoni pizza, sai crème brûlée french toast, and fruit salad.

Gyara zamansa yayi tare da jawo kayan breakfast din ya soma ci, wani abu saboda da baisan dalilin faruwarsa ba kuwa shine, sam baya jin testing din abincin abakinsa, amma haka ya tuttura, fruit salad dinne ma ya d'ansha da yawa saboda yasan dalilin da yasa Aamman ta kawo masa.
Baiwuce kewar ma'abocin shan fruit salad din da take yi.
Wanda duk gidan shine kad'ai wanda ya maida fruits abun ci dana shan sa.
Kallon Aamman yayi wanda ya tabbatar da cewa tana cikin tsananin kewar wannan mutum d'ayan.

Kammala cin abincin ya sashi d'aukan Tissue ya ya goge bakinsa, tare da mik'ewa tsaye, yana me cewa.

"Aamma na k'oshi sosai, saina dawo."
Ya k'are maganar yana me kissing din hannun Aamman nasa wacce ke kallonsa tun fara cin abincin nasa har ya k'are.

"Allah ya kiyaye hanya."
Ta amsa tana me binsa da murmushi har ya fice.
Yana fita ya bud'e umbrella dinsa, saboda har zuwa lokacin ruwa ake, yana fitowa kuwa ya tarar da Saed Driver na jiransa, tun kafun ya k'araso Saed ya bud'e masa murfin motar, yana shiga yaja suka fice daga gidan.

Tafiya me d'an tsawo sukayi kafun motar tasu ta ratso cikin babban compound din hospital din, adaidai inda yake parking motar kullum Saed ya tsaida motar, wanda jin tsayuwar motar ne yasa Emraan dake zaune abayan motar, d'ago da kansa ya sauk'e bisa tamfatsetsen ginin hospital din nasu, kasancewar tunda suka kama hanya kansa na k'asa, yayi nisa wajen checking news a internet.
Hakan yasa bai san sun iso ba sai tsayuwar motar tasu ce ta ankarar dashi.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now