Free page (Chapter 2)

158 7 0
                                    


*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, Amount 500 naira only. WhatsApp number 07069917168)*

*Free page*

*Page 2*

Friday Morning..
Sassanyan safiya ce me d'auke da daddad'an yanayi, kasancewar yanayin garin ana d'an sanyi, hakan yasa sama tayi hazo hazo, tare da bada yanayi me matukar ban sha'awa, musamman ma da yanayin ya kasance ana d'an yayyafin ruwan sama me sanyi.

8 am daidai New Brand car k'irar 2021 Lexus GX 470 grey color, ta shigo cikin farfajiyar babban asibitin, da acan samansa, aka rubuta sunan hospital din da manyan bak'i, wanda komin rashin iya ganin mutum, bai isa yace ya kasa iya tantance rubutun ba, domin ya fito rad'au...
*ASSIDIQUE ATTOM El-FAROUQ CONSULTANT HOSPITAL*
Hospital ne da yake sahun gaba acikin jerin hospitals na garin Abuja, kasancewar ya dace da k'wararru kuma hazik'an ma'aikatan da suka san aikinsu.

Cikin iya tuk'i driver din dake tuk'a grey car din, ya nufi babban parking space d'in da aka k'awata sa da shuke shuken flowers masu kyau da d'aukar hankali, daidai wajen daya saba parking motar ya tsaya, da yanayin nutsuwa ya daidaita parking d'in motar, tare da bud'e murfin motar, wani d'an matashin saurayi ne ya fito daga b'angaren zaman driver, jikinsa sanye da uniform d'in dake bayyana matsayin aikinsa, wanda da dukkan alama shine driver'n motar, domin yana fitowa cikin sauri ya zagayo ya bud'e murfin motar b'angaren gidan baya, tare da neman waje ya tsaya k'am yana me jiran fitowar mamallakin motar, wanda ya d'auki tsawon mintuna 4 batare da ya fito ba.
sake gyara tsayuwarsa drivern yayi domin idan da sabo ya riga daya saba da wannan d'abi'ar ta maigidan nasa, hakan ba bak'on abu bane awajensa, aduk sanda suka zo hospital din yakan d'aukan some minutes kafun ya fito daga motar.

Ahankali ya zuro da kyawawan k'afafunsa waje, wanda suke sanye cikin Navy blue Gustavo Patent Italian Leather Shoe, masu matuk'ar kyau da tsadar gaske, wanda sukayi wa k'afartasa kyau, jim kad'an kuma ahankali cike da nutsuwa hadi da isar daya sabayi akoda yaushe, ya k'arasa fitowa daga cikin motar hannunsa na dama rik'e da tsadaddiyar briefcase d'insa da kuma wayarsa.
Kyakkyawan matashin saurayi ne, wanda ak'alla bazai d'arawa 35 years ba, sanye yake cikin wasu Navy blue Italian suit, da suka matuk'ar amsar jikinsa had'i da bayyana asalin kalar fatarsa, da ta kasance fara sol, yayinda daga ciki kuwa ya sanya white color long sleeve shirt, wanda ita ta k'ara kawata shigar tasa, had'i da tie d'i dake sak'ale a wuyansa.

Masha Allah!
Da kyaun wannan namijin da kwarjininsa ke cika Idanu, kasancewar sa farin fata mai hasken gaske, wanda kallon yanayinsa kadai zai iya sa ka hasasho shekarunsa kai tsaye, domin yana da madaidaicin tsawo had'i da kakkauran jikin dake nuna alaman kasantuwarsa ma'abocin motsa jiki, duk da jikin nasa bawai ya murde sosai ba ne.
Kyakkyawa ne ajin farko, wanda akan fuskarsa yana d'auke da dogon hanci, had'i da matsakaitan Idanun da cikinsu ke d'auke da light brown color eye balls, wanda saika k'ura masa ido sosai kafun ka gano hakan, sune kuma suka kasance sirrin kyaunsa, baya ga haka yana da siraran light pink lips d'in sa da sukayi kamar ya shafa musu lipstick, domin kuwa lips dinsa masu kyaune da burgewa had'i da daukar hankali, musamman Idan ka kallesu acikin kwakkwayan black beard din da yayiwa fuskar tasa k'awanya.
Tabbas duk wani shika shikan kyau ya cika su, kyakkyawa ne na k'arshe, domin ya mallaki duk wasu abubuwa da suke cika kyau, kama daga kan shiryayyun eye brows dinsa, da Kuma eye lashes dinsa da suka bayyana zara zara, kowannensu ya zauna a inda ya kamata.
Azahirance kyau da launin fatarsa ne ke bayyanar da wanene shi, domin suffarsa da kuma tsarin halittarsa daban take dana bak'ak'en fata, kaitsaye yafi kama da LEBANESE, domin ko daga yanayin sumar kansa wacce take a yalwace, tana shining saboda gyaran da ta samu, kaitsaye idakan ka cika kallonsa ko sai kaga ya fi yanayi da Berdber din Morocco, saboda yanayin gashin jikinsa da kuma haskensa me surki da kalan nasu, hakan ya nuna cewa da dukkan alama shi d'in ruwa biyu ne bawai zallan Lebanese ba.
Baya ga haka, kallo d'aya tak idan kayi masa zaka fahimci cewa shid'in mutum ne me babban matsayi, aji, kud'i had'i da miskilanci, duk da a ayanayin fuskarsa akwai alaman sakin fuska, domin mutum ne shi wanda baida yawan tsumewa, saidai ba kowa ke fahimtar hakan ba sai wanda ya zauna dashi.  
DR. EMRAAN ATTOM EL-FAROUQ kenan (MEDICAL DOCTOR) daya kasance babban likitan asibitin, haka kuma k'ashin bayan asibitin, kasancewar sa d'aya daga cikin likitotin da ake ji dasu acikin asibitin, masu rik'e da kambun nasara, wacce suka ciyo a k'asashe daban daban, saboda k'warewarsa awajen aikinsa, ya samu lambobin yabo da yawa daga k'asashe goma na duniya, hakan yasa mutane da yawa ke respecting d'insa saboda duk wani abu da yasa a gaba saiya cimma.

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now