Last Free page (Chapter 15)

200 9 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This Book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it, here's the account number for people that are willing to pay-2268498748 Fatima Abubakar UBA Bank, amount 500, WhatsAp number 07069917168)*

*(Please don't forgot to follow me on Arewabooks @fatymasardauna)*

*LAST FREE PAGE*
*Chapter 15*

"Kingani ko, kin dai ga abunda nake fad'a miki yanzu kin tabbata Bikir miyagun aljanu ne suka shiga jikinsa ko, wato abun nasa ma k'ara ta'azzara yake, zuk'ek'en Namiji dakai kace baka son aure, ikon Allah ikon gaske, yau naga takaina ni Ayeesha."

Ta k'are maganar tana me rik'e hab'arta idanunta, cike da al'ajabi idanunta kuwa na kansa har ya gama haurawa sama, kafun ta kuma juyo da kallonta ga Aamma, cikin yanayin fad'a tace.

"Ke saikiyi shiru kamar wacce ruwa ya cinye, wai ko baki jin bakin cikin ganinsa haka ne? to Idan zaki tashi tsaye mu nema masa gani ki tashi, domin nadai fad'a na kuma aljanune suka aure shi, wannan abun da yake yi ba lafiya ba, yau basai gobe ba, zan yi waya zansa ayi masa sauk'an al'qur'ani."

Ta k'are maganar tana me mik'ewa cikin jan k'afafunta da sukai tsami ta nufi d'akinta don d'auko wayarta.
Ganin haka yasa Aamma dake zaune lumshe idanunta, cike da damuwar rashin fahimtar menene asalin abunda ke damun Emraan din, yana yinwasu irin abu dake tsorata ta, akoda yaushe idan Ammabuwa tace aljanu sun aure shi, gani take kawai surkulle Ammabuwan keyi, because tasan aure lokaci ne, kuma idan lokaci yayi zaiyi, amma ayanzu kam abun ya fara bata tsoro.
Ta fara yarda cewa da gaske aljanun ne suka aureshi, wannan tunanin yasa ta mik'ewa da sauri ta nufi saman, saidai koda ta isa part din nasu bata iske sa a falo ba, hakan yasa ta nufi bedroom dinsa, akoda yaushe idan zata shiga sai tayi knocking amma ayau murd'a handle din kofar dakin kawai tayi ta fad'a ciki.

Tsaye yake ajikin babban drawer'nsa, ya d'aga kansa sama yayinda hannayensa duka biyu ke cikin aljihun wandonsa, idanunsa na lumshe kirib.

Da mamaki Aamman tayi tsaye tana kallonsa har na tsawon wasu seconds kafun ahankali cikin sanyin murya tak'ira sunanshi.

"Emraaan."

Jin muryar Aamman acikin kunnuwansa yasa shi, d'ago da kansa cikin hanzari, domin sam bai tsammaci zuwanta ba, ido cikin ido sukayi wanda hakan yasa shi sunkuyar dakai cikin son b'oye tsananin damuwarsa ahankali yace.

"Aamma yaushe kika shigo?"

"Eh ai baka ma san na shigo ba, tunanin me kakeyi Emraan?"
Ta tambaya tana me kafesa da idanunta, wanda hakan yasa shi shafa tattausar sumar kanshi, murmushi yayi wacce tafi kama dana karfin hali, kana asanyaye yace.

"Ba tunani nake ba Aamma, just na gaji ne kawai."

Idanunta ta d'an tsura masa na d'an wasu lokuta, kafun ta kamo hannunsa ahankali ta jawosa suka zauna akan gadon d'akin.

"Kada ka b'oyemin komai Emraan, ni na haifeka na kuma raine ka, tun kana karami nasan wanene kai, kana da damuwa kuma na ganta kwance akan fuskarka, harma da cikin idanunka, fad'amun meke damunka ne Emraan?"

Idanunsa ya d'an lumshe hadi da ware su alokaci guda, labb'an bakinsa ya motsa tamkar me ciwon baki ahankali yace.

"Aamma ba na son wannan auren? dan Allah abarshi."

Idanu Aamman ta kuma tsura masa cike da gaskata maganganun Ammabuwa tace.
"Aure ne kwata kwata baka so? ko kuwa dai Fadimen ne baka so asauya ma da wata daban?"

PART OF OUR DESTINY Where stories live. Discover now