Free page (Chapter 12)

71 5 0
                                    

@fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it, here is the account number for people that are willing to pay-2268498748 fatima abubakar uba bank, amount 500, WhatsApp number 07069917168)*

*Free page*
(Please don't forgot to fallow me on AREWABOOKS @fatymasardauna)

*Chapter 12*

Ahanzarce yabar wajen tare da nufan d'akinsa, azuciyarsa yake tambayar kansa shin menene hak'ik'anin abunda ke damun shi?
Bak'on al'amari ne wanda baisan shi ba, kasancewar bai tab'a jin irinsa ba aduk rayuwarsa.
Baisan dalili ko wani abu da yasa yakejin zuciyarsa na tsananta bugawa akan kowani lamarin ta ba.

"Ohhh Emraan ka dawo cikin hayyacin ka."
Wani sashi na zuciyarsa ya fad'a masa, alokacin da yayiwa kansa ma sauk'i akan lallausan bed d'insa, idanunsa ya lumshe, yana me jinjinawa girmar k'addarar sa, yayinda abayyane kuwa amsa d'aya tak yake nemawa kansa, shin acikin littafin k'addararsa an rubuta masa SO?, idan har babu So to menene abunda yake ji, ayanzu wanda yake dukan zuciyarsa?

"Ba SO bane."
Ya fad'a abayyane cikin son k'arfafawa kansa guiwa, domin kuwa yasan zuciyarsa bazata iyayin so ba, saboda bata cancanta ba, shiba cancacce bane, shi d'in ya kasance me matukar rauni ne, raunin da bazai tab'a iya bayyanawa kowa shi ba, ba wai a iya gangar jikinsa ba, ciwon azuciyarsa yake, ciwon da ako wace rana yake wasa da rayuwarsa, a irin wannan yanayin shin ya cancanta da SO?
Kansa ya girgiza saboda yasan hakan wani abune wanda baya yiwuwa, idan zuciyarsa nada raunin kamuwa da So, to shi bai kamata yabar hakan ya kasance ba, da wannan tunanin ya tashi ya jawo laptop dinsa, aiki ya fara amma still zuciyarsa tak'i daina wannan bugawan, yana ji kamar ya baro tunaninsa a baya, wannan yasa shi tashi ya sake d'auro alwala, sallah ya tayar domin hakan ne al'adarsa aduk lokacin da yaji tunaninsa na neman gushewa.

Yayinda acan b'angaren Aamma da Yacine kuwa, Amman na cikin rarrashinta bacci b'arawo ya kuma sace ta, d'aukan ta Amman tayi ta d'aura ta akan gado, tare da rufe mata jiki da blanket, bayan ta shafa mata addu'an kwanciya bacci, had'i da kashe mata wuta, sannan tabar d'akin, kaitsaye bedroom d'in Abbou ta nufa, bayan ta sauya shigarta zuwa expensive silky night gown, mai kyaun gaske, tana shiga ta same shi azaune ya baza takardu agabansa yana ta dubawa, agefensa ta zauna, bayan sun d'an tab'a hira take gaya masa yanda sukayi dasu Khalty, sam Abbou baiyi mamakin jin alfarmar da ta rok'a agaresu ba, saboda yasan wacece ita, yasan tana matuk'ar son y'ay'a mata.

Yayinda Aamman kuwa ganin yana murmushi ya sata gyara zama, ahankali cikin sanyin muryar dake bayyana damuwarta tace.

"Lokaci yayi da ya kamata Tareeq ya dawo gida."

"Me yasa?"
Ya tambaya cikin halin ko in kulan da yasa Aamman lumshe idanunta, asanyaye tace.

"Irin wannan halayen naka nako in kula shike k'ara nesanta ni dashi, nagaji da duka way'an nan abubuwan, ina buk'atar Taariq akusa dani, inajin kewarsa fiye da komai, shi d'in jinina ne fa, d'ana ne nina haifeshi, dan ya zab'i abunda yake so, bashi ke nufin nesanta kanmu dashi ba."

Kai Abboun ya girgiza tare da d'agowa ya kalli Aamman, da yanayi na nuna fushi yace.

"Shiya zab'i hakan, domin shida kansa ya barmu, shida kansa ya zab'i kalan rayuwar da yake so, shekarunsa 4 baizo ba, bai damu da sanin wani hali muke ciki ba, taurin kai da tsananin miskilancin sa ya hanashi waiwayan baya, yanzu mune kikeso mu nemoshi? koshi ne ya kamata ya nemo mu?"

Hawayen da suka cika idanunta ne suka k'waranyo, ahankali cikin danne abunda ke zuciyarta tace.

"Akowacce rana yana neman mu, koda bai kiraba ni nasani muna zuciyar sa, amma koma meye lokaci yayi da ya kamata d'ana ya dawo gareni."

PART OF OUR DESTINY Où les histoires vivent. Découvrez maintenant