prologue

1.2K 36 6
                                    


AURE UKU.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

AURE UKU littafine kirƙirarre wanda na ƙirkira badan cin fuska ga wani ba ko wata ba ,idan har labarin nan yayi dai dai da wani a raye ko amace a mun afuwa dan ba komai bane face sabani.

Ban yarda wani ko wata ya juya mun littafina ba ta kowacce irin siga ba idan har bai nemi izini na ba,yin hakan yana nufin haɗuwata da kai, a kiyaye dan Allah.

Gamasu sha'awar karatu a Arewa BOOK @chuchujay

Follow me on wattpad @chuchujay.

Description .

DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara ,

Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL ,

Aure  Uku, ƴaƴanta uku .

Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaɗdarar samunsu ta rarraba mata Aure .

Kalma ɗaya zaka faɗa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta .

Ita ɗin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki.

Bangaren soyayya fa?

Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda ɗaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a ƙwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani ɗa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da ƙin mazanta karara a fili.

Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi?

Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya?

Shin zata faɗa soyayyar wani ɗa namiji ko a'a?

Idan zata faɗa wanenen wannan mai sa'ar?

DR IMAM MUKTAR PAKI,

Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba,

Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara ɗaya wadda kareta ne kaɗai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta ɗauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake ƙarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka,

Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings ɗin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba?

Shin ya wannan kaɗdarar tasu zata kasance?

Shin  Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin ɗaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ƴaƴanta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba.

Ku biyo ɗiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !

Labari ne da zakuso  ,sannan na tabbata zaku nishaɗantu ,ku ilimantu ,

©®

CHUCHUJAY.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now