x29&30

436 27 0
                                    

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share i want audience domin baku.

Episode 2⃣9⃣➡3⃣0⃣

FRIDAY 12:00pm

    Tun daga harabar gidan Bulama zaka san ana gagarumun taro,

Idan ka tsaya Kallan babban compound ɗin wanda aka ware gefe aka tsantsarasa cikin yanayi na event zaka ce wani arnen hall ne aka kama 'dan gurin Ya tsaru ciki tsaruwa da decoration na blue and white,

Gurin da amarya zata zauna kan sa abun kallo ne,

Biki ne ake na kwana ɗaya wanda duk wanda Ya hallarce sa zai daɗe yana tuna wannan biki,

(Da Alƙalami na da littafina na taka 'dan shiga cikin gidan Bulama dan ɗaiɗai kun mutanen da nake gani basu gamsar dani ba ,mutum ɗaya nake san na saka a idanu na wato Umaimah Bulama ,sannan ina san na tsinci labarin shin bikin wa ake gidan attajiri bulama).

    Ahalin gidan maza da yan uwa da sukazo baki dayan su shirye suke cikin rich white expensive getzner a yayin da bakin daddy kuwa yaƙi ruruwa,

Fita sukayi harabar gidan suna masu hawa Arnan motocin da suka mallaka domin isa baban masallacin Sudais ƙashim domin gabatar da sallar juma'a da kuma ɗaurin Auren da zai kwashi Alumma masu numfashi After All ɗaurin Aure ne za'ayi na ɗiyar Bulama tilo,wadda take tsoka ɗaya a miya garesa,A karo na HUƊU.

    Magana ta mutane dama baka isa ka tare ta ba muddin idan sukaso yin ta,haka nan maganar Auren Paki da Umaimah ta ringa yawo a duniya kamar bonfire,ko wanne vlog da gossip page idan kaje maganar su Ake,wasu suyi Negative magana wasu positive Har da masu faɗin umaimah ta Auri ƙaninta,wasu suce asiri tayi masa ta Aure sa,wasu suce Auren kuɗi ne da dai sauran su,sun gagara gane soyayyar dake tsakanin su,

A watan da aka saka na bikin su ba karamar soyayya suke nunawa juna ba ,kar ma ace paki wanda baki ɗaya yarda take amsa masa soyayyar sa yasa shi kara zaucewa a soyayyarta ,

Wani lokacin har kunya yake bata a asibiti yarda yake zaƙewa soyayyarta ,tun ana gulmar har An haƙura saboda basu bawa maganganun mutane attention ba ,love ɗinsu kawai suka saka a gaba .

    Maganar Auren su ba a wani saka ta da nesa ba saboda yazo Aure kuma ko wanne side sun amince sannan Ita ba budurwa bace da za'a tsaya wani bata lokaci,dan haka iyayensu suka taƙaice lokaci da yardar su,

Hajiya Nana kuwa kowa yayi mamakin yarda tayi shiru ta kwantar da hankalin ta kamar dama tun farko ba ta ƙi Auren ba,

Babu wanda Ya maida hankali sa gareta dan kowa Ya saka shi ne as ta haƙura sannan tasan rigima ne kawai ta saka a gaban ta.

   

***

    Zaune Umaimah take bakin mirror tana gyara gelling gefen sumarta da tasha kananun kitso wanda suka zuba bayan ta kasancewar ta mace mai yawaitar suma,

Tsantsaɗediyar kwalliya ce a fuskarta wadda batayi kadan ba bakuma tayi yawa ba,

Idan ka Kalle ta Zaka so ka kuma saka ta ciki Idanun ka saboda irin kyau ɗin da tayi mai ɗaukar ido,hannun ta zane da ja da baƙin lalle,Abun ka da Mai haske sai wanda Ya kalla.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now