episode 17&18

422 27 0
                                    

AURE UKU

(a hospital romance)

  By

Chuchujay✍🏽

Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣

    Tsaye taki bakin katafaren mansion ɗin su Paki tana tunanin abun da ya kawo ta ba tare da tayi tunani na biyu ba,

"Wata zuciyar na faɗa mata ta koma saboda bata san abunda zata ce ba idan ta shiga,tunda dole tasan yana tare da iyayen sa,"

"Wata zuciyar kuma tace mata "taje a matsayin Caring doctor ɗin da yake ƙarkashin ta After all babu wanda yasan baya da lafia ɗin,"

Kallan Kb dake kallan ta tayi tace lapia?

Murmushi yayi yace "lapia kalau Dr ,ina so ne kawai na faɗa miki,Paki yana mutuwar san ki,sannan saboda Allah yake sanki,tunda nake dashi babu ɗiya macen da Ya tab'a nuna soyayyar ta ƙarara kamar taki,".

"Kallan sa tayi Kafun ta ɗauke idanun ta kamar abin bai affecting ɗin ta ba tace "zaka mana jagora ne ko kuma na shiga da tambaya".

Faɗaɗa fara'arsa yayi a lokacin da Ya jiyo humour cikin maganar ta,

Baisan tana da wannan side ɗin ba.

Kafun yace "cikin da tafiya yi horn sai mu shiga."

Gate biyu ne a gidan wanda tsakanin gate na farko dana biyu akwai yar tazara,tun daga gate ɗin farko tasan Paki yaran Soldier ne ,taso tayi sensing a case ɗin su Dr Jabir ganin yarda sojojin ke basa ladabi.

"Sojoji ke gadin su dan sune gate ɗin farko dana biyun,"

Ganin KB ne yasa basu tsare su ba suka basu damar shiga,

Ba tare da ta kalli KB ba tace "dad ɗin paki hala soja ne?"

Kaɗa kai yayi yace admiral ne ,yaso sosai paki yayi aikin amma yaki wanda nafi maidashi ga kaddarar haɗuwa dake takaisa Likitanci.

Tsintar kanta tayi da yin murmushi wanda bai kub'ucewa KB ba,at least yanzu hankalin sa Ya kwanta daya gane Abokin sa ba haukan banza kawai yake ba.

"A gefen expensive motocin gidan ta faka tata,"

KB ne Ya fara fitowa Kafun ita,

Haka nan taji gabanta na faɗuwa,

Kallan Kb tayi tace "is it okay.

Kaɗa mata kai yayi Kafun Ya fara tafiya tana binsa a gefe,

A bakin wata wide kofa dake rufe suka tsaya inda Kb Ya danna door bell,

Minti ƙalilan aka buɗe kofar,

Sameer ce tsaye "idanun ta na sauka umaimah ta haɗe rai kamar an aiko mata da saƙon mutuwa tace"uban me Ya kawoki nan?

Kin biyo sa gida ne a cigaba daga inda aka tsaya tunda ke roban pants ɗinki ya sake baya Kama miki ƙugu. "

KB na koƙarin magana muryan ummu da ta Aiko ta ta buɗe ta katse ta a yayin da take cewa""Ke Sameer wa kike faɗawa maganar rashin ɗa'a haka.

Faɗada murmushi umaimah tayi Nervously a lokacin da Ummu ta bayyana wadda ke mutuƙar Kama da Iman paki,kana kallanta kasan mahaifiyar sa ce,

"Matsa mun bakin hanya nan,Au kabir kune ma ,Kallan umaimah tayi Kafun tace "da ita kike,"Baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah ku shigo daga ciki,

Kiyi hakuri.

Murmushi umaimah tayi ba dan maganar sameera bata mata zafi ba,ita bama tasan sameera gidan take zaune ba da ba lallai tazo ba dan ta fahimci yarinyar notinan kanta a kunce suke.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now