finale

599 27 3
                                    

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share ❤

FINAL EPISODE.

    Jeka ka dawo  Imam paki yake a bakin theatre room na Queen cleopatra Hospital  dake ƙasar misra yana Mai shafa fuskar sa a hankali,

Kallo ɗaya zakayi masa kasan cewa yana cikin tashin hankali wanda ba'a sawa rana.

Dafa sa Ummu tayi tana Mai faɗin"Imam kazo muje ka zauna dan Allah tun ɗazu kake abu daya komai zai zama dai dai da ikon Allah ,Addu'ar mu bazata faɗi kasa nan ba Za'ayi aikin nan lafiya,"

Hannunsa ta kamo ta zaunar dashi kafun ta buɗe ruwan gora ta miƙa masa ,

Babu musu Ya ƙarba ya daga a bakinsa Ya sha Mai isarsa kafun Ya sauke ya kalli Ummu cike da damuwa yace"Ummu sun jima 'fa har yanzu shiru,"

Ganin yarda Ya ke cikin mutuƙar damuwa ne yasata fara bashi baki a hankali tana kwantar masa da hankali.

Ji yake kamar Ya tashi Ya shiga ,tsinewa rashin samun licence ɗin sa yayi cos da ace yana da shi da babu wanda Ya isa Ya hanasa ko tsayawa ne yayi akan matarsa ,

    Dalilin zuwan su misra umaimah ta takura akan ita Chan take san haihuwa tun tana da sauran wata ɗaya ta haihu,

Bai yi mata musu ba ya yarda da zuwan nata duk da bai samu sun wuce tare ba saboda kammala medInternship ɗin sa wanda dole dole yasa shi tsayawa ganin yarda ta nace akan Ya tsaya ɗin she will be okay musamman hindu na tare da ita sannan ga Afnan Ya haɗasu tare.

Satin ta biyu a garin Ya kammala abunda zaiyyi Ya bita .

    Kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa wannan ciki ba abu ɗaya ke cikinsa ba ,ille kuwa scanning ɗin farko aka ce musu Twins ne wanda murna gurin Paki ba'a saka mata rana,siyayya kuwa da yayi kamar bashi da mafaɗi ,

Ciwo sosai ta fara da yaje tana Mai yan ƙananun naƙuda dan haka Ya tatarata suka koma asibitin su hindu baki ɗaya wanda suke ta kulawa da ita kamar su maida ta ciki,abunka da larabawa,

Yarda take nakudar ja da ja yasa da aka dubata suka tabbatar masu bazata iya haihuwa da kanta ba dan babies ɗin sunyi girma da yawa sannan ciresu shine kawai zai tsallakar da uwa da yaran,

Babu musu Paki yasa hannu inda suka tsaya a washe gari zasuyi aikin dan haka yakira Ummu Ya tada mata hankali dole tayo takakkiya ta taho.

    Suna wannan zaman jiran tsammanin Hindu ta fito tana Mai washe baki tace"Ummu,Imam Congratulations,"

da saurinsa Ya tako inda take yana Mai faɗin"Hindu matana fa?"

Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalin ka baban uku ,matar ka da yaran ka suna cikin koshin lafiya,"

Washe baki yayi yana Mai faɗin"Alhamdulillah ,Allah na gode maka,zan iya ganinsu?"

Shiru yayi lokaci guda kuma yana san tuna abunda tace cike da mamaki yace "yara nawa ma kikace?"

Sake faɗaɗa fara'arta tayi tace "yara uku ,kai da umaimah kun samu triplet .

Da saurinsa Ya koma ga ummu yana Mai hawayen murna yace "Ummu Kina ji ko,

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now