x43&44

432 28 0
                                    

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share ❤

Episode4⃣3⃣➡4⃣4⃣

  TWO MONTHS LATER.

Jin alamun ana mata tafiyan tsutsa a tafin kafarta kamar a mafarki yasaka ta buɗe idanunta a hankali tana tunanin ko Abdallah ne 'dan tasan hallayyarsa ce,

    Tashi tayi zaune tana tunanin 'dan bazan dukan da Zatayi masa cos taga alamun bai daddara dukan da yasha a gurin ta ba da safe,

Cike da bala'in da take ji a yanzu tace "Abdallah you're trying me again ba,"

Ga mamakinta kuma sai taga ko ina na ɗakin dim sannan babu alamun mutum a gurin,ɗan tsaki tayi tana tunanin irin jarabar da Za tayi ga Paki idan Ya shigo gidan cos tun 10 ta kwanta da ta gaji da zaman jiransa ,maganar abinci kuwa yanzu tama daina jiransa ,muddin bai dawo da wuri ba zata saka abincinta ne taci ta rabu dashi,

Wayanta ta jawo taga 11:59pm,

Ƙwafa tayi tace "Baby you're dead ,kazo gidan nan ka sameni,bari ma na kulle ɗakina idan ka dawo Ai kana da ɗaki zamu haɗe da safe,"

Saukowa tayi a kan gadon tana Mai saka takalmin da ke bakin gadon ta nufi kofar 'dan kullawa ,tana saka key ta juya dan komawa taga ɗakin baki ɗaya Ya ɗauki haske ,tsaye yake bakin switch ɗin hannunsa ɗauke da balloons guda biyu,bin ɗakin tayi da kallo taga ko ina is well decorated da roses wanda hakan Ya bata amsar inda take jin kamshin rose,

Daga jikin bango an rubuta HAPPY 30 WIFFY da decorated shining Papers,

Hannu tasa ta rufe bakinta tana Mai jin wasu hawaye na zubo mata lokacin da yafara Takowa yana Mai faɗin"Happy birthday to you,Happy birthday to you,"

Takowa  yayi gabanta da balloon ɗin a hannunsa wanda yake daure jikin wani box Mai kyau ,buɗe box ɗin yayi yaciro wata diamond chain siririya Ya zo daf da ita yana Mai faɗaɗa murmushin sa Ya maƙala mata a wuya,

Kafun tace wani abu Ya jawo wani envelope Ya miƙa mata yana Mai faɗin "Happy 30 wiffy,"

Washe baki kawai take kamar wata wawiya kafun ta buɗe envelope ɗin da zumuɗin dan ganin menene cikin ta,

Paper ne guda biyu ta ciro,a hankali tafara karanta na farkon ,property ownership ne na asibiti Mai suna UMAIMAH PRIVATE HOSPITAL,

Da mamaki take kallan paper kafin ta buɗe ta biyu Mai ɗauke da yarjewa na lasisin Buɗe asibitin,

Kallansa tayi tana Mai san saita kanta da kuma tabbatarwa da kanta abunda take zargi,realization ne Ya  dake ta lokacin da ta tuna ya karbi Blue print na asibitin ta ,sannan duk lokacin da tayi masa maganar asibitin zaice mata ta bari tukunna wanda cikin yimasa biyayyah ta bari ɗin,

Rungumesa tayi tana Mai fashewa da kuka tace "Baby dont tell me this,"

Shafa kanta yayi yana Mai kissing saman kanta yace "yes wiffy asibitin ki Ya kammala da duk wani abu da kike buƙata a cikin sa abu kadan ne Ya rage ,im just Happy cos na samu na mamaki wannan birthday surprise ɗin da nake mutuwan san na miki,

Raba jikinta tayi da nasa tana Mai kallan cikin idanunsa kafin ta taba Chain ɗin dake wuyanta tace "Bansan wane Aikin lada ba nayi da yazama Allah ya mun kyautar ka,

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now