x37&38

412 20 0
                                    

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share ❤



Episode 3⃣7⃣➡3⃣8⃣

    Ganin Nana ta sume ne yasa imam saurin sakin sameera yayi kan Nana 'dan bata taimakon gaggawa yama manta da tana hannun umaimah ne,ganin yarda Ya ruɗe ne yasata dafa shi tace "baby let me handle her for you,ta suma ne due to naushin da sameera ta bata da shaƙeta da tayi wanda shine ya tsoratata mu kaita ciki,"

Ɗaukar Nana yayi kamar Baby yayi sasheshi da ita,

    Sameera na kokarin guduwa Affan Ya kamata muchukwi yace"ki yarda dani Babu yarda za'ayi kibar gidan nan da ƙafafunki a tsaye,yakamata Kafun ki daki Nana kisan wacece ita,it was a bad move i most say,a tunaninki idan kika kashe Nana zamuyi alfahari dake?

Dariya yayi a lokacin da Ya hango sojojin first gate da Ya kira yace "gasu Chan su zan bawa rainanki,kar ki damu bazasu dakeki ba kafafunki kawai zasu karya 'dan naga ta Nana kamar ta karye" .

    Tasa ƙeyar sameerah wadda ta shiga ainayin dana sanin dukan Nana sojojin sukayi suna mata muzurai wanda yasa taji kamar ta saka fitsari a wando.

Kai tsaye sashin su Ya nufa dan sanar dasu Ummu abinda ke faruwa 'dan yasan bama su san anayi ba,ille kuwa da yaje kallo ma sukeyi a falo,

Cikin tashin hankali kowanensu Ya tashi dan zuwa gun Nana ɗin saboda duk rigimarta su masu ƙaunartane,koda suka shiga Nana nata rigizar kuka taƙi tayi shiru duk kuwa abinda zasu faɗa mata ,zama ummu tayi kusa da ita tana Mai dora hannunta kan Kafarta,

Da sauri Nana ta kwallara wata ƙara jin azabar da ta ratsa kwakwalwarta sakamakon tab'a mata ƙafar da akayi ,

Da sauri umaimah ta isa inda take kwance tana Mai duba kafar ,kallan Paki tayi tace akwai damuwa a kafar ta Ɗin nan cos ta buge kafar sosai,amma banace menene ba,

    Cike da raki Nana tace"Umaimatu,ki duba mun mana 'dan Allah inace ke likitace da kika iya komai,

Dafa kafaɗarta Nana tayi tace "Nana yanzu asibiti zamu ,kinga ni ba likitan abunda Ya shafi ƙashi ba ce amma na tabbata ba karaya bace nasan bai wuce gochewa bane ko buguwa,

Riƙe hannun umaimah Nana tayi tace "'dan Allah kar ku Kaini asibiti a kira malam hadi mai ɗaurin karaya Ya dubani,habiba ki kiramun muntari mutuwa zanyi,'dan Allah ku yafe mun,Apan ,Apnan kuyi haƙuri dani wallahi na tuba ,ku yafe mun ,musamman ke Umaimatu ko na daina jin raɗaɗin da nake ji a yanzu ,imamu na zo nan,

Mastowa kusa da Ita yayi yace "Nana gani,

Hannunsa yasa cikin nata yace "Nana kiyi shiru haka nan ba zaki mutu ba sannan na kira Abbu ɗin da kuma malam hadi ɗin da kikace na saka aje a ɗauko sa 'dan Allah kiyi shiru hakan nan,

Kaɗa kai tayi tana Mai Kama baki tace"nayi shiru imamuna nayi shiru amma kafunnan 'dan Allah ku faɗamun idan Tega Ya cinye  tsokokin dake jikin sameera,idan bai cinye ba ni zan zama Tega na cinye yar shegiya dan wallahi yarinyar nan ido na idanta sai romanta".

    Dariya ke san Kwacewa inteesar ,mazawa tayi tana Mai ɗaukar babynta dake Kananun kuka suka futa tana Mai ririrgata,tana fita wajen ta saka dariya,haɗiye dariyarta tayi tayi kamar wasa takewa babynta jin mutum a bayanta,tana juyawa taga Afnan,suna haɗa ido suka kwashe da wata dariyar a tare sai da sukayi mai isarsu sannan inteesar tace "Allah naji daɗin yarda sameera ta nunawa Nana Allah,ki kalla dai duk yarda mukeyi da ita a gidan nan bata ganewa kowa yayi ƙokarin Ya nuna mata Allah amma tana runtse ido Amma kinga cikin tafka ɗaya sameera ta dawo da Nana.

AURE UKU(completed)Where stories live. Discover now